Tinubu Ya Halarci Ɗaurin Auren Ɗan Yari, Ya Kai Ziyara Gidan Tsohon Shugaban Ƙasa Buhari
Published: 20th, September 2025 GMT
Daga nan ya wuce gidan tsohon shugaban ƙasa Marigayi Muhammadu Buhari domin yi wa matar sa Aisha da sauran ‘yan uwa ta’aziyya.
Ya bayyana Buhari a matsayin “shugaba mai kishin ƙasa da sadaukarwa, wanda gudunmawarsa ga haɗin kan Najeriya da ci gabanta ba za a manta da su ba,” inda ya tabbatar da ci gaba da goyon bayansa ga iyalan.
Cikin manyan baki da suka halarci taron har da Gwamna Nasir Idris na Jihar Kebbi; Gwamna Umar Bago na Jihar Neja; Gwamna Dikko Radda na Katsina; Gwamna AbdulRahman AbdulRazak na Kwara da Ministan Tsaro, Bello Matawalle.
Sauran sun haɗa da tsoffin gwamnoni Sule Lamido na Jigawa; Aliyu Wamakko na Sakkwato; Abdullahi Adamu Aliero na Kebbi; Ahmad Sani Yarima na Zamfara; Abdulfatai Ahmed na Kwara da Aminu Bello Masari na Jihar Katsina.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
2027: Ko Kano Ta Zauna Lafiya Ko Ta Hautsine, Sai Mun Sauke Gwamna Abba — Shugaban APC
Shugaban Jam’iyyar APC a Jihar Kano, Yarima Abdullahi Abbas, ya bayyana cewa, jam’iyyarsa za ta yi duk mai yiwuwa don tabbatar da cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jam’iyyar NNPP bai dawo kan mulki ba a babban zaben 2027. A cikin wani gajeren faifan bidiyo da ke yawo a Facebook, an ga Abbas yana jawabi ga magoya bayan APC a wani taro da ya yi da masu yada labaran jam’iyyar a karamar hukumar Gwale ta Jihar, inda ya yi wadannan kalamai. “Koma meye zai biyo baya, Abba ba zai koma kan kujerar gwamna ba. Ko Kano ta zauna lafiya ko ta hautsine, babu ruwanmu, amma dole ne Abba ya sauka a kujerar gwamnan Kano,” in ji Abbas ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Zargin Kisan Kiyashi Ga Kiristoci: Trump Bai San Ƙalubalen Tsaron Da Najeriya Ke Ciki Ba — Ndume November 4, 2025
Manyan Labarai Zulum Ya Raba Motocin Sintiri 63 Ga Hukumomin Tsaro A Borno November 4, 2025
Manyan Labarai China Ta Gargaɗi Amurka Kan Tsoma Baki A Harkokin Nijeriya November 4, 2025