Ministan Harkokin Waje na Jamhuriyar Benin, Olushegun Adjadi Bakari, ya ce kimanin sojoji 200 daga Najeriya da Ivory Coast yanzu haka na cikin kasar shi a matsayin wani ɓangare na aikin tsaro don tallafa wa gwamnati.

Ƙaramar ƙasa ta Yammacin Afirka ta girgiza da yunƙurin juyin mulkin da bai yi nasara ba a ranar Lahadi, wanda ya sa Najeriya, Faransa da Ivory Coast suka tashi tsaye wajen goyon bayan gwamnatin farar hula.

Jam’iyyar PDP ta tabbatar da mutuwar mataimakin Gwamnan Bayelsa Ɗaliban Jami’ar Unijos 8 sun mutu a hatsarin mota

“A halin yanzu akwai kusan sojoji 200 da suka zo don ba da taimako ga rundunar tsaron Benin a cikin aikin sharewa da tsaftacewa,” in ji Olushegun Adjadi Bakari ga ’yan jarida a taron manema labarai da aka yi a Abuja ranar Alhamis.

Wata majiyar tsaro daga Ivory Coast ta ce Abidjan ta turo sojoji 50 a matsayin ɓangare na wannan aiki, inda ƙungiyar ECOWAS ta bayyana cewa za a haɗa da sojoji daga Ghana da Saliyo.

Najeriya ta ce sojojinta sun isa Benin tun ranar Lahadi. ECOWAS ba ta bayyana adadin sojojin da ake sa ran za su shiga ba.

Bakari ya ce lokacin da rundunar Benin ta nemi taimako, shirin juyin mulkin “ya riga ya yi wargaje.”

Ya ce sojojin Benin masu biyayya sun fatattaki harin farko, amma lamarin na buƙatar kulawa sosai don kauce wa asarar rayukan fararen hula.

“Mun nemi goyon bayan ’yan’uwa ba saboda rundunarmu ba za ta iya ba, amma saboda Shugaban Ƙasa bai so a yi asarar rayuka masu yawa ba.”

Ya ƙara da cewa kai hari kai tsaye zuwa sansanin masu juyin mulkin na iya haifar da zubar da jini mai yawa. “Shi ya sa Shugaba Patrice Talon ya nemi goyon bayan Jamhuriyar Tarayyar Najeriya.

“Rundunar Benin ta yi nasarar fatattakar wannan yunƙurin juyin mulki, amma haɗarin asarar rayuka da dama ya sa aka buƙaci martani na haɗin gwiwa.”

Ana ci gaba da tattaunawa kan ko sojojin tsaro na yankin za su ci gaba da zama na ɗan lokaci, amma Bakari ya ce duk wani mataki “za a ɗauka ne tare da haɗin gwiwar rundunar tsaro ta Benin, wadda ta nuna jarumta.”

Yadda Najeriya ta taimaka wa Benin — Tuggar

A taron ministocin ECOWAS da aka yi a Abuja, Ministan Harkokin Waje na Najeriya, Yusuf Maitama Tuggar, ya ce saurin matakan diflomasiyya, na soja da na leƙen asiri tsakanin Najeriya da Benin ne ya taimaka wajen dakile juyin mulkin.

Tuggar ya ce lamarin ya nuna yadda za a iya kare dimokuraɗiyya idan ƙasashe makwabta suna sadarwa yadda ya kamata.

Ya ce, “Haɗin kai don tabbatar da cewa dimokuraɗiyya ta ci gaba da kasancewa a Benin ya yi nasara, kuma wannan misali ne na abin da ya kamata a yi duk lokacin da dimokuraɗiyya ke fuskantar barazana a yankinmu.”

A halin yanzu, kamfanin dillancin labarai na Reuters ya rawaito cewa Pascal Tigri, wanda ake zargi da jagorantar juyin mulkin da bai yi nasara va, tare da abokan aikinsa suna buya a Togo.

A ranar Laraba, jami’an gwamnatin Benin suka shaida wa Reuters cewa shugaban juyin mulkin yana gudun hijira a Lome 2, unguwa a babban birnin Togo inda gidan shugaban ƙasar, Faure Gnassingbe yake.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Jamhuriyar Benin Ivory Coast

এছাড়াও পড়ুন:

Sakkwatawa na murnar kisan da sojoji suka yi wa mataimakin Bello Turji

Al’ummar ƙaramar hukumar Sabon Birni da ke jihar Sakkwato sun bayyana farin ciki bayan samun labarin kashe fitaccen ɗan bindiga da ya dade yana addabar yankin gabashin jihar, Kacalla Kallamu.

Rundunar Sojoji ta 8 ta hallaka jagoran ’yan bindiga, Kachalla Kallamu, a wani samamen haɗin gwiwa da aka kaddamar a ƙaramar hukumar Sabon Birni.

Dalibin jami’a ya rasu a hatsarin motar murnar kammala jarabawa Iya sojojin da ke tsaron Seyi Tinubu sun isa su samar da tsaro a Benin – Soyinka

Wata majiyar soja da ta tabbatar da lamarin ga manema labarai a ranar Talata ta bayyana samamen a matsayin “babbar asara ga cibiyar ’yan bindigar Bello Turji,” tana mai cewa Kallamu shi ne babban na hannun daman Turji.

A cewar majiyar, an kashe Kallamu tare da wani daga cikin manyan masu samar wa Turji kayayyakin aiki a lokacin samamen da aka gudanar da safe a kauyen Kurawa ranar Litinin.

Majiyar ta ƙara da cewa aikin ya samu muhimmiyar gudunmuwar kungiyoyin sa‑kai na yankin.

“Mun dade muna bibiyar Kallamu. Kashe shi wata babbar nasara ce wajen raunana karfin ’yan bindigar da ke Sabon Birni da kewaye,” in ji majiyar.

Mamacin, wanda asalin ɗan Garin Idi ne a Sabon Birni, ya dade yana addabar al’ummar yankin.

Ana zargin ya gudu zuwa Jihar Kogi bayan ya tsere wa luguden wutar sojoji a watan Yuni 2025, amma ya sake shigowa yankin kwanan nan ba tare da an sani ba.

Majiyar ta yaba da ƙarin bayanan sirri da ake samu daga al’ummomin yankin, tana mai cewa haɗin kai tsakanin mazauna yankin da jami’an tsaro ya taka muhimmiyar rawa wajen nasarorin baya‑bayan nan.

Manema labarai sun ruwaito cewa an ci gaba da murnar labarin a Sabon Birni, yayin da mashawarcin musamman ga Gwamna Ahmad Aliyu kan harkokin tsaro, Kanal Ahmed Usman (mai ritaya), ya yaba wa dakarun bisa “ci gaba da jajircewa da ƙwarewa” wajen yaƙi da ’yan bindiga.

Mutanen garin Sabon Birni sun fito maza da mata suna murnar nasarar da aka samu, har suna cewa suna jin wannan rana kamar ta Sallah.

Sun yi fatan a ci gaba da samun nasarori irin wannan domin kawar da ’yan bindiga a yankin, a jihar, da kuma Arewacin Najeriya gaba ɗaya.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Ƴan Bindigar Daji: Jihohin Arewa 7 Sun Kaddamar Da Rundunar Fatattakar Su
  • Sakkwatawa na murnar kisan da sojoji suka yi wa mataimakin Bello Turji
  • Majalisar Dattawa Ta Bawa Tunubu Damar Kai Sojoji Zuwa Kasar Benin
  • Iya sojojin da ke tsaron Seyi Tinubu sun isa su samar da tsaro a Benin – Soyinka
  • Iya sojojin da ke tsaron Seyi Tinubu sun isa su samar da tsaro a Jamhuriyar Benin – Soyinka
  • Majalisar Dattawa ta amince Tinubu ya tura sojojin Najeriya zuwa Jamhuriyar Benin
  • Faransa ta tabbatar da sa hannunta wajen dakile juyin mulki a Benin
  • Juyin Mulki: ECOWAS ta ayyana dokar ta-baci a kasashenta
  • Najeriya: Jirgin Sojojin Kasar Yana Kan Hanyarsa Ta Zuwa Portugal, Amma Ta Sauka A Burkina Faso