Annabi SAW Ya Zarce Duk Sauran Annabawa Yawan Mu’uzijoji
Published: 12th, December 2025 GMT
Wata rana, Abu Huraira (RA) yunwa ta kama shi matuka, har yazu wurin mimbarin Annabi SAW da ke cikin masallacin Annabi, sai ya fadi a wurin, duk wadanda suka zo wurin suka ganshi, sai suce Allah Sarki, wane ba shi da lafiya har sai da Annabi ya zo ya ganshi, sai yace masa, Abu Hurairah kana jin yunwa ko? Sai ya amsa da eh.
Don haka, wata rana, Annabi SAW ya ta shi ya yi kuka yana tuna masoyansa a gaban Sahabbansa, sai suka ce, ya Rasulullah ba mu ne masoyanka ba, sai ya ce, A’a ku Abokaina ne, wadan can sun yi imani da ni, ba suga mu’uzija ko daya ba, ku kuma kun yi imani da ganin irin wannan abu: Nono dan kadan, a shayar da tawaga da shi, ruwa ya fito ta tsakanin ‘yan yatsu, halittarsa mai kyau, sadaukanta, jarumta, Ilimi, fasaha, cika alkawari, Amana, kyauta, ga su nan da yawa ba iyaka.
A yakin Kandak, lokacin da Sayyadina Aliyu ya kashe Amru bin Waddu (mai karfin kasar Larabawa gaba daya a zamanin) bayan ya yi wa Sayyadina Ali rawani, ya ba shi takobin shi sannan ya ce “rabbi la tazarni farda wa anta kairul warisin”, bayan ya kashe shi sai Annabi ya tambaye shi, ya kake jin kanka a yanzu? Sai ya ce, ina jin da za a tattara min mutanen Madina, zan iya kashe su gaba daya! Sai Annabi SAW ya ce masa, to shirya, akwai wani Saurayi sadauki zai fito daga wannan dajin, za ku yi yaki. Bayan fitowar saurayi sadauki, sai ya tambaya, kai ne Ali? wurinka aka turo ni, yau daya ne zai tsira tsakanin ni da kai, bayan gwabzawa, saurayi ya yi wata wujijjiga da Sayyadina Ali, nan take ya ga ne cewa, wannan saurayi ba kowa ba ne face SAW. Don babu wani da ya isa ya yi wa Sayyadina Ali irin haka duk duniya sai Annabi SAW, sai ya fahimci cewa, akwai sama da shi. Fakrurrazi mai Hadisi ne ya fitar da wannan Hadisin.
15 – Annabi Adam da duk ‘ya’yansa Annabawa suna karkashin tutar Annabi Muhammad SAW a ranar Alkiyama: wannan ya tabbatar cewa, duka Annabawa suna kasa da shi. Ya zo cikin Hadisi Annabi SAW yana cewa, “ana sayyadi waladi Adam wala fakr – ni ne shugaban ‘ya’yan Annabi Adam ba alfahari ba”, sabida Manzon Allah SAW, zuciyarsa tana da fuska biyu – yadda yake kallon hadarar Allah da yadda ya ke kallon bayin Allah. Don haka, Annabi SAW in yana gaban Ubangiji, sunan shi “Abdu”, amma in ya taho wurinmu sauran bayi, shugabanmu ne. Annabi Yahya a wurinmu ma, Ubangiji kiranshi ya yi da cewa, “Sayyidan wa hasuran wa nabiyyan minassalihin – Shugaba, katangagge kuma Annabi daga cikin managarta bayi”
A wani wuri kuma, Annabi SAW ya ce, babu wanda zai shiga Aljannah daga Annabawa kafinsa SAW, kuma babu wata al’umma da za ta shiga daga al’ummomin da suka gabata kafin al’ummarsa SAW! Duka wannan saboda albarkar Annabi SAW.
An ruwaito hadisi daga Anas bin Malik yana cewa, manzon Allah SAW ya ce, “ni ne farkon halitta wanda zai fara fita daga kabari idan an tashi al’umma a ranar Alkiyama, ni ne wanda zan wakilce su wurin yin bayani a gaban Ubangiji don kowa ya tsira, ni ne zan yi musu bushara idan gwiwoyinsu sun sage sun ga kamar ba za su tsira ba, tutar godiya tana hannuna, ni ne mafi girman dan Adam a wurin Ubangijina, kuma ba alfahari nake ba, cewa aka yi in fada, “wa amma bini’imati rabbika fahaddis – ka bayyana ni’imomin Ubangijinka a gareka”.
Wannan magana da Annabi ya fada wa Sahabbansa, ita muke kira da Maulidi. A tara Jama’a a fada musu girma da darajar fiyayyen halitta, Annabi Muhammad SAW.
An karbo Hadisi daga Abdullahi bin Abbas yana cewa, wasu daga cikin sahabban Annabi SAW sun taru suna hirar karatu, sai wasu suka ce, ” ittakazallahu Ibrahima kalila – mamakin yadda Allah ya riki Annabi Ibrahim Badadi (Kalila)”, wasu kuma suka ce, “wannan ai ba abin mamaki ba ne, kamar yadda Ubangiji ya yi hira da Annabi Musa, – wakallamallahu Musa taklima,” wasu kuma suka ce, ina kuka bar Annabi Isa, “Kalimatullahi wa ruhuhu – Kalmar Allah kuma ruhinsa yadda ya dace da shi”, wasu kuma Adamu “isdafahu – Allah ya zabe shi”, kuma duk babu wanda ya san Annabi SAW yana jinsu.
Da Annabi SAW, ya fahimci abun na su ya ki kare wa kuma suna shirin fadawa hadari, sai ya fito ya dakatar da su, ya ce musu, na ji duk batutuwanku da hujjojinku, kuma duk abinda kuka fada haka ne! Kun ce, “Annabi Ibrahim Kalilullah, Musa kalimullahi wa najiyyahu, Adamu isdafahu, duka haka ya ke, amma duk ku saurara kuji! Ni Habibullahi ne ba alfahari ba, saboda mukamin na shi ne! Ni nake rike da tutar godiya, ni ne wanda zai yi ceto, ni ne farkon wanda za a karbi cetonsa a ranar Alkiyama, ba alfahari ba! Ni zan fara kwankwasa kofar Aljannah don a bude, sai a bude in shiga, tare da ni akwai Mu’uminai fukara’u.
Don haka, ya tabbata a hadisi, ranar Alkiyama, ana neman ceto, kowa ya dimauce, sai a tafi wurin Annabi Adam, ya ce, ba ni ba, sai a tafi wurin Annabi Musa, shi ma ya ce ba ni ba, a tafi wurin Annabi Isa, shi ma haka, a tafi wurin Annabi Ibrahim shi ma haka, amma dai a tafi wurin Rasulullah SAW.
A ranar Alkiyama, bayan Annabi SAW ya bude kofar shiga Aljannah, Shahidai za su taho zuwa shiga Aljannah, sai a tambayesu, waye ya kira ku? Sai suce Malamai suka gaya mana cewa, mune farko, sai a ce musu, to kubari Malamai su fara shiga; Malamai da jin haka, sai su ta so za su shiga, sai a tambayesu, ku su waye? Sai su ce, mu ne Malamai, to ya aka yi kowa bai zama Malami ba sai ku kadai, sai suce, saboda duk sun tafi wurin neman abinci muka muna wurin koyon ilimi, to ku ba ku cin abinci? Muna ci, wasu ne suka dauki nauyin cin abincinmu, to ku bari masu ciyarwa su fara shiga. Don haka, sai mai ciyarwa ya fara shiga Aljannah, sannan Malami sannan Shahidi.
Annabi SAW, ya kara ce musu, kuma ni ne mafificin mutanen farko da na karshe, ba alfahari ba!
ShareTweetSendShare MASU ALAKAকীওয়ার্ড: Annabi SAW ya ce a ranar Alkiyama A ranar Alkiyama Sai Annabi SAW sai Annabi SAW ba alfahari ba Annabi SAW Ya Sayyadina Ali Abu Huraira
এছাড়াও পড়ুন:
’Yan jaridar Daily Trust da Trust TV sun lashe kyautar binciken ƙwaƙwaf ta Wole Soyinka ta bana
Jaridar Daily Trust da gidan talabijin na Trust TV, dukkansu mallakar kamfanin Media Trust, a bana ma sun sake yin fice bayan ’yan jaridansu suka lashe kyautar binciken kwakwaf ta Wole Soyinka ta bana.
’Yan jaridar na Daily Trust da Trust TV, Afeez Hanafi da Muslim Muhammad Yusuf, sun lashe gasar ne a matsayin zakaru a rukunin rahoton jarida da kuma na talabijin mafi daraja a bana a Najeriya.
Majalisar Dattawa ta amince Tinubu ya tura sojojin Najeriya zuwa Jamhuriyar Benin Sojoji sun kashe ’yan bindiga 13, sun ceto ’yan kasuwa a SakkwatoHanafi ya lashe rukuni na rubutu bisa labarinsa mai taken: “Bincike: Dan jarida ya samu ayyuka biyu da takardun bogi na Oluwole.”
Wanda ya zo na biyu da na uku a rukunin na rubutu su ne Kingsley Jeremiah da Ann Godwin, dukkansu daga jaridar The Guardian.
Sai dai kamar yadda aka saba, babu wanda ya lashe kyautar a rukuni na rediyo, kuma babu wanda ya fito a matsayin na biyu ko na uku.
A rukuni na yanar gizo, Theophilus Adeokun na National Record ya lashe gaba ɗaya da labarinsa mai taken: “Dangote, a neman makamashi mai arha, yana zubar da guba cikin kogunan Binuwai.”
Wanda ya yi na biyu shi ne Kunle Adebajo daga HumAngle, yayin da Isah Ismaila, shi ma daga HumAngle din ya zo na uku.
A rukunin hoto kuwa, Elliot Ovadje na jaridar Punch ya fito a matsayin zakara, sannan shi ɗin ne ya sake fitowa a matsayin na biyu da na uku.
A bangaren girmamawa, tsohon Alkalin Kotun Ƙoli, Justice Ayo Salami, ya samu kyautar mai rajin kare hakkin dan Adam, yayin da fitaccen marubuci kuma mawaki, Odia Ofeimun, ya samu kyautar kwarewa a aikin jarida.
Tun kafin gabatar da kyaututtuka, shugabar alkalai ta shekarar 2025, Abigail Ogwezzy‑Ndisika, a jawabinta ta ce an samu shigar da rubuce‑rubuce 180, amma aka tace su zuwa 129.
Ta jaddada abubuwan da aka yi amfani da su wajen tantance kowanne rubutu da suka hada da jarumta, zurfi, daidaito, tasiri da kuma jajircewa ga muradun jama’a.
“Mun yi wannan aikin ne daban‑daban kuma ba tare da katsalandan ba, ta amfani da wasu ka’idoji da suka shafi rufe batutuwan cin hanci, take hakkin ɗan adam, laifuka da ayyukan ɓoye, da kuma kyawawan hanyoyin binciken jarida,” in ji ta.
Marubucin da aka saka wa gasar sunansa kuma mai lambar yabo ta Nobel, Wole Soyinka, ya taya dukkan wadanda suka samu kyautar murna, yana mai gargadin kada su yi sakaci.
“Wasu daga cikin jaruman da za su ceci wannan ƙasa za a same su a cikin kafafen yada labarai. Amma a lokaci guda, dole ne in roƙi kafafen yada labarai su yi dada takatsantsan, su yi bincike mai zurfi kan abin da suke wallafawa. Akwai labarai masu yawa da ake wallafawa da ba daidai ba ne,” in ji shi.
Ya kuma yi kira ga jaridun da su inganta rahotanninsu, yana nuna damuwa kan yawan labaran karyar da ke yawo a kafafen sada zumunta.