Dan bindiga ya kashe sojojin Amurka biyu da wani farar hula a Siriya
Published: 14th, December 2025 GMT
Wani dan bindiga ya kashe sojojin Amurka biyu da wani farar hula a yankin hamada na Palmyra a Syria.
Kafofin yada labarai sun bayyana harin da na wani dan bindiga daga kungiyar IS.
An sanar da hakan a cikin wata sanarwa da rundunar sojin Amurka ta tsakiya (CENTCOM) ta fitar, inda ta kara da cewa an kashe dan bindigar.
Shugaba Donald Trump ya yi alkawarin cewa Amurka za ta mayar da martani ga harin.
Wani jami’in sojan Siriya, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce harbin ya faru ne a lokacin da jami’an Siriya da na Amurka ke taro a hedikwatar tsaron Siriya da ke Palmyra.
Siriya ta yi ikirarin cewa sojojin kawancen kasa da kasa karkashin jagorancin Amurka sun yi watsi da gargadin da akayi musu game da barazanar shiga yankin.
A lokacin ziyarar shugaban rikon kwarya na Siriya Ahmed al-Sharaa a Washington a watan da ya gabata, Damascus ta shiga kawancen kasa da kasa da Amurka ke jagoranta na yaki da ISIS.
Wannan shi ne karo na farko da aka ruwaito irin wannan lamari a Siriya tun bayan kulla dangantaka ta kud da kud da Amurka.
Siriya ta “yi Allah wadai” da abin da ta kira da na ta’addanci.”
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Mutum biyu sun mutu a harbin bindiga a Jami’ar Brown ta Amurka December 14, 2025 Shugabannin kasashen (ECOWAS) na taro a Abuja December 14, 2025 Kasashen AES zasu kafa bankin dogaro da kai December 14, 2025 Sheikh Na’im Kassim: Idan Duniya Baki Daya Za Ta Taru, Ba Wanda Zai Iya Kwace Makaman Hizbullah December 13, 2025 DRC: Kungiyar M23 Ta Kwace Iko Da Wani Gari Mai Muhimmanci December 13, 2025 Syria: Sojojin “Isra’ila” Sun Kutsa Cikin Yankin Qunaidhara December 13, 2025 Kalibaf: Iran Da Habasha Suna Bunkasa Alakokin Siyasa Da Tattalin Arziki December 13, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan(a) 171 December 13, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan(a) 170 December 13, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan(a) 169 December 13, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Sojoji sun kashe ’yan ta’adda 2, sun ƙwato makamai a Borno
Dakarun Sojin Rundunar Operation Haɗin Kai, sun kashe ’yan ta’adda biyu a wani samame da suka kai yankin Shettimari da ke Ƙaramar Hukumar Konduga, a Jihar Borno.
Majiyoyi sun shaida cewa rundunar ta kai harin ne ƙarƙashin Operation Desert Sanity V da safiyar ranar Alhamis.
Osimhen ya lashe kyautar gwarzon ɗan wasan bana na Turkiyya Sojoji sun kashe ’yan bindiga 3 a BinuwaiWata majiyar soji ta ce, “Sojojin sun tare mayaƙan a kusa da inda suka ke shirin kai hari a yankin da misalin ƙarfe 1:20 na dare.”
Ya ƙara da cewa, “Sojojin sun yi nasarar daƙile ’yan ta’addan nan take, inda suka kashe biyu daga cikinsu yayin da wasu suka tsere.”
Bugu da ƙari, majiyar ta ce daga baya an gano wasu bama-bamai guda biyu da kuma wani gidan harsashi guda ɗaya mai ɗauke da harsasai 23 masu ɗangon 7.62mm x 39mm da ’yan ta’addan suka watsar yayin tserewa.
Majiyar ta ƙara da cewa, “Babu wanda ya mutu a cikin sojojin, sai dai daga baya tawagar sojojin sun ci gaba da aikinsu.”