Kotu ta sa ranar yanke hukunci a Shari’ar Abba Kyari da NDLEA
Published: 13th, December 2025 GMT
Babban Kotun Tarayya da ke Abuja ta sanya ranar 26 ga Fabrairu, 2026 domin yanke hukunci a shari’ar da Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA) ta shigar kan DCP Abba Kyari, wanda aka dakatar.
NDLEA na tuhumar Abba Kyari, tsohon Shugaban Rundunar ’Yan Sanda Masu Yaƙi da Garkuwa d a Mutane (IRT), tare da ’yan uwansa biyu kan zargin rashin bayyana kadarorinsu.
A ranar Juma’a Mai shari’a James Omotosho ya sanya ranar, bayan lauyoyin NDLEA, Sunday Joseph; lauyan Abba Kyari, Onyechi Ikpeazu, SAN; da lauyan ’yan uwansa, Monjok Agom, sun gabatar da hujjoji da muhawara kan tuhumar.
A cikin tuhumar da ta ƙunshi laifuffuka 23, NDLEA ta ce ta gano kadarori 14, ciki har da manyan shaguna, gidaje, filin wasan polo, filaye da gonaki mallakar Abba Kyari, a Babban Birnin Tarayya Abuja da Maiduguri a Jihar Borno.
Gwamnatin Kano ta haramta kafa hukumar Hisbah mai zaman kanta Matatar man Dangote ta rage farashin fetur zuwa N699NDLEA ta kara da cewa ta gano sama da Naira miliyan 207 miliyan da kuma Yuro 17,598 a asusun bankunan Abba Kyari daban-daban, ciki har da Guarantee Trust Bank, United Bank for Africa da Sterling Bank.
Hukumar ta kuma zargi waɗanda ake tuhuma su da ɓoye mallakar kadarori da kuma juya kuɗaɗen.
NDLEA ta ce yin hakan laifuffuka ne a ƙarƙashin Dokar NDLEA da kuma Dokar Hana Safarar Kuɗaɗe.
Sai dai wadanda ake tuhuma sun ce ba su amince da dukkan tuhumar ba.
NDLEA ta kira shaidu 10 domin tabbatar da tuhumar, tare da gabatar da aƙalla hujjoji 20.
Duk da haka, Abba Kyari, ya gabatar da buƙatar a watsar da shari’ar bayan masu gabatar da bayanansu.
Abba Kyari, ta bakin lauyansa, ya ce masu gabatar da ƙara sun kasa kawo hujja da ke nuna shi ne mai mallakar kadarorin da ake zargi.
Amma a ranar 28 ga Oktoba, Mai shari’a Omotosho ya yi watsi da bukatarsa, inda ya ce masu gabatar da kara sun kafa hujja ta farko da ke buƙatar wadanda ake tuhuma su kare kansu.
Kyari, ya dage cewa ya bayyana kadarorinsa da na matarsa bisa ƙa’ida, ya kuma musanta mallakar wasu kadarorin da NDLEA ta danganta masa, inda ya bayyana cewa wasu daga cikin kadarorin na mahaifinsa ne da ya rasu, wanda ya bar ’ya’ya kusan 30.
Ya kuma ƙaryata zargin mallakar filin wasan polo a Borno, inda ya ce abin mamaki ne a danganta masa wannan katafaren fili.
A ranar 26 ga Nuwamba, 2025, Abba Kyari ya rufe kare kansa bayan ya gabatar da hujjoji ta bakin lauyansa, kuma aka yi masa tambayoyi daga lauyan NDLEA.
Sai dai ‘yan uwansa biyu (Mohammed da Ali), ta bakin lauyansu Monjok Agom, sun shaida wa kotu cewa ba za su kira wani shaida ba, inda suka ce za su jingina shari’arsu da hujjojin masu gabatar da ƙara.
Wannan shari’ar ta daban ce da ta zargin safarar hodar iblis da yake fuskanta tare da wasu ‘yan sanda a gaban Mai shari’a Emeka Nwite na wata Babban Kotun Tarayya da ke Abuja.
Dukkan shari’o’in biyu, NDLEA ce ta shigar da su a shekarar 2022
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: ɓoye kadarori Kyari zargi masu gabatar da
এছাড়াও পড়ুন:
Zan yi amfani da Salah a wasan Liverpool da Brighton — Arn Slot
Mai horar da Ƙungiyyar Ƙwallon Ƙafa ta Liverpool, Arne Slot ya ce zai sanya Mohammed Salah cikin jerin ’yan wasan da za su bugawa Liverpool wasa da Brighton a ranar Asabar.
Slot wanda ya samu saɓani da Salah kan ajiye shi a benci a wasanni uku a jere, ya ce yana da yaƙinin cewa, Salah zai ci gaba da bugawa ƙungiyar wasa.
2027: Jam’iyyar NNPP ta rantsar da sabbin shugabanni a Gombe Osimhen ya lashe kyautar gwarzon ɗan wasan bana na TurkiyyaYa kuma ƙara da cewa, zai ci gaba da tattaunawa da ɗan wasan domin ya ci gaba da taka leda a Anfield.
Salah mai shekara 33, baya cikin jerin ‘yan wasan da suka doke Inter Milan a Italiya a ranar Talata, wanda hakan ke bayyana tsamin rashin jituwa tsakaninsa da Arne Slot.
Liverpool dai zata karɓi baƙuncin Brighton a wasan mako na 16 da ƙarfe 3 na ranar Asabar.
Mo Salah, ɗan asalin ƙasar Masar, ya bugawa Liverpool wasanni 420 tare da zura ƙwallaye 250 cikin zamansa a ƙungiyyar.
Ɗan wasan zai bar Liverpool domin dawowa ƙasar Masar a ranar 15 ga watan Disamba, kwanaki 6 gabanin fara kofin nahiyyar Afrika da ƙasar Morocco zata karɓi baƙunci.