Za A Yi Manyan Zabuka A Kasar Habasha A Watan Yuni Na 2026
Published: 12th, December 2025 GMT
Hukumar zaben kasar Habasha ta sanar da cewa za a yi manyan zabukan kasar a ranar 1 ga watan Yuni na 2026.
Shugabar hukumar zaben kasar ta Habasha Melatwork Hailu ta fada wa kafafen watsa labarun kasar cewa; Ana gudanar da ayyukan ne a yanzu domin tsara wuraren da za a yi zabukan da samar da rumfunan zabe a cikin rassan da za a kada kuri’a.
Har ila yau shugabar hukumar zaben kasar ta Habasha ta ce, jam’iyyun siyasar kasar sun sami horon da ya dace domin bayyana da tallata manufofinsu ga jama’ar kasar.
Sai dai yin zabe a kasar ta Habasha yana fuskantar kalubale mai yawa. Kasar dai ba ta dade da fitowa daga yakin basasa ba wanda aka yi a tsakanin gwamnatin tarayya da yankin Tigray da aka yi a tsakanin 2020 zuwa 2022.
Rikicin ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 600,000, kuma wasu da adadinsu ya kai miliyan 1 su ka bar gidajensu.
Kuma har yanzu ana fama da tashe-tashen hankula a cikin yankunan Oromia da Amhara.
A jawabin da ya gabatar a ranar 28 ga watan Oktoba, Fira ministan kasar ta Habasha Abiy Ahmed ya ce; Gwamnatin kasar tana da karfin da za ta iya gudanar da zabukan.”
Haka nan kuma ya ce, zaben da za a yi zai zama shi ne mafi tsaruwa a tarihin kasar.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Turkiya A Shirye Take Ta Aike Da Sojoji Zuwa Yankin Gaza December 12, 2025 Kremlin: Putin Ya Bayyana Wa Shugaba Maduro Na Venezuela Goyon Bayansa December 12, 2025 Ben Gafir Ya Sha Alwashin Rushe Kabarin Sheikh Izzuddin Alkassam December 12, 2025 Maduro: Amurka Ta Bude Sabon Salon Fashi Akan Doron Ruwa December 12, 2025 Ayatollah Khamenei : Iran na samun ci gaba duk da kalubale da dama December 11, 2025 Kyaftin Traoré : Yau Burkina ta zama misali a duniya December 11, 2025 Iran da Kazakhstan Sun rattaba hannu kan yarjeniyoyi da dama December 11, 2025 Hamas : Isra’ila ta gaza cika alkawarin da ta dauka kan yarjejeniyar tsagaita wuta December 11, 2025 Kasashen ECOWAS sun rage kudin sufirin jiragan sama a tsakaninsu December 11, 2025 Dakarun IRGC 3 Sun Yi Shahada A wani Harin Ta’addanci A Kudancin Kasar Iran December 11, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: kasar ta Habasha
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaban Kasar Iran Yace Mata Su ne Ginshin Gina Makomakar Kowacce Kasa
Shugaban kasar |iran Mas’ud pezeshkiyan da yake Magana a wajen taron ranar mata a kasar iran ya bayyana cewa maza ta da mata suna taka rawa iri daya wajen ciyar da alumma gaba, kan kyawawan ayyukan, kana ya jaddada cewa mata musamman iyaye suna taka muhimmiyar rawa wajen samar da matasa masu tasowa da kuma nusar da Alumma kyakkyawar makoma.
Kyawawan halayen musulunci wasu ginshi kai ne da suke daidaita maza da mata, saboda Al’qur’ani yayi alkawarin kyakkyawar rayuwa ga wadanda suka yi kyawawan ayyuka, da gaskiya ba tare da la’akari da jinsin su suba, haka zalika ya jaddada wannan ka’ida inda aka tsara mata ba a matsayin na biyu ba, amma a matsayin muhimmin abokan hulda wajen gina ci gaban rayuwar zamantakewa.
Pezeshkiyan yace maza da mata daya suke wajen aikata ayyukan kwaraai wanda dole ne ya hada da Imani da ayyukan kwarai acikin jama’a. kuma jaddada tasirin mata fiye da na maza musamman ta hanyar bada gudunmawa wajen renon iyalai da kuma tsara dabiu na managarta.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label Name* Email* Website Label Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran Ta yi Tir Da Kisan Karen Dangin Isra’ila A Gaza A Ranar Yaki Da Kisan Kiyashi Ta MDD December 10, 2025 Borkina Faso Ta Saki Sojojin Sama Na Najeriya 11 Da ta Kama Bayan Jirginsu Yayi Saukar Gaggawa. December 10, 2025 Hamas Ta yi Tir Da Sabbin Matsugunan Yahudawa Da Isra’ila Ke yi A Yankunan Da Ta Mamaye December 10, 2025 Iran Tana Daukar Bakwancin Taron BRICS Na Binciken Kimiya Da Kuma Ci Gaban Ilmi December 10, 2025 Nasarar Da Iran Ta Samu A Yakin Kwanaki 12 Kan HKI Yana Jawo Hankalin Kasashen Duniya December 10, 2025 ‘Yan Ta’adda Sun Kai Hare-Hare Kan Sojojin Pakistan Sun Kuma Kashe 6 Daga Cikinsu December 10, 2025 Najeriya: Majalisar Dattawa Ta Bawa Tunubu Damar Kai Sojoji Zuwa Kasar Benin December 10, 2025 Ministan Makamashi: Iran Tana Da Sanayya Ta Ilimi Na Samar Da Hadari Domin Yin Ruwan Sama December 10, 2025 Kasar China Ta Zartar Da Hukuncin Kisa Akan Wani Babban Jami’in Banki December 10, 2025 Ganawa A Tsakanin Mataimakan Ministocin Waje Na Kasashen Saudiyya, China Da Minista Arakci Na Iran December 10, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci