Yadda APC Da ADC Ke Amfana Da Rikicin Jam’iyyar PDP
Published: 12th, December 2025 GMT
PDP wanda ke da gwamnonin 11 bayan zaben 2023, yanzu tana da biyar kawai tare da karin wasu suna nuna suna son barin jam’iyyar.
Yawancin gwamnonin da suka sauya sheka a cikin wannan lokaci sun koma APC, yayin da jam’iyyar Accord ta samu guda daya.
Gwamnonin da suka bar PDP zuwa APC su ne Umoh Eno na Akwa Ibom da Sheriff Oborebwori na Delta da Douye Diri na Bayelsa da Peter Mbah na Jihar inugu.
Akwai fargaba cewa gwamnonin Caleb Muftwang na Jihar Filato da gwamnan Zamfara, Dauda Lawal ma na iya canza sheka. Gwamnonin PDP kadai da suka bayyana a fili cewa za su tsaya cikin jam’iyyar don gyara al’amuran gida su ne gwamnan Jihar Bauchi, Bala Muhammad da abokin aikinsa na Jihar Oyo, Seyi Makinde, yayin da Ahmadu Umaru Fintiri na Adamawa ya bayyana tamkar yana son sauya sheka.
Rikicin PDP y afara kuno kai ne tun bayan zabukan 2023, baya ga gwamnoni, jam’iyyar ta rasa karin ‘yan majalisa, ciki har da manyan mambobin majalisar tarayya zuwa APC.
Daga cikin ‘yan majalisar tarayya da suka bar tsohuwarsu zuwa APC akwai Sanata Agom Jarigbe daga Jihar Kuros Ribas da Sunday Marshal Katung daga Kaduna.
Tun daga shekarar 2023 har zuwa yanzu, jam’iyyun adawa a majalisar wakilai sun rasa akalla mambobi 66 zuwa jam’iyyar APC mai mulki.
Babbar jam’iyyar adawa ta PDP wadda ta rasa ‘yan majalisu 44, sai LP 14, NNPP 6, ADC 1 da YPP 1.
A lokacin da aka kaddamar da majalisar a watan Yuni 2023, tsarin majalisar wakilai ya kasance APC tana da kujeru 178, PDP 115, LP 35, NNPP 19, APGA 5, SDP 2, YPP 2 da ADC 2.
Bayan guguwar sauya sheka, yawan ‘yan majalisar yanzu sun kasance kamar haka: APC 246, PDP 71, LP 21, NNPP 13, APGA 5, SDP 2, ADC 1 da YPP 1.
A ranar Juma’a da ta gabata, mambobi 16 na majalisar dokokin Jihar Ribas karkashin jagorancin shugaban majalisan, Martin Amaewhule, sun sauya sheka daga PDP zuwa APC.
Lokacin da aka kaddamar da majalisar dokoki ta kasa ta 10 a ranar 13 ga Yunin 2023, jam’iyyar APC ta rike kujeru 59 a majalisar dattawa.
Amma jam’iyyar ta kara tumbatsa zuwa samu sanatoci 76, ta wuce kashi biyu bisa uku na samun rinjaye, bayan samun sauya sheka da ‘yan majalisar dattawan suka shiga cikinta.
Lokacin da aka amince da ADC a matsayin jam’iyyar hadaka ta tsofaffin shugabannin PDP, jam’iyyar ta sami sabon rayuwa tare da shigowar manyan mambobin PDP da suka hada da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar da tsohon shugaban majalisar dattawa, Dabid Mark da tsohon gwamnan Jihar Osun, Rauf Aregbesola da wasu.
Yawan wadanda ke barin PDP suna shiga APC ne, yayin da kadan daga ciki suke shiga ADC.
Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir Elrufai ya sauya sheka daga APC zuwa SDP, sannan daga baya ya shiga ADC.
PDP ita ce kawai babbar jam’iyya da ba ta amfana daga guguwar sauyin sheka ba, amma tana ci gaba da rasa babban adadin mambobinta.
Wani masanin siyasa kuma farfesa a fannin kimiyyar siyasa, Gbade Ojo, wanda ya yi magana da wakilinmu kan wannan batu, ya lura cewa rushewar jam’iyyun adawa yana da babban tasiri wajen yawan tserewar mambobi, yana mai cewa hakan ya kara rage gwarin gwiwar al’ummar Nijeriya.
“Idan ka kalli majalisa, APC yanzu tana da gagarumi rinjaye a duka majalisar wakilai da majalisar dattawa. Ayyukan sa ido nasu suna da rauni sosai saboda shugaban kasa ya nada jami’an da su ne za su je su gudanar da ayyukan sa ido a kansu. Amma yawancinsu yanzu suna cikin jam’iyyar gwamnati,” in ji shi.
Sau da dama PDP ta yi kokari dawo da martabar jam’iyyar. Ta gudanar da babban taro a matakin gundumomi da karamar hukumomi da jihohi da dama kuma kasa baki daya, inda mambobi suka zabi sabon shugaban jam’iyyar na kasa.
Amma lamarin ya ci tura, inda magoya bayan ministan Abuja, Nyesom Wike suka kalubalantar babban taron.
Wasu na cewa ko da an gudanar da babban taron zaben, jam’iyyar ta kasa haifar da irin amincewar da zai sa mambobinta su ci gaba da kasancewa wuri guda.
Duk da yake akwai alamun da ke cewa ko wadanda suka saura na iya barin jam’iyyar a kowane lokaci.
Masana na cewa ci gaban rikicin a jam’iyyar da shari’o’i da dama na iya sanya ‘yan takararta a 2027 cikin hadari ta fuskar doka, musamman gwamnonin da ke neman wa’adi na biyu su nemi wasu jam’iyyar.
A hankali, ADC tana samun karuwa a matsayin babban jam’iyyar adawa a kasar, tana matsar da PDP zuwa baya, wacce ta rike wannan matsayi tun bayan ta fadi a zaben shugaban kasa a 2015, zuwa matsayi na biyu.
A kwanan nan, jam’iyyar ta ce tana shirin karbar sama da mambobin majalisar ta 10 guda 100 kafin zaben shekarar 2027.
A halin yanzu APC na da yawancin ‘yan majalisa a duka majalisun dokoki kasar nan tare da zargin cewa wasu na shirin shiga jam’iyyar.
Akwai rahotannin da ke cewa a jihohi kamar Benuwai, Kano, Adamawa da Yobe cewa ADC ta kafu kuma za ta bunkasa c
ikin ‘yan watanni kadan masu zuwa.
ShareTweetSendShare MASU ALAKAকীওয়ার্ড: gwamnan Jihar jam iyyar ta a jam iyyar a majalisar sauya sheka jam iyyar A jam iyyar a
এছাড়াও পড়ুন:
Farashin Kayan Abinci Na Sauka Yayin Da Bikin Kirsimeti Da Sabuwar Shekara Ke Matsowa
A Legas farashin shinkafa ya fadi sosai
A kasuwannin Mushin da Daleko, farashin buhun shinkafa kilo 50 da ake sayar da shi a da Naira N75,000 cikin Nuwamba, a yanzu ya dawo Naira 54,000.
Jihar Delta
A Jihar Delta, musamman a Asaba, farashin kayan abinci ya daidaita a manyan kasuwanni irin su Kasuwar Oko (Hausa), Midwifery Market da Ogbogonogo Market, sai dai a kasuwannin mako-mako na kauyuka.
Bincike a babban birnin jihar ya nuna cewa farashin muhimman kayan abinci ya dan daidaita, amma ‘yan kasuwa da masu sayayya sun nuna damuwa kan karancin kudin da ake da shi don sayayya.
Kwandon tumatir da ake sayarwa Naira 5,000 a wasu watanni da suka gabata, yanzu ya sakko Naira 4,000. Farashin doya ya tsaya a tsakanin Naira 1,800 zuwa Naira 2,000 kowace guda, yayin da garri yake kan Naira 3,000 gwangwani, ba tare da sauyi ba duk da lokacin girbi.
A Kasuwar Ogbogonogo, wata mai girki, Mrs Beatrice Nnamdi, ta ce wasu kayan abinci har yanzu suna da tsada duk da zuwan sabbin kayan abinci.
“Talon shinkafa yanzu yana tsakanin Naira 60,000 zuwa Naira 65,000. A da yana tsakanin Naira 90,000 zuwa Naira120,000. Buhun wake yanzu Naira 50,000. Mun taba sayarwa a nan tsakanin Naira70,000 zuwa Naira 90,000,” in ji ta.
“A lokacin girbi, idan doya, masara da dankali suka fara fitowa, ya kamata garri ya yi sauki. Tumatir yanzu yana tsakanin Naira 7,500 zuwa Naira 8,000, gwangwani Wake da shinkafa sun sauka kadan daga Naira 6,000 zuwa Naira 5,500 gwangwani,” a cewarta.
Jihar Yobe
Manoma a wasu sassan Jihar Yobe, musamman a cikin da kewaye da Damaturu, babban birnin jihar, na fama da mummunan tasirin fari wanda ya busar da amfanin gona saboda karancin ruwan sama.
Da dama daga cikin manoma da mazauna yankunan da abin ya shafa sun bayyana fargaba matuka game da karancin ruwan sama a bana, wanda suka ce ya rage girbinsu kuma ya kara tsananta yanayin rayuwarsu.
Wasu daga cikin manoman sun shaida wa LEADERSHIP Weekend cewa karancin ruwan sama a wannan yanki, idan aka kwatanta da wasu sassan jihar da suka samu isasshen ruwan sama, ya sa amfanin gona irin su masara, gero da shinkafa suka bushe, kuma hakan na iya jawo karancin abinci a gaba.
Daya daga cikin manoman, Mallam Bukar Abba, mazaunin Damaturu, ya ce fari da ya biyo bayan karancin ruwan sama ya bar amfanin gona suna bushewa.
Bukar ya ce ruwan sama ya tsaya da wuri, kuma lokutan da ya yi, zuba yayyafi ne kawai ba wanda zai wadatar don ciyar da amfanin gona ba.
Ya kara da cewa ruwan saman bana ya bar manoma da fargabar tsaro a fannin abinci, inda ya nuna cewa da dama daga cikin manoma sun yi asarar miliyoyin naira saboda amfanin gonar bai kai lokacin girma ba kafin ya bushe.
Wani manomin da ke kuka da halin fari, Mohammed Salisu, mazaunin Karamar Hukumar Gashua, ya ce karancin ruwan saman ya yi mummunan tasiri sosai domin ya lalata hanyar samun rayuwarsu.
Jihar Kaduna
A Kaduna, wani mai sayar da kayan abinci na Kasuwar Sabon Tasha, Elias Samson, ya ce farashin kayan abinci ya ci gaba da daidaituwa tun bayan da gwamnatin tarayya ta rage farashin abinci.
“Farashin abinci yana fara tashi ne a watan Disamba, kusa da Kirsimeti, amma a halin yanzu farashin yana nan yadda yake. Ka san manoma har yanzu suna girbe masara, wake, shi ya sa ake da tsoffin kayan abinci da sababbi a kasuwa yanzu. A lokacin girbi farashi ba ya tashi haka kawai,” in ji shi.
Wata mai sayen kayan abinci, Laadi Onoja, ta ce: “Farashin abinci har yanzu yana da kyau idan aka kwatanta da yadda muke saya wasu watanni da suka gabata. Lokacin cunkoso shi ne watan Disamba, kuma a wancan lokacin wasu dillalai kan kara kudi domin samun karin riba.
Na sayi mudu daya na shinkafa mai tsabta Naira 1,800 kuma wasu wurare suna sayarwa Naira 1,700 musamman a kasuwannin kauye.”
Jihar Kogi
An samu daidaituwar farashin kayan abinci a Lokoja, babban birnin Jihar Kogi, matuka, ban da naman Sa wanda ya rika tashi a ‘yan watannin nan.
Lokacin da LEADERSHIP Weekend ta ziyarci sabuwar kasuwa a Lokoja, ana sayar da shinkafa Naira 7,000 maimakon farashin da ya kai Naira 14,500 a da.
Wata ‘yar kasuwa mai sayar da shinkafa da wake, Hajiya Lami Sule, ta ce babu wani tashin farashi da aka samu kan kayan abinci.
Sai dai a wajen sayar da nama, lamari ya bambanta domin farashin kilo daya na nama yana kara tashi kullum.
Wani mutum mai matsakaicin shekaru, Ismail Jegede, ya ce: “Ban da farashin nama, farashin sauran kayan abinci ya yi tsaya dai-dai a kasuwannin baya guda biyar. Kilo daya na nama da muke saya tsakaninNaira 3,500 zuwa Naira 4,500 yanzu ana sayar da shi Naira 6,000.”
Shi ma wani mai sayar da nama a sabuwar kasuwar Lokoja, Mallam Danladi Abu, ya danganta tashin farashin namansa ga kudin sufuri da kuma matsalar tsaro.
“Dole mu je wurare masu nisa domin samun shanu saboda rashin tsaro. Mafi nisan wurin da muka tafi, shi ne mafi tsadar jigilar dabbar,” in ji shi.
Jihar Akwa Ibom
A yayin haka, farashin yawancin kayan abinci na yau da kullum, kamar garri, wake, shinkafa, albasa, barkono da sauran su, ya kasance daidai, a cewar binciken da aka gudanar a manyan kasuwanni a Uyo, da kuma Kananan Hukumomin Itu da Etinan.
Kodayake har yanzu ya yi wuri a yi hasashen abin da zai faru domin har yanzu jihar ba ta fuskanci cunkoson jama’ar bukukuwan shekara ba, farashin kayayyaki ya kasance a daidaitacce a kasuwannin Akpan Andem Market (Uyo), Itam International Market (Itu) da Okpokpo Market (Etinan).
Garri, wanda a baya ake sayar da kofi 5 zuwa 6 kan Naira 1,000 bayan shugaba Tinubu ya hau mulki, yanzu ana samun kofuna 12 zuwa 13 akan farashi guda.
Buhun shinkafa, da a baya yake tsakanin Naira 70,000 zuwa Naira 80,000, yanzu yana tsakanin Naira 38,000, Naira 47,000 zuwa Naira 60,000 gwargwadon inganci da nau’in hatsi.
Farashin wake ya sauka daga Naira 450 zuwa Naira 500 zuwa Naira 250 zuwa Naira 300.
Naman Sa kuwa ya ci gaba da kasancewa mai tsada tsakanin Naira 3,000 zuwa Naira 3,200 kowane kilo, yayin da farashin kaji ya sauka daga Naira 10,000 zuwa Naira 15,000 zuwa Naira 6,000.
Wani dillalin hatsi daga Sokoto, Adamu Isa, ya danganta saukar farashin da matakin da gwamnatin Jihar Akwa Ibom ta dauka na rusa kungiyoyin kasuwa a manyan kasuwanni.
Wani dillalin dabbobi, Abubakar Garba, ya bayyana cewa matakin Gwamnonin Nijeriya (NGF) na kawar da harajin kan tituna toll points “shima babban dalili ne da ya taimaka wajen rage farashin muhimman kayan masarufi.”
ShareTweetSendShare MASU ALAKA