Sakamkon Jin Ra’ayi: Yawancin Amurkawa suna adawa da yunkurin kai hari kan Venezuela
Published: 11th, December 2025 GMT
Galibin Amurkawa na adawa da yunkurin gwamnatin kasar na neman kai harin soji kan Venezuela da sunan murkushe safarar miyagun kwayoyi.
Ayyukan sojin Amurka a yankin ya zuwa yanzu sun sanadiyar mutuwar mutane 87, sanann kuma ana gudanar da su ne ba tare da izini daga alkali ko kotuko kuma majalisar dokoki ba.
Binciken ya nuna cewa kashi 48 cikin 100 na wadanda aka ji ra’ayoyinsu sun nuna adawa da da harin, yayin da kashi 34% ke nuna goyon bayansu, kuma kashi 18% ba su da ra’ayi.
Masu adawa da Shirin sun fi yawa a tsakanin ‘yan jam’iyyar Democrat, inda kashi 80% na ‘yan jami’iyar na adawa da wadanna ayyukan kashi 9% cikinsu ne kawai ke nuna goyon baya. A cikin ‘yan Republican, 67% sun goyi bayan harin, kuma 19% na adawa dashi.
Jin ra’ayin jama’ar na kwanaki shida, na zuwa ne a daidai lokacin da takun-saka ke kara ta’azzara tsakanin Washington da Caracas, kuma a daidai lokacin da shugaban Amurka Donald Trump ke la’akari da karin wasu hanyoyin soji da suka hada da kai hare-hare kan kasar, a daidai lokacin da Amurka ke zargin shugaban Venezuela Nicolas Maduro na da hannu a safarar miyagun kwayoyi. Maduro ya yi watsi da zargin baki daya, tare da bayyana shi a matsayin batu na siyasa zalla.
Hare-haren na baya-bayan nan da sojojin Amurka suka kai a kusa da Venezuela, wanda aka kaddamar a ranar 2 ga Satumba, 2025, karkashin Operation Southern Spear, ya haifar da cece-kuce bayan da aka kashe mutane 87 ba bisa ka’ida ba. Inda masana kan harkokin shari’a na kasa da kasa da kuma kungioyin kare hakkin bil adama suka bukaci da a gudanar da bincike kan lamarin.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Hamas Ta yi Tir Da Sabbin Matsugunan Yahudawa Da Isra’ila Ke yi A Yankunan Da Ta Mamaye December 10, 2025 Kasashen Nijeriya Da Saudiyya Sun Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar Tsaro Ta Shekaru 5 December 10, 2025 Shugaban Kasar Iran Yace Mata Su ne Ginshin Gina Makomakar Kowacce Kasa December 10, 2025 Iran Ta yi Tir Da Kisan Karen Dangin Isra’ila A Gaza A Ranar Yaki Da Kisan Kiyashi Ta MDD December 10, 2025 Borkina Faso Ta Saki Sojojin Sama Na Najeriya 11 Da ta Kama Bayan Jirginsu Yayi Saukar Gaggawa. December 10, 2025 Hamas Ta yi Tir Da Sabbin Matsugunan Yahudawa Da Isra’ila Ke yi A Yankunan Da Ta Mamaye December 10, 2025 Iran Tana Daukar Bakwancin Taron BRICS Na Binciken Kimiya Da Kuma Ci Gaban Ilmi December 10, 2025 Nasarar Da Iran Ta Samu A Yakin Kwanaki 12 Kan HKI Yana Jawo Hankalin Kasashen Duniya December 10, 2025 ‘Yan Ta’adda Sun Kai Hare-Hare Kan Sojojin Pakistan Sun Kuma Kashe 6 Daga Cikinsu December 10, 2025 Najeriya: Majalisar Dattawa Ta Bawa Tunubu Damar Kai Sojoji Zuwa Kasar Benin December 10, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: na adawa da
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Sha Alwashin Wadata Al’ummarsa da Tsaftataccen Ruwan Sha
Daga Usman Muhammad Zaria
Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu, Dr. Builder Muhammad Uba, ya umarci a gaggawata gyaran bututun da suka hada tashar tacewa da samar da ruwa yankunan Dutsawa da Kantudu.
Wannan mataki ya biyo bayan matsalolin da ake yawan fuskanta sakamakon lalacewar wutar lantarki da na’urar janareto, wanda ke hana jama’a samun ruwa yadda ya kamata.
Yayin da yake bayyana jimaminsa bisa wannan lamari, Dr. Muhammad Uba ya basu tabbacin cewa In Shaa Allahu matsalar ta zo karshe.
A cewarsa, majalisar ta kudirin aniyar yin duk mai yiwuwa domin magance matsalolin da ake fuskanta tare da tabbatar da samun isasshen tsaftataccen ruwan sha ga al’umma.
Ya yi alkawarin tura dukkan kayan aiki da ake bukata domin ganin an warware matsalar.
Dr. Muhammad Uba ya kuma bukaci ma’aikatan hukumar ruwa ta Birnin Kudu da su kara jajircewa wajen kula da tsarin domin kauce wa sake fuskantar irin wannan matsala a gaba.
“Ina karfafa gwiwar dukkan ma’aikatan hukumar ruwa da su kasance masu lura, su zama masu saurin daukar mataki, kuma su kawar da duk wani cikas da zai hana cimma burin samar da ruwa mai dorewa a ko’ina cikin Birnin Kudu.”
Shugaban ya bayyana cewa aikin da ake yi a babbar tashar tacewa da samar da ruwan sha ya kusa kammaluwa.
A cewarsa, wannan aikin tare da gyaran bututun da ake yi yanzu na daga cikin babban shirin gwamnatinsa na inganta samar da ruwa a fadin karamar hukumar.
Wasu daga cikin mutanen yankin sun ce wannan mataki ya nuna jajircewar Dr. Uba wajen inganta muhimman ababen more rayuwa da kuma kyautata jin dadin al’ummar Birnin Kudu.