Iran Ta Bukaci Mutanen Yemen Su Daina Kashe Juna
Published: 14th, December 2025 GMT
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esmail Baghaei ya gargadi mutanen kasar Yemen daga kungiyoyi daban daban da su yi kokarin sasantawa a tsakaninsu, saboda ci gaba ta yakar juna yana taimakawa HKI ne kawau.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Baghaei ya na fadar haka a yau Lahadi a cikin wani bayanin da ya watsa a shafinda na X.
Ya kara da cewa a cikin yan makonnin da suka gabata yan bindiga wadanda suke samun goyon bayan saudia sun fara yaki da sojojin Gwamnatin Yemen a kudancin kasar mai arzikin man fetur da nufin tada hankali a kasar.
Wasu kafafen yada labarai suna maganar cewa kudancin kasar Yemen zata shelanta bellewarta daga arewacin kasar nan ba da dadewa ba.
Baghaei ya bayyana cewa dukkan wadan nan al-amura suna faruwa ne a cikin shirin HKI na sake tsara kasashen yammacin Asiya. Kuma shi yasa bata barin wata kasa daga kasashen yankin ta ci gaba da zaman lafiya ba.
Daga karshen ya bukaci kungiyoyi daban-daban a kasar ta Yemen su yi kokarin sasantawa a tsakaninsu kada su ci gaba da aiki wa yahudawa ta hanyar rarraba kansu da kuma zubar da jinanensu don amfanin yahudawa.
Yayi kira ga gwamnatin kasar Yemen ta yi kokarin sasantawa da sauran Kabilun kasar don dawo da zaman lafiya a kasar. Duk wanda bai son zaman lafiya shi ne wanda yake khidima wa makiyan kasar.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran Tayi Tir Da Hare-Haren Sydney Na Kasar Austaralia December 14, 2025 Sudan: Makaman ‘Drones’ Sun Kashe Ma’aikatan MDD 6 A Kadugli Na Kurdufan Ta Kudu December 14, 2025 Eritrea Ta Fice Daga Kungiyar Raya Kasahsen Gabacin Afrika (IGAD) December 14, 2025 َA Yau Ne Za’a Gudanar Da Taron Koli Na Kungiyar ECOWAS A Birnin Abuja December 14, 2025 Iran Ta karbi Bakunci Taron Kasashen Dake Makwabtaka Da Afghanistan Da Rasha December 14, 2025 Isra’ilaTa Kashe Wani Bafalasdine Matashi A Wani Hari Da Takai A Arewacin Kogin Jodan. December 14, 2025 Shuwagabannin Majalisar Kasar Iran Da Na Ethiopia Sun Gudanar Da Taron Manema Labarai December 14, 2025 Ghana Ta Kori Wasu Yahudawa Guda 3 Don Mayar Da Martani December 14, 2025 Araghchi ya bukaci Amurka ta girmama al’ummar Iran da gwamnatinta December 14, 2025 Dan bindiga ya kashe sojojin Amurka biyu da wani farar hula a Siriya December 14, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Za A Yi Manyan Zabuka A Kasar Habasha A Watan Yuni Na 2026
Hukumar zaben kasar Habasha ta sanar da cewa za a yi manyan zabukan kasar a ranar 1 ga watan Yuni na 2026.
Shugabar hukumar zaben kasar ta Habasha Melatwork Hailu ta fada wa kafafen watsa labarun kasar cewa; Ana gudanar da ayyukan ne a yanzu domin tsara wuraren da za a yi zabukan da samar da rumfunan zabe a cikin rassan da za a kada kuri’a.”
Har ila yau shugabar hukumar zaben kasar ta Habasha ta ce, jam’iyyun siyasar kasar sun sami horon da ya dace domin bayyana da tallata manufofinsu ga jama’ar kasar.
Sai dai yin zabe a kasar ta Habasha yana fuskantar kalubale mai yawa. Kasar dai ba ta dade da fitowa daga yakin basasa ba wanda aka yi a tsakanin gwamnatin tarayya da yankin Tigray da aka yi a tsakanin 2020 zuwa 2022.
Rikicin ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 600,000, kuma wasu da adadinsu ya kai miliyan 1 su ka bar gidajensu.
Kuma har yanzu ana fama da tashe-tashen hankula a cikin yankunan Oromia da Amhara.
A jawabin da ya gabatar a ranar 28 ga watan Oktoba, Fira ministan kasar ta Habasha Abiy Ahmed ya ce; Gwamnatin kasar tana da karfin da za ta iya gudanar da zabukan.”
Haka nan kuma ya ce, zaben da za a yi zai zama shi ne mafi tsaruwa a tarihin kasar.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Turkiya A Shirye Take Ta Aike Da Sojoji Zuwa Yankin Gaza December 12, 2025 Kremlin: Putin Ya Bayyana Wa Shugaba Maduro Na Venezuela Goyon Bayansa December 12, 2025 Ben Gafir Ya Sha Alwashin Rushe Kabarin Sheikh Izzuddin Alkassam December 12, 2025 Maduro: Amurka Ta Bude Sabon Salon Fashi Akan Doron Ruwa December 12, 2025 Ayatollah Khamenei : Iran na samun ci gaba duk da kalubale da dama December 11, 2025 Kyaftin Traoré : Yau Burkina ta zama misali a duniya December 11, 2025 Iran da Kazakhstan Sun rattaba hannu kan yarjeniyoyi da dama December 11, 2025 Hamas : Isra’ila ta gaza cika alkawarin da ta dauka kan yarjejeniyar tsagaita wuta December 11, 2025 Kasashen ECOWAS sun rage kudin sufirin jiragan sama a tsakaninsu December 11, 2025 Dakarun IRGC 3 Sun Yi Shahada A wani Harin Ta’addanci A Kudancin Kasar Iran December 11, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci