Rasha Ta Yi Maraba Da Cire Sunanta A Matsayin ” Barazanar Da Amurka Teke Fuskanta
Published: 8th, December 2025 GMT
Mai Magana da yawun fadar mulkin Rasha Dmitry Viskov ya ce; Fadar mulkin kasar tana maraba da matakin da shugaban kasar Amurka ya dauka na bitar siyasar tsaron kasar, da ta kunshi cire kasar Rasha a matsayin barazanar da Amurkan take fuskanta.
Viskov ya fada wa kamfanin dillancin labarun “Tass” cewa; a cikin sabon tsarin tsaron kasar ta Amurka an cire Rasha a matsayin baraza, don haka yana kira da a samo hanyoyin aiki tare akan muhimman batutuwa na duniya.
Haka nan kuma ya ce; Wannan matakin ci gaba ne sosai.
Wannan sabuwar siyasar tsaron ta Amurka tana yi wa China a matsayin babban kalubale ta fuskar tattalin arziki, don hakan Amurka za ta yi aiki domin sake dawo da adalci da kuma abinda ta kira ‘yancin Amurka.”
Sai dai kuma ta jaddada wajabcin ci gaba da jibge sojoji a yankin tekunan Inida da kuma Pacific domin abinda ta ce kokarin hana afkuwar yaki.
Haka nan kuma ya bayyana fatansa na ganin sabuwar siyasar tsaron Amurka ta share fagen kawo karshen yakin kasar Ukirniya da kuma tattaunawa da bude sabuwar alaka da Amurka, da hakan shi ne ra’ayin shugaba Vladmir Putin.
Matakin na Amurka akan Rasha ya bakantawa kasashen turai da suke son Amurkan ta zamar musu jagora a yakin da suke yi da Rasha ta hanyar kasar Ukiraniya.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Majid Majidi Na Iran Ya Sami Kyauyar Girmamawa Daga Cibiyar Fina-finai Na “Eurasia Dake Kasar Rasha December 8, 2025 Benin : Har yanzu Shugaba Patrice Talon ne a kan mulkin_fadar shugaban kasa December 7, 2025 Dole ne Amurka ta amince da ‘yancin Iran na samar da makamashin nukiliya cikin lumana (Araghchi) December 7, 2025 Hamas : ‘’Babu batun kwance damarar makamai matuƙar Isra’ila ta ci gaba da mamaya’’ December 7, 2025 Iran : sabbin dabarun tsaron Amurka cimma maradun Isra’ila December 7, 2025 Masar : ba za mu bari a yi amfani da iyakar Rafah ba don korar Falasdinawa December 7, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan(a) 168 December 7, 2025 Kissoshin rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 167 December 7, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 166 December 7, 2025 Rwanda Da Amurka Sun Rattaba Hannu Kan Tallafin Dalar Amurka Miliyon $228 Na Kiwon Lafiya December 7, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Iran : sabbin dabarun tsaron Amurka cimma maradun Isra’ila
Jamhuriya Musulinci ta Iran, ta bayyana sabbin dabarun tsaron Amurka na cimma maradun gwamnatin Isra’ila ne.
Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ya ce sabbin dabarun tsaron Kasa na Amurka (NSS) da ke bayyana ka’idojin Washington da muhimman manufofin harkokin waje a zahiri cimma maradun tsaro ne ga gwamnatin Isra’ila ne.
Esmaeil Baghaei ya yi wannan furucin ne a lokacin wani taron manema labarai, kwana biyu bayan gwamnatin Shugaban Amurka Donald Trump ta bayyana sabbin dabarun tsaron na NSS na 2025.
A kwanan ne gwamnatin Amurka ta sanar da sabbin dabarun tsaron na ta wanda ya tanadi har da soke bada mafaka ga ‘yan kasashen duniya 19.
Kasashe sun suka hada da Chadi, Congo, Equatorial Guinea, Eritrea, Libya, Somalia, Sudan, Burundi, Saliyo da kuma Togo, Afghanistan, Burma, Haiti, Iran, Yemen, Cuba, Laos, Turkmenistan, da Venezuela.
Matakin ya shafi ‘yan kasashen 19 da suka shiga Amurka a ranar 20 ga Janairu, 2021 ko bayan haka don tantance duk barazanar da ke akwai ga tsaron kasar da tsarin jama’a.”
Wannan shawarar ta zo ne bayan da Shugaba Donald Trump da Sakataren Tsaron Cikin Gida Kristi Noem suka yi kira da a tsaurara matakan tsaro kan shige da fice bayan harbin da aka yi wa wasu jami’an tsaron National Guard guda biyu a makon da ya gabata a Washington, D.C.
Wanda ake zargin, dan kasar Afghanistan ne mai shekaru 29 wanda aka ba shi mafaka a watan Afrilu, ya shiga Amurka a shekarar 2021 bayan janyewar sojojin Amurka daga Afghanistan kuma ya taba yin aiki a wasu hukumomin gwamnatin Amurka, ciki har da CIA, a cewar kafofin watsa labarai na Amurka.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Masar : ba za mu bari a yi amfani da iyakar Rafah ba don korar Falasdinawa December 7, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan(a) 168 December 7, 2025 Kissoshin rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 167 December 7, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 166 December 7, 2025 Rwanda Da Amurka Sun Rattaba Hannu Kan Tallafin Dalar Amurka Miliyon $228 Na Kiwon Lafiya December 7, 2025 Amurka: Mun Yi Kokarin Kifar Da Gwamnatin JMI Har Sau Biyu Ba Tare Da Samun Nasara Ba December 7, 2025 Iran Ta Gargadi Kasashen Larabawa Dangane Da Tsibiran Kasar Guda Uku A cikin Tekun Farisa December 7, 2025 Hamas Tace Zata Mikawa Gwamnatin Falasdinawa Makamanta Idan An Kawo Karshen Mamaya December 7, 2025 Venezuela: Ba Mu Tsoron Kaudin Amurka Na Wuce Gona Da Iri December 7, 2025 Iran Ta Zama Zakaran Duniya A Wasan “Taekwondo” Na Masu Shekaru Kasa Da 21 December 7, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci