Hafsan sojin ƙasa ya buƙaci sabbin dakaru su zama masu kishin ƙasa
Published: 14th, December 2025 GMT
Rundunar Sojojin Najeriya, ta yaye sabbin dakarun soji guda 3,439, bayan kammala ɗaukar horo a cibiyar horar da sojoji da ke Zariya, a Jihar Kaduna.
Babban Hafsan Sojin Ƙasa, Laftanar Janar W. Shaibu, ya yaba wa sabbin sojojin bisa jajircewa, haƙuri da ƙwazon da suka nuna tsawon watannin da suka yi suna karɓar horo.
Janar Shaibu, ya bayyana hakan ne a wajen bikin yaye sojojin, inda ya ce wannan nasara na nuni da ƙoƙarin rundunar soji na ƙara yawan ma’aikata domin fuskantar matsalar tsaro a ƙasar nan.
Ya taya sabbin sojojin murna, inda ya bayyana cewa kammala horon shi ne mataki na farko na rayuwar sadaukarwa, kishin ƙasa da hidimta wa jama’a.
A cewarsa, sabbin sojojin sun shiga rundunar a lokaci mai muhimmanci, ganin yadda ƙasar ke fuskantar matsalolin tsaro da dama.
Ya buƙace su da su kasance masu gaskiya, ladabi da bin doka a duk inda aka tura su aiki.
Babban Hafsan ya ƙara da cewa horon da aka ba su ya horar da su yadda za su iya fuskantar aikin soja a zamanance tare da sauran hukumomin tsaro.
Ya kuma yaba wa Kwamandan Depot NA, Janar Ahmadu Bello Muhammad, da jami’an da kw horar da sojoji bisa ƙoƙarin da suka yi wajen ganin horon ya gudana cikin nasara.
Ya ce buɗe sabbin cibiyoyin horo a Osogbo da Abakaliki zai ƙara wa rundunar ƙarfin karɓar sabbin sojoji.
Haka kuma, Janar Shaibu ya gode wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmad Tinubu bisa goyon bayan da yake bai wa rundunar soji, tare da jinjina wa Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, da Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli, da al’ummar Zariya saboda kyakkyawar alaƙa da sojoji.
Ya kuma taya iyalan sabbin sojojin murna, inda ya roƙi sabbin dakarun da su ci gaba da zama masu kishin ƙasa da jajircewa wajen hidimta wa Najeriya.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: dakaru Tsaro Yayewa Zariya
এছাড়াও পড়ুন:
Taɓarɓarewar rashin tsaro ya nuna rashin shugabanci na gari — Obi
Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP, Peter Obi, ya ce taɓarɓarewar rashin tsaro a Najeriya na nuna gazawar shugabanci.
Ya yi kira da a gudanar da bincike mai zurfi cikin gaggawa kan zargin wasu jami’an gwamnati da taimaka wa ’yan ta’adda.
Buɗe cibiyar horas da sabbin sojoji a Kudu zai taimaka — Janar Shaibu Shirin kafa ‘Hisbar Ganduje’ ya tayar da ƙura a KanoObi, ya bayyana hakan ne bayan wani bidiyo da aka yaɗa a kafafen sada zumunta, inda wasu da ake zargin ’yan ta’adda ne suka ce jami’an gwamnati ne ke taimaka musu da makamai.
Ya ce wannan zargi abu ne mai matuƙar muhimmanci da bai kamata a yi watsi da shi ba.
“An ga wani bidiyo mai tayar da hankali a Jihar Kwara inda waɗanda aka kama suka ce jami’an gwamnati ne suka ba su harsasai da kayan aiki.
“Wannan zargi na buƙatar bincike cikin gaggawa kuma a bayyane.”
Obi ya ce duk da maƙudan kuɗaɗen da aka kashe a fannin tsaro tsawon shekaru, rashin tsaro na ƙara taɓarɓarewa a ƙasar.
“An kashe tiriliyoyin juɗi da biliyoyin daloli a fannin tsaro, amma duk da haka rashin tsaro na ƙara taɓarɓarewa a faɗin ƙasar nan.”
Ya kuma tambayi dalilin da ya sa ba a amfani da na’urorin zamani da fasahar tsaro wajen gano da kama ’yan ta’adda, duk da cewa ƙasar na da irin waɗannan damarmaki.
“Gwamnati na da iko da hanyoyin sadarwa, bayanan sirri da bin sahun kuɗaɗe, amma duk da haka satar mutane da ta’addanci na ci gaba da ƙaruwa.”
Obi ya kuma soki yadda ake murnar sakin waɗanda aka sace ba tare da kama waɗanda suka aikata laifin ba, inda ya ce hakan na nuna rashin ɗaukar al’amarin da muhimmanci.
A ƙarshe, ya yi gargaɗin cewa ƙaruwar rashin tsaro na nuni da gazawar gwamnati da kuma yin sakaci, inda ya jaddada cewa babban aikin kowace gwamnati ne kare rayuka da dukiyoyin al’umma.