Amurka ta matsa lamba a kan kotun ICC don janye bincike kan yakin Gaza da Afghanistan: Reuters
Published: 11th, December 2025 GMT
Gwamnatin shugaban Amurka Donald Trump ta bukaci kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa (ICC) ta yi gyara ga yarjejeniyar da aka kafa domin kare Trump da manyan jami’an Amurka daga duk wani bincike na yanzu ko nan gaba, in ji wani jami’in gwamnatin Trump a ranar Laraba. Barazanar dai na kunshe ne da gargadin kara sanya takunkumi idan kotun ta ki bin umarnin.
Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayar da rahoton cewa, wa’adin na Washington ya hada da karin wasu bukatu guda biyu: cewa kotun ta ICC ta janye bincikenta kan laifukan yaki da shugabannin Isra’ila suka aikata a lokacin yakin Gaza, da kuma cewa ta rufe binciken da ta yi tun farko kan halin sojan Amurka a Afghanistan. Idan kotu ta ki yin aiki, gwamnatin Amurka na iya sanya sabbin takunkumi kan daidaikun jami’an ICC.
Matsayin gwamnatin Trump na baya-bayan nan ya ginu ne kan takun saka a baya da hukumomin kasa da kasa. Kotun hukunta manyan laifuka ta ICC da ke birnin Hague, ta fuskanci matsin lamba daga Washington tun bayan da ta bude bincike kan ayyukan sojan Amurka a lokacin yakin Afghanistan da kuma a baya-bayan nan, kan matakin da “Isra’ila” ta dauka a zirin Gaza.
Jami’an Trump sun bayyana irin wannan binciken a matsayin na siyasa da kuma cin zarafi ga ikon kasa, kamar dai yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya rawaito.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Ghana ta yi Allah wadai da cin mutuncin ‘yan kasarta da ke balaguro a Isra’ila December 11, 2025 Sakamkon Jin Ra’ayi: Yawancin Amurkawa na adawa da kai hari kan Venezuela December 11, 2025 Hamas Ta yi Tir Da Sabbin Matsugunan Yahudawa Da Isra’ila Ke yi A Yankunan Da Ta Mamaye December 10, 2025 Kasashen Nijeriya Da Saudiyya Sun Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar Tsaro Ta Shekaru 5 December 10, 2025 Shugaban Kasar Iran Yace Mata Su ne Ginshin Gina Makomakar Kowacce Kasa December 10, 2025 Iran Ta yi Tir Da Kisan Karen Dangin Isra’ila A Gaza A Ranar Yaki Da Kisan Kiyashi Ta MDD December 10, 2025 Borkina Faso Ta Saki Sojojin Sama Na Najeriya 11 Da ta Kama Bayan Jirginsu Yayi Saukar Gaggawa. December 10, 2025 Hamas Ta yi Tir Da Sabbin Matsugunan Yahudawa Da Isra’ila Ke yi A Yankunan Da Ta Mamaye December 10, 2025 Iran Tana Daukar Bakwancin Taron BRICS Na Binciken Kimiya Da Kuma Ci Gaban Ilmi December 10, 2025 Nasarar Da Iran Ta Samu A Yakin Kwanaki 12 Kan HKI Yana Jawo Hankalin Kasashen Duniya December 10, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Rashin Tsaro: Gwamnatin Tarayya ta gaza — Kwankwaso
Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma dan takarar shugaban ƙasa na Jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce Gwamnatin Tarayya ta gaza wajen shawo kan matsalar tsaro da ke ƙara ta’azzara a faɗin kasar nan, lamarin da ya ce yana barazana ga haɗin kan ƙasa da zaman lafiya.
Kwankwaso, wanda ya taɓa zama Ministan Tsaro, ya bayyana a shafinsa na Facebook cewa yana da “damuwa ta musamman” kan yadda gwamnati ta kasa daƙile ayyukan ’yan ta’adda, ’yan bindiga, rikice-rikicen ƙabilanci da kuma yaɗuwar makamai ba tare da kulawa ba.
Ya ce abin da ya fi nuna gazawar gwamnati shi ne yadda aka bar jihohi su kafa ƙungiyoyin sa-kai ba tare da horo na musamman ba, abin da ya ƙara yaɗuwar kananan makamai a ƙasar.
“Abin takaici, Gwamnatin Tarayya ta gaza. Hakan ya bayyana a yadda ta amince da jihohi su kafa kungiyoyin sa-kai ba tare da horo na kwararru ba,” in ji shi.
An kama tsohon fursuna da bindiga ƙirar AK-47 Dalilin yawaitar juyin mulki a ƙasashen ECOWASKwankwaso ya gargadi cewa wasu ’yan siyasa suna amfani da wannan dama wajen kafa kungiyoyin su na musamman, abin da ya kara jefa kasar cikin hadari.
Ya kuma nuna damuwa kan yadda ake ƙara samun wariyar ƙabilanci da yankuna, inda ya ce ’yan Najeriya musamman daga wani yanki ke fuskantar tsangwama ba bisa ƙa’ida ba, tare da cin zarafi da azabtarwa a sassa daban-daban na kasar.
“Hakan ya kara muni da yadda ake samun cin zarafi, tsangwama da maganganun ƙiyayya a kafafen sada zumunta, wanda ake cusawa da kabilanci da addini. Wannan na barazana ga hadin kan ƙasa,” in ji shi.
Kwankwaso ya buƙaci gwamnati ta ɗauki mataki cikin gaggawa don dakatar da wannan hatsari kafin ya ƙara tsananta.
Ya ce a matsayinsa na tsohon Ministan Tsaro da kuma Shugaban Kwamitin Kula da Yaɗuwar Ƙananan Makamai, yana matuƙar damuwa da yadda makamai ke yaɗuwa cikin sauki a kasar.
Sai dai ya taya Janar Christopher Gwabin Musa murnar nada shi Ministan Tsaro, yana mai fatan zai yi nasara idan aka ba shi goyon bayan siyasa da ya dace.
“Ina da yaƙinin cewa idan aka ba shi goyon bayan siyasa da ya dace, yana da ƙwarewa da gogewa da za su taimaka wajen dawo da tsaro da zaman lafiya a kasar,” in ji Kwankwaso.