Aminiya:
2025-12-11@19:34:50 GMT

Ɗaliban Jami’ar Unijos 8 sun mutu a hatsarin mota

Published: 11th, December 2025 GMT

Aƙalla ɗalibai takwas na Jami’ar Jos ne aka ruwaito sun mutu, yayin da wasu uku suka samu munanan raunuka, a wani mummunan hatsarin da ya rutsa da wata tirela da wata motar bas.

Hatsarin ya faru ne a hanyar Zariya, cikin ƙaramar hukumar Jos ta Arewa a Jihar Filato.

NAFDAC ta lalata kayayyakin Naira biliyan 5 a Jihar Nasarawa Zanga-zanga ta ɓarke bayan haɗarin tirela ta kashe mutum a Yobe

Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe biyu na tsakar daren ranar Alhamis lokacin da ɗaliban ke dawowa daga wani biki.

Jami’in kula da wayar da kan jama’a na hukumar kiyaye haɗɗura ta ƙasa (FRSC) Peter Yakubu Longsan ne ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa motar bas ɗin na ɗauke da ɗalibai 11 na Jami’ar.

A cewar Hukumar ta FRSC, shaidun gani da ido sun danganta hatsarin da tsananin gudu na direban motar yake yi na wuce gona da iri.

Da yake bayar da cikakken bayani kan lamarin, Longsan ya bayyana cewa, “A yau 11 ga Disamba, 2025, Hukumar FRSC reshen Jihar Filato ta samu kiran waya da misalin ƙarfe 02:30 na tsakar dare, inda aka ba da rahoton wani haɗarin mota da ya afku a kusa da hanyar Zariya wajen  Unity Bank, a Jos.

“Hatsarin ya haɗa da motoci biyu, tirela da bas, mutum 11 ne a cikin motar kuma an ce ɗaliban jami’ar Jos ne. Da faruwar lamarin ne mutum bakwai ake zargin nan take sun mutu, domin daga ƙarshe likita ya tabbatar da cewa sun mutu, sai kuma wani da ya mutu a asibitin wanda ya kawo adadin waɗanda suka mutu zuwa takwas.

“A yanzu haka wasu uku suna karɓar magani a asibitin, dukkan waɗanda abin ya rutsa da su maza ne, kamar yadda wani ganau ya shaida cewar motar bas ɗin na cikin tsananin gudu, lamarin da ya kai ga rasa natsuwa daga bisani kuma lamarin ya faru. A halin yanzu dai ana ci gaba da gudanar da cikakken bincike,” in ji shi.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Jami ar Jos

এছাড়াও পড়ুন:

An kama wani mutum a Abuja yana ƙoƙarin kai harsasai ga ’yan bindiga a Zamfara

Rundunar ’yan sandan yankin Babban Birnin Tarayya Abuja ta kama wani mutum mai suna Ahmed Abubakar mai shekara 32, bisa zargin ƙoƙarin kai harsasai 1,000 ga ’yan bindiga a Jihar Zamfara.

Kwamishinan ’yan sanda na birnin, Miller G. Dantawaye, ne ya bayyana hakan ga ’yan jarida a hedikwatar rundunar a Abuja ranar Laraba.

Sakkwatawa na murnar kisan da sojoji suka yi wa mataimakin Bello Turji Dalibin jami’a ya rasu a hatsarin motar murnar kammala jarabawa

Dantawaye ya ce an kama wanda ake zargin ne a ranar Litinin da misalin ƙarfe 3:30 na yamma, kuma tawagar musamman ta rundunar ce ta kama shi bayan samun sahihin bayanan sirri a Unguwar Dodo da ke ƙaramar hukumar Gwagwalada.

Ya ce binciken farko ya nuna cewa wanda ake zargin yana mu’amala da wani abokinsa da aka gano sunansa Yusuf Mohammed, inda aka gano cewa yana shirin sayo harsasai 1,000 domin kai wa ’yan bindiga da ke cikin daji a Zamfara.

“Bincikenmu ya ƙara nuna cewa wani ɗan uwansa, Ahmed Yakubu, ne ya turo shi kuma yanzu ya cika wandonsa da iska, domin ya sayo ya kuma kai wa ’yan ta’adda da ke aiki a yankin su na Zamfara,” in ji CP Dantawaye.

Ya ce wanda ake zargin yana hannun ’yan sanda a halin yanzu, yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin kama abokin aikin nasa da ya tsere.

Kwamishinan ya jaddada kudirin rundunar na kawar da masu aikata laifuka a Abuja da kewaye, tare da tabbatar da tsaron mazauna yankin.

Ya yi kira ga jama’a da su ci gaba da tallafa wa ’yan sanda ta hanyar bayar da rahoton duk wani abin da ake zargin laifi ta layukan gaggawa na rundunar.

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Zanga-zanga ta ɓarke bayan haɗarin tirela ta kashe mutum a Yobe
  • Gwamnan Kano ya naɗa mace ta farko a matsayin shugabar Jami’ar Northwest
  • Ba ni da shirin ficewa daga PDP — Gwamnan Bauchi
  • Kisan Zariya: Na bar Buhari da Allah — Sheikh El-Zakzaky
  • EFCC ta tsare Malami kan binciken kuɗaɗen Abacha
  • An kama wani mutum a Abuja yana ƙoƙarin kai harsasai ga ’yan bindiga a Zamfara
  • Dalibin jami’a ya rasu a hatsarin motar murnar kammala jarabawa
  • Kasar China Ta Zartar Da Hukuncin Kisa Akan Wani Babban Jami’in Banki
  • Kamfanin Mangal ya kori direba kan dauko yara 21 da aka kama a Kogi