Sojoji sun kashe ’yan bindiga 13, sun ceto ’yan kasuwa a Sakkwato
Published: 8th, December 2025 GMT
Sojoji sun kashe wasu da ake zargin ’yan bindiga ne da suke ƙoƙarin yi garkuwa da ayarin ’yan kasuwa a kan hanyar Tarah–Karawa da ke Sabon Birni a Jihar Sakkwato.
’Yan kasuwar na kan hanyarsu daga ƙauyen Tarah zuwa kasuwar mako a Sabon Birni ne lokacin da ’yan bindiga suka kai musu hari a Kwanan Akimbo da misalin karfe 8 na safe.
Wani mazaunin yankin ya shaida wa wakilinmu cewa sojojin da ke sansani a Kurawa sun ji karar harbe-harbe, suka garzaya wajen, inda aka yi musayar wuta na kusan sa’a guda.
“Sojoji sun yi musu luguden wuta, daga baya ’yan bindigar suka ja da baya suka tsere zuwa maɓoyarsu a can bayan rafin.
Rashin Tsaro: Gwamnatin Tarayya ta gaza — Kwankwaso An kama tsohon fursuna da bindiga ƙirar AK-47“Mun ƙirga gawarwakin ’yan bindiga tara a yankinmu, sannan aka gano wasu hudu a dajin kusa da rafin. Sojoji kuma sun kwashe makamai da babura da dama suka kai Kurawa,” in ji wani mazaunin.
Ya ƙara da cewa mutane biyu ne suka samu raunuka, suna karbar magani a asibiti, amma dukkan ’yan kasuwar sun tsira ba tare da wani rauni ba. “Babu asarar rayuka a ɓangaren sojoji,” in ji shi.
Al’ummomin Kurawa da maƙwabtansu sun yi murna da nasarar da sojojin suka samu.
Ɗan majalisar dokokin jihar da ke wakiltar Sabon Birni, Hon. Aminu Boza, ya ce an gano gawarwakin aƙalla tara daga cikin ’yan bindigar, kuma bincike na ci gaba.
“An kwato makamai da babura da dama daga hannunsu. Ina fatan sojojinmu za su ci gaba da irin wannan aiki,” in ji shi.
Wannan lamari ya faru ne kwana guda bayan da ’yan bindiga suka kai hari ƙauyukan Gatawa da Shalla da ke Sabon Birni da Isa, inda suka kashe mutane bakwai tare da yin garkuwa da mata da dama.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Bindiga yan kasuwa musayar wuta Sakkwato yan bindiga
এছাড়াও পড়ুন:
Ina nan a PDP duk da sauya sheƙar ’yan majalisar Ribas — Wike
Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya bayyana cewa har yanzu yana nan daram a jam’iyyar PDP.
Ya yi wannan bayani ne a Abuja a ranar Juma’a yayin da yake mayar da martani kan ficewar wasu ’yan majalisar dokoki na Jihar Rivers daga PDP zuwa jam’iyyar APC.
Na kashe N100bn a kan harkar tsaro a 2025 — Zulum Najeriya ta shigo da tataccen man fetur na tiriliyan 12.8 cikin watanni 15A ranar Juma’a, ‘yan majalisar Ribas guda 16, ciki har da Kakakin Majalisar, Martins Amaewhule, da suka sauya sheƙa zuwa APC.
Amaewhule, ya ce ya yanke shawarar komawa APC ne saboda rarrabuwar kai da aka samu a PDP.
Hakazalika, kakakin ya ce yana son ya yi aiki tare da Shugaba Bola Tinubu, bayan ya gano yana da kyakkyawan tsari na ciyar da ƙasar nan gaba.
Da yake magana da manema labarai bayan duba wasu ayyuka a Abuja, Wike, ya ce ’yan majalisun ba su tuntuɓe shi game da batun sauya sheƙarsu ba, amma ya ce suna da ’yancin zaɓen abin da suke so.
Ya ƙara da cewa ba duka ’yan majalisar ne suka fice daga PDP ba.
Ya ce, “Ni har yanzu ina PDP. Ba dukkaninsu ne suka fice daga jam’iyyar PDP ba. Ina ganin 16 ko 17 ne suka fice daga cikin 27. Har yanzu muna da kusan mutum 10, kuma za mu ci gaba da aiki tare da su.”
Wike, ya bayyana lamarin a matsayin abin baƙin ciki, amma ya ce kowa na da ’yancin zaɓen abin da yake so.
Ya ɗora alhakin ficewarsu kan rikicin cikin gida da PDP ke fama da shi, inda ya bayyana cewa kundin tsarin mulkin jam’iyyar ya bai wa mutane damar barin jam’iyyar idan ta rabu gida biyu.
Ya ce tun da farko ya bai wa shugabancin PDP shawara su gyara jam’iyyar, tare da gargaɗin cewa idan ba a ɗauki mataki ba jam’iyyar za ta ci gaba da yin asara.
Wike, ya ƙara da cewa suna ci gaba da ƙoƙari domin sauran mambobin PDP su haɗa kai don yaƙar jam’iyyun adawa.