Aminiya:
2025-12-12@06:47:40 GMT

Jam’iyyar PDP ta tabbatar da mutuwar mataimakin Gwamnan Bayelsa

Published: 12th, December 2025 GMT

Jam’iyyar PDP a ranar Alhamis ta tabbatar da mutuwar mataimakin gwamnan jihar Bayelsa, Sanata Lawrence Ewhrudjakpo.

Jam’iyyar ta tabbatar da rasuwar ce a cikin wata sanarwa da sakatarenta yada labaranta na kasa, Kwamared Ini Ememobong, ya fitar.

Rahotanni sun ce Ewhrudjakpo ya yanke jiki ya faɗi a ofishinsa da ke gidan gwamnati, Yenagoa, a ranar Alhamis, inda aka garzaya da shi zuwa Cibiyar Lafiya ta Ƙasa (FMC) da ke Yenagoa.

Lamarin ya faru ne a ranar Alhamis.

An haifi Ewhrudjakpo ranar ranar biyar ga watan Satumban 1965, a ƙauyen Ofoni da ke Ƙaramar Hukumar Sagbama, Jihar Bayelsa. Ya rasu yana da shekaru 60.

Kodayake ba a san ainihin dalilin faɗuwarsa ba, majiyoyi sun ce ya faɗi ne ba zato ba tsammani yayin da yake gudanar da ayyukan ofis, lamarin da ya sa dogarai da ma’aikatansa suka yi gaggawar taimaka masa.

Wasu majiyoyi da ke kusa da marigayin sun nuna cewa mutuwarsa na iya zama sakamakon bugun zuciya.

Lamarin ya haifar da ɗan tashin hankali a gidan gwamnati da kuma fadin Yenagoa, inda mazauna garin suka nuna damuwa game da mutumin da suke kira da “Mataimakin Gwamna Mai Aikin Dare.”

Sun ce sau da yawa yana yin aiki har dare ba tare da hutu ba.

A lokacin da ake rubuta wannan rahoto da yammacin jiya, gwamnatin Jihar Bayelsa ba ta fitar da wata sanarwa ba a hukumance a kan lamarin.

Kazalika, da mai taimaka wa mataimakin gwamnan kan yaɗa labarai, Doubra Atazi, da kuma Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar, Ebiuwou Koku-Obiyai, sun ƙi yin bayani lokacin da aka tuntube su.

Sai dai a cikin sanarwarta, PDP ta bayyana kaduwa da alhini kan rasuwar mataimakin gwamnan, tana bayyana shi a matsayin “amintaccen ɗan jam’iyya kuma mai gaskiya.”

Sanarwar ta ce: “Jam’iyyar PDP ta kadu matuƙa da labarin rasuwar Mataimakin Gwamnan Jihar Bayelsa kuma ɗan jam’iyya mai aminci, Mai Girma Sanata Lawrence Oborawharievwo Ewhrudjakpo, wanda rahotanni suka ce ya faɗi ya rasu a yau.

“Wannan labari mai tayar da hankali ya jefa Kwamitin Zartarwa na Ƙasa ƙarƙashin jagorancin Kabiru Tanimu Turaki, SAN, da kuma dukkan mambobin jam’iyyarmu mai girma, musamman mambobinmu masu aminci a Jihar Bayelsa, cikin baƙin ciki mai yawa.

“Tun yana raye, Sanata Ewhrudjakpo ya kasance ɗan siyasa mai gaskiya da daidaito wanda ya yi siyasa bisa ƙa’ida. Mutum ne da ya yi tsayin daka, jagora ne wanda rayuwarsa ta ta’allaka da imani, gaskiya da ƙarfin hali. Ya tsaya tsayin daka kan waɗannan dabi’u har zuwa ƙarshe.

“Muna cikin baƙin ciki matuƙa da rasuwar wannan jarumin siyasa mai gaskiya, kuma muna roƙon Allah ya ba shi hutu na har abada. Muna mika ta’aziyyarmu ga gwamnati da al’ummar jihar Bayelsa kan wannan babban rashin da ba za a iya maye gurbinsa ba.”

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Bayelsa mataimakin gwamna Jihar Bayelsa

এছাড়াও পড়ুন:

Najeriya za ta buga wasan sada zumunta da Masar kafin fara gasar AFCON ta 2025

Tawagar Super Eagles ta Najeriya za ta buga wasan sada zumunta da ƙasar Masar kafin fara gasar Kofin Afrika da za a yi a Maroko.

Wasan zai gudana ne a ranar 11 ga wata. Disamba, da misalin ƙarfe 7 na dare, a filin wasa na Cairo da ke Masar.

EFCC ta tsare Malami kan binciken kuɗaɗen Abacha Real Madrid  za ta ɓarje gumi da Manchester City a Santiago

Za a yi wasan ne kwana shida kafin a fara gasar da ƙasashe 24 za su fafata a cikinta.

Najeriya za ta fara wasanta na farko a ranar 23 ga watan Disamba da Tanzania.

Ita kuwa Masar za ta buga wasanta na farko da Zimbabwe a ranar 22 ga watan Disamba.

A tarihi, Masar ce tafi lashe Kofin Afrika inda ta lashe gasar sau bakwai, yayin da Najeriya ta lashe sau uku.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnonin Arewa Sun Yi Rawar Gani A Kafa Gidauniyar Fuskantar Matsalar Tsaro
  • Gwamnan Kano ya naɗa mace ta farko a matsayin shugabar Jami’ar Northwest
  • Ba ni da shirin ficewa daga PDP — Gwamnan Bauchi
  • Karamar Hukumar Agwara ta Jinjinawa Gwamnati Bisa Tabbatar da Tsaron Rayuka da Dukiyoyin Jama’a
  • Najeriya za ta buga wasan sada zumunta da Masar kafin fara gasar AFCON ta 2025
  • Sakkwatawa na murnar kisan da sojoji suka yi wa mataimakin Bello Turji
  • Uwargidan Gwamnan Jihar Zamfara Ta Taya Oluremi Tinubu Murnar Nadin Sarauta a Ile-Ife
  • Saurayi ya kashe budurwarsa sannan ya soya qwaqwalwarta 
  • Majalisar Dattawa ta amince Tinubu ya tura sojojin Najeriya zuwa Jamhuriyar Benin