Faransa ta tabbatar da sa hannunta wajen dakile juyin mulki a Benin
Published: 9th, December 2025 GMT
Faransa ta tabbatar da sa hannunta wajen dakile yunkurin juyin mulki a Jamhuriyar Benin.
Fadar gwammnatin faransa ta Élysée ta ce bisa bukatar hukumomin Benin ta bayar da “goyon baya ta fuskar bayar da bayanai da dabaru” ga sojojin Benin a matsayin martani ga yunkurin juyin mulki da aka dakile a karshen makon da ya gabata.
Sanarwar ta ce Emmanuel Macron ya yi hadin gwiwa” da “musayar bayanai da kasashen yankin,” in ji daya daga cikin masu ba shi shawara ga manema labarai, a cewar AFP.
Shugaban Faransa ya yi magana a ranar Lahadi da takwaransa na Benin, Patrice Talon, wanda sojoji suka nemi su hambarar, da kuma shugaban Najeriya da kuma kasar Saliyo.
Kasar Saliyo ce ke rike da shugabancin kungiyar ECOWAS, wacce ta dauki matakin soja don taimakawa Cotonou wajen dakile yunkurin juyin mulki.
Dama a jiya Shugaban Bola Tinubu ya tabbatar da cewa sojojin kasarsa sun taimaka wajen dakile juyin mulki a benin.
Wata sanarwa da Bayo Onanuga, mai magana da yawun shugaban ya fitar ta ambato Shugaba Tinubu yana cewa “sojojin sun mayar da martani wajen ceto dimokuraɗiyya ta 35.”
Sanarwar ta ce shugaba Tinubu ya dauki mataki bayan samun buƙatar neman ɗauki daga Benin.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka RSF : Rabin ‘Yan jarida 67 da aka kashe a bana, a Zirin Gaza ne December 9, 2025 An cire Tony Blair daga jerin wadanda zasu jagoranci Gaza December 9, 2025 Isra’ila ta sake kai hare-haren a kudancin Lebanon December 9, 2025 Trump Ya Yi Gefe Da Kasashen Turai Dangane Da Tattaunawa Kan Rikicin Ukraine December 9, 2025 Iran Ta Gudanar Da Taro Kan Yadda Manzon Allah (s) Ya Yi Mu’amala Da Wadanda Ba Musulmi Ba December 9, 2025 Najeriya : Matsala ce ta sa jirgin sojinmu yin saukar gaggawa A Burkina Faso December 9, 2025 Saudiya da Qatar Zasu Gina Layin Dogo Mai Sauri Tsakanin Kasashen Biyu December 9, 2025 Nigeria Ta Aike Da Jiragen Yaki Zuwa Kasar Benin Domin Dakile Yunkurin Juyin Mulki December 9, 2025 Pakistan ta Bai Wa Taliban Ta Aghanistan Zabi A Tsakanin Mu’amala Da Ita Ko Da ‘Yan Ta’adda December 9, 2025 Kasashen Iran Da Turkiya Za Su Bunkasa Alakarsu A Fagen Ilimi Da Musayar Fasaha December 9, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: wajen dakile
এছাড়াও পড়ুন:
Benin : Har yanzu Shugaba Patrice Talon ne a kan mulkin_fadar shugaban kasa
Rahotanni daga Jamhuriyar Benin na cewa am kama wasu 12 bayan yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba da jijjibin safiyar Lahadin nan.
Tun da farko dama fadar shugaban kasar ta ce har yanzu Shugaba Patrice Talon ne a kan mulkin.
Ministan harkokin cikin gida na Jamhuriyar Benin ya bayyana a gidan talabijin din kasar cewa yunkurin juyin mulkin da wasu tsirarun sojoji suka yi bai yi nasara ba.
Wani rukunin sojojin kasar ne karkashin Laftanar Kanar Pascal Tigri ya sanar da hambare Shugaba Patrice Talon tare da dakatar da tsarin mulki a kafar talabijin din.
Mr Talon, mai shekaru 67, ana sa ran zai mika mulki a watan Afrilu na shekara mai zuwa bayan shekaru 10 a kan mulki.
Tuni Ƙungiyar Tarayyar Afirka (AU) ta bayyana cewa “ta yi Allah wadai da yunkurin juyin mulkin da aka yi wa Shugaba Patrice Talon da karfi kuma ta yi kira ga sojoji da su koma sansaninsu.
Ita ma kungiyar ECOWAS ta bayyana matukar damuwa bayan samun rahotannin yunkurin juyin mulki a Jamhuriyar Benin.
A cikin wata sanarwa da ta fitar, kungiyar ta soki abin da ta kira “yunkurin da ya saba wa tsarin mulki” wanda ke nufin take wa jama’ar Benin muradunsu.
A cewar ECOWAS, duk wani yunƙurin karɓe mulki ta hanyar ƙarfi barazana ce kai tsaye ga mulkin dimokuraɗiyya da zaman lafiya a yankin.
Yunkurin juyin mulkin na Benin na zuwa ne bayan wanda ya wakana a kasashen Mali, Burkina Faso, Nijar, Guinea sai kwanan nan a Guinea-Bissau.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Dole ne Amurka ta amince da ‘yancin Iran na samar da makamashin nukiliya cikin lumana (Araghchi) December 7, 2025 Hamas : ‘’Babu batun kwance damarar makamai matuƙar Isra’ila ta ci gaba da mamaya’’ December 7, 2025 Iran : sabbin dabarun tsaron Amurka cimma maradun Isra’ila December 7, 2025 Masar : ba za mu bari a yi amfani da iyakar Rafah ba don korar Falasdinawa December 7, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan(a) 168 December 7, 2025 Kissoshin rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 167 December 7, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 166 December 7, 2025 Rwanda Da Amurka Sun Rattaba Hannu Kan Tallafin Dalar Amurka Miliyon $228 Na Kiwon Lafiya December 7, 2025 Amurka: Mun Yi Kokarin Kifar Da Gwamnatin JMI Har Sau Biyu Ba Tare Da Samun Nasara Ba December 7, 2025 Iran Ta Gargadi Kasashen Larabawa Dangane Da Tsibiran Kasar Guda Uku A cikin Tekun Farisa December 7, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci