Aminiya:
2025-09-20@15:31:27 GMT

’Yan bindiga sun kashe basarake, sun tarwatsa mutane a Sakkwato

Published: 20th, September 2025 GMT

Wasu ’yan bindiga da ake zargin Lakurawa ne, sun kai hari ƙauyen Sayinna, da ke Ƙaramar Hukumar Tangaza a Jihar Sakkwato.

Sun kashe Hakimin ƙauyen, Malam Murtala Sa’adu, tare da wani mutum mai suna Ibrahim Mai-Kuɗi.

Yadda za ka dawo da kuɗinka da ka yi kuskuren turawa wa wani An tsinci gawar kwamandan hukumar NDLEA a otel a Kalaba

Mai bai wa shugaban Ƙaramar Hukumar Tangaza shawara, Alhaji Gazali Raka ne, ya tabbatar da harin.

Ya ce maharan sun kashe hakimin ne saboda yana taimaka wa ’yan sa-kai wajen tsaro a yankin.

An ce maharan sun shiga ƙauyen ne da misalin ƙarfe 1:30 na daren ranar Alhamis, inda suka dinga harbi a ko ina.

Bayan sun kashe mutanen biyu, sai suka tsere zuwa cikin daji.

Sojojin Operation FANSAN YANMA sun isa yankin, inda suka ɗauki gawarwakin zuwa asibiti.

Rahotanni sun nuna cewa Lakurawa sun kai hare-hare a wasu ƙauyuka na ƙananan hukumomin Kebbe da Tambuwal, inda suka ƙone gidaje, suka kwashe kaya, kuma suka tilasta mutane yin gudun hijira.

A ƙaramar hukumar Kebbe, ƙauyuka kamar Fakku, Sha’alwashi, Tulluwa, Bashi Bakin Dutse da Rafin-Gora sun zama kufai saboda mutane sun tsere.

Hakimin Fakku da iyalansa sun bar garin, sun tsere zuwa Koko a Jihar Kebbi, inda suka haɗu da ɗaruruwan ’yan gudun hijira daga yankin.

Matsalar tsaro a Jihar Sakkwato na ƙara ta’azzara, kuma jama’a na kira gwamnati ta ɗauki matakan gaggawa don kawo ƙarshen lamarin.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: hari Lakurawa Sakkwato

এছাড়াও পড়ুন:

’Yan bindiga sun sako ma’auratan da suka sace a Katsina bayan biyan N50m

Wani ɗan kasuwa a Jihar Katsina mai suna Anas Ahmadu da matarsa, Halimatu wadda ke ɗauke da juna biyu, da kuma ’yarsu mai shekaru biyu, sun kuɓuta daga hannun ’yan bindiga, bayan sun shafe kwanaki 21 a hannunsu.

An sako su ne a daren ranar Laraba bayan biyan kuɗin fansa Naira miliyan 50, kamar yadda wani ɗan uwansu ya bayyana wa Aminiya.

Gobara ta kashe manyan jami’an hukumar FIRS 4 a Legas NAJERIYA A YAU: Wadanne Kalubale Gwamna Fubara Zai Fuskanta Bayan Dawowa Mulkin Ribas?

“Alhamdulillah! Anas, Halimatu da ’yarsu sun kuɓuta. Yanzu haka suna kan hanyarsu ta zuwa gida, amma sai da aka biya ’yan bindigar kuɗin fansa Naira miliyan 50,” in ji shi.

An sace su ne a ranar 26 ga watan Agusta, 2025 a gidansu da ke Filin Canada Quarters, a Jihar Katsina.

Da farko, mahafan sun nemi Naira miliyan 600, daga baya suka rage kuɗin zuwa miliyan 100, sannan daga ƙarshe suka amince aka biya su miliyan 50.

Saboda dalilan tsaro, ’yan uwansu ba su bayyana inda aka sako su ba.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Ajali: Wasu Ƴan Ƙauye Sun Gujewa Ƴan Bindiga Sun Nutse A Ruwa
  • Sudan: Rundunar Daukin Gaggawa ( R.S.F ) Ta Kashe Mutane 75 A Wani Hari Da Ta Kai Wa Masallaci A Garin Al-Fasha
  • An dakatar da shugabannin sakandare 6 a Sakkwato kan zargin cin amanar aiki
  • Mutum 1,666 ne suka kashe kansu a Legas cikin shekaru biyar – ’Yan sanda
  • Cutar Kwalara ta kashe mutum 58 a Bauchi
  • Yadda jariri ya rasu a bayan mahaifiyarsa yayin tsere wa harin ’yan bindiga a Neja
  • Fasahar AI ta gano cutar da za ta kama mutane a shekara 10 masu zuwa
  • ’Yan bindiga sun sako ma’auratan da suka sace a Katsina bayan biyan N50m
  • An kama ɗaya daga cikin manyan kwamandojin IPOB