Zaben 2027: NNPP Ta Sha Alwashin Maye Gurbin Tinubu da Radda
Published: 8th, December 2025 GMT
Daga Isma’il Adamu
Jam’iyyar NNPP ta bayyana cewa tana da kwarin gwiwar lashe karin mukaman siyasa a zaben shekarar 2027, ciki har da na shugaba kasa da gwamnan Jihar Katsina.
Sabon shugaban jam’iyyar da aka rantsar a Jihar Katsina, Alhaji Armaya’u AbdulKadir ne ya bayyana haka a zaben shugabannin jam’iyyar da aka gudanar a Katsina.
Ya ce jam’iyyar, wacce ta ba da muhimmanci ga ilimi, walwalar jama’a, karfafa matasa da ci gaban abubuwan more rayuwa, ta kara samun farin jini a wajen jama’a saboda ingantaccen jagoranci da wakilcin da take bayarwa ta hannun mambobinta da ke rike da mukamai a matakin kananan hukumomi, jihohi da tarayya.
“Masu zabe sun ga abin da jam’iyyarmu ke aiwatarwa. ‘Yan majalisa da sauran wadanda aka zaba suna aiki a matakai daban-daban tun daga kananan hukumomi har zuwa matakin tarayya. ‘Yan Najeriya sun shaida kwarjininmu, shi ya sa muke da tabbacin lashe karin kujeru a zaben 2027.
“Jagoranmu na kasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya kuduri aniyar karbar shugabancin kasa, yayin da a nan Jihar Katsina kuma muke shirin tsayar da kwararru masu kwarewa da kuzari da za su iya lashe kujerar Gwamna da sauran mukaman zabe.”
AbdulKadir, wanda ya jaddada cewa NNPP na kara samun karbuwa a tsakanin ‘yan Najeriya, ya ce hakan ya nuna a kwanan nan ta hanyar sauya sheka da wasu ‘yan wasu jam’iyyu suka yi zuwa NNPP. Ya kuma bukaci mambobin jam’iyyar da su kara samun magoya baya domin tunkarar zaben 2027.
Zaben shugabannin jihar, wanda ya samar da mambobi 38 ta hanyar maslaha, ya samu kulawar INEC da hukumomin tsaro, tare da halartar wakilan jam’iyyar daga kasa da yankin Arewa maso Yamma, da kuma daruruwan mambobin jam’iyyar.
Alhaji Armaya’u AbdulKadir ya kasance Shugaban jam’iyya, Sani Arga mataimaki na farko, Tijjani Zakari sakatare, Umar Musa sakataren shirya ayyuka, sannan Hauwa Abubakar ta zama shugabar mata.
Tunda farko, shugaban kwamitin gudanar da taron, Alhaji Muhammad Yusuf-Fagge, ya yaba wa wakilai da mambobin jam’iyyar a jihar bisa ladabi da natsuwar da suka nuna a yayin taron, da kuma yadda suka amince da hanyar maslaha wacce “ta sauƙaƙa aikin.”
Ya yi kira ga mambobin jam’iyyar a jihar da su ci gaba da kasancewa cikin hadin kai, biyayya da ladabi, tare da kara yawaita mambobi da samun goyon baya ga jam’iyyar a jihar.
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: mambobin jam iyyar jam iyyar da
এছাড়াও পড়ুন:
Fyaɗe ga ’yar shekara 12 ya ja wa matashi ɗaurin rai-da-rai a Yobe
Kotu ta yanke wa wani wanda ya yi wa wata yarinya ’yar shekara 12 fyaɗe hukuncin ɗaurin rai-da-rai a Ƙaramar Hukumar Guba ta Jihar Yobe.
Babbar Kotun Jihar Yobe da ke zaune a ƙaramar hukumar Gujba ta yanke wa mutumin mai shekaru 31 mai suna Ali Kwano.
An gurfanar da shi ne a kan zargin ya kai yarinyar cikin aji a ƙaramar makarantar sakandare ta je-ka-ka-dawo da ke garin Bumsa, inda ya yi lalata da ita da ƙarfi.
Ya yaudari yarinyar ce bayan ya gaya mata cewa ta jira shi a cikin aji bisa cewar zai sayi ƙosai.
Bayan da ta shiga ajin sai ya kama hannunta, ya rufe bakinta ya danne ta a ƙasa sannan ya yi lalata da ita da ƙarfi.
Ƙasashen waje na taimaka wa ’yan ta’adda a Najeriya —Sheikh Gumi ’Yan sanda sun kama tsohon shugaban PCACC, Muhuyi Rimin Gado a KanoAlƙaliyar da ke jagorantar shari’a, Mai Shari’a Amina Shehu, ta same shi da laifi, don haka ta yanke masa hukuncin ɗaurin rai-da-rai bisa ga sashe na 3 na dokar haramta cin zarafin mutane, ta Jihar Yobe ta Shekarar 2020.