Gwamnatin Kano Ta Haramta Sabuwar Hisbah Da Ganduje Ke Shirin Ƙirƙirowa
Published: 13th, December 2025 GMT
Gwamnatin Jihar Kano ta fitar sanarwar umarnin haramta kafa wa, da ɗaukar aiki da gudanar da duk wata ƙungiyar Hisbah mai zaman kanta a jihar, inda ta dakatar da ƙungiyar Independent Hisbah Fisabilillahi da tsohon gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ke shirin Ƙirƙirowa.
Kwamishinan yaɗa labarai ne ya sanar da hakan a taron manema labarai a Kano, yana mai cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya rattaba hannu kan umarnin ne domin kare zaman lafiya da kuma kare sahihancin Hukumar Hisbah ta Jihar Kano da doka ta kafa.
Umarnin ya bayyana cewa duk wani yunƙuri na ɗaukar aiki, da horarwa ko tura mutane don kafa wata Hisbah ta daban haramun ne, kuma ba shi da inganci a doka. Gwamnati ta umurci jami’an tsaro su dakatar da duk wani motsi da kuma bincikar masu ɗaukar nauyin ƙungiyar.
ADVERTISEMENTGwamnatin ta kuma gargadi jama’a da su guji shiga ko tallafa wa ƙungiyar da aka haramta, tana mai cewa duk wanda ya bin umarnin zai fuskanci hukunci bisa dokokin jihar kuma umarnin ya fara aiki nan take.
ShareTweetSendShare MASU ALAKAএছাড়াও পড়ুন:
An koro ’yan Najeriya 32 kan kasuwancin miyagun ƙwayoyi a Indiya
Aƙalla ’yan Najeriya 32 ne aka koro su daga Indiya kan zargin su da hannu a kasuwancin miyagun ƙwayoyi.
A ƙarshen watan da ya gabata, ’yan sandan Delhi da na Telangana, sun kama ’yan Najeriya 50 biyo bayan samamen da suma kai wa wata ƙungiyar safarar miyagun ƙwayoyi mai alaƙa da ƙasashen waje.
Ba ni da shirin ficewa daga PDP — Gwamnan Bauchi Cin hanci da rashawa sun yi ƙatutu a Najeriya — ICPCAna zargin mutanen da rarraba ƙwayoyi a birane da dama a Indiya, inda suke amfani da kamfanonin bayar da kaya don ɓoye ƙwayoyin da suke safara.
An gano mutanen suna da alaƙa da wani ɗan Najeriya mai suna “Nick,” wanda ake nema ruwa a jallo, kuma ana zargin yana jagorantar wannan ƙungiyar daga Najeriya.
Wasu majoyi sun bayyana cewa yana da abokan aiki aƙalla 100 a Delhi.
Masu bincike sun ce ƙungiyar tana da waɗanda ke aiki a ƙarƙashinta sama da 3,000 a Indiya kuma tana aika manyan kuɗaɗe zuwa Najeriya.
Daga cikin waɗanda aka kama, an koro ’yan Najeriya 32, yayin da wasu bakwai ke fuskantar tuhumar shari’a.
Hukumomi a ƙasar sun ana ci gaba da ce bincike.