Sin Ta Karbi Shaidu Daga Rasha Dangane Da Tawagar Aikin Sojin Japan Mai Lamba 731
Published: 14th, December 2025 GMT
Kasar Sin ta karbi shaidu daga Rasha, dangane da tawagar aikin sojin kasar Japan mai lamba 731, rukunin da ya kware wajen amfani da kwayoyin cuta domin yaki, a yayin yakin duniya na biyu.
A cewar hukumar koli ta tattara kayan tarihi, Sin ta samu kwafin bayanai, ciki har da takardun shari’u da aka yiwa dakaru membobin tawagar ta 731, da rahotannin bincike dangane da laifukan da tawagar ta tafka, da takardun musayar bayanan hukuma na tsohuwar tarayyar Soviet, tsakanin 11 ga watan Mayun shekarar 1939 zuwa ranar 25 ga watan Disamban 1950.
Yayin yakin duniya na biyu, dakarun mamaya na kasar Japan, sun kafa wata cibiyar amfani da kwayoyin cuta domin yaki a sassa daban daban na Asiya, inda ta kafa tawaga mai lamba 731 a birnin Harbin, na lardin Heilongjiang dake arewa maso gabashin kasar Sin, wurin da ta rika gwajin nau’o’in kwayoyin cuta kan bil’adama.
ADVERTISEMENTA kalla Sinawa, da al’ummun tarayyar Soviet, da na wasu kasashe da yankuna har mutane 3,000, tawagar ta 731, ta yi gwajin kwayoyin cututtuka masu hadari a kansu. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
ShareTweetSendShare MASU ALAKAএছাড়াও পড়ুন:
Sin Ta Yi Kira Da A Gaggauta Tsagaita Bude Wuta A Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo
Kwamitin tsaron MDD ya gudanar da taron tattauna halin da ake ciki a Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo a jiya Jumma’a, inda ya mayar da hankali ga batun tabarbarewar yanayin tsaro a gabashin kasar, da kuma wa’adin aikin tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD dake kasar ko MONUSCO a nan gaba.
A gun taron, wakilin Sin ya bukaci kungiyar ’yan tawaye ta Kongo, da ta gaggauta tsagaita bude wuta nan take, yana mai kira da a warware sabani ta hanyar tattaunawa ta gaskiya, da kuma soke takunkumi kan ayyukan MONUSCO, da kuma daidaita wa’adin aikin MONUSCO zuwa lokacin kyautatuwar yanayi a kasar, ta yadda za a tabbatar da amincin MONUSCO da kwamitin tsaron MDD. (Safiyah Ma)
ADVERTISEMENT ShareTweetSendShare MASU ALAKA