An Fara Gyaran Tashar Talabijin Ta Jigawa Don Kara Mata Nisan Zango
Published: 14th, December 2025 GMT
Gidan Talbijin na Jihar Jigawa wato JTV, ya fara gudanar da gyare-gyaren doguwar eriyar yada shirye-shiryen tashar dake garin Andaza.
Da yake yiwa shugaban gidan Talabijin na JTV Alhaji Abba Tukur karin bayani kan fara aikin, jagoran tawagar injiniyoyin, Injiniya Obi Onya, ya ce za su gudanar da aikin ta hanyar gano sassan doguwar eriyar da suke da matsala.
Injiniya Onya ya bayyana cewar, haka kuma za su gudanar da irin wannan aikin a kananan tashoshin yada shirye-shiryen tashar dake garuruwa 3 na kananan hukumomi a Jihar.
Yana mai cewar, garuruwan su ne Gumel da Hadejia da kuma Kazaure.
Shugaban gidan talabijin din wanda ya sami wakilcin Manajan Sashin injiniya na JTV, Malam Sha’aban Abubakar Tahir, ya yi bayani kan muhimmancin yi wa doguwar eriyar gyara, wanda ya ce zai karawa tashar nisan zango.
Usman Muhammad Zaria
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Jigawa
এছাড়াও পড়ুন:
Bankin Ajiya na Jihar Jigawa Ya Karamar Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu
Daga Usman Muhammad Zaria
Majalisar Karamar Hukumar Birnin Kudu ta bada tabbacin hada hannu da bankin ajiya na Savings and Loan na Jihar Jigawa domin habaka tattalin arziki.
Shugaban Karamar hukumar, Dr. Builder Muhammad Uba ya bada wannan tabbaci a lokacin da Manajan bankin, Babandi Isah Gumel ya kai masa ziyara.
Builder Muhammad Uba ya ce karamar hukumar za ta ci gaba da mu’amulla da bankin wajen ganin ma’aikatan wucin gadi na bude asusun ajiya a bankin.
Ya kuma bayyana farin cikinsa kan wannan ziyara da kuma karrama shi da aka yi.
A jawabinsa, Manajan bankin Savings and Loan na Jihar Jigawa, Babandi Isa Gumel, ya ce sun karrama shugaban Karamar hukumar ne bisa daukar ma’aikatan wucin gadi a karamar hukumar ta birnin kudu.
Yace Dr Muhammad Uba ya dauki ma’aikatan da dama a fannin kiwon lafiya da ilimi wato B-health da B-teach da kuma amincewa da yin mu’amulla da bankin.