Xi Jinping Ya Mika Gaisuwar “Bikin Girbi Na Manoman Kasar Sin” Na Takwas
Published: 22nd, September 2025 GMT
Yayin da “bikin girbi na manoman kasar Sin” na takwas ke karatowa, babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin wato JKS, shugaban kasar, kuma shugaban kwamitin kolin soja Xi Jinping, a madadin kwamitin kolin JKS, ya mika gaisuwar bikin, da fatan alheri ga manoma da ma’aikatan dake gudanar da ayyukan da suka shafi harkokin noma, da kauyuka da kuma manoma a fadin kasar.
Xi Jinping ya yi nuni da cewa, a bana, mun shawo kan illar bala’o’i kamar fari, da ambaliyar ruwa, da samun daidaiton noman hatsin rani, da karuwar noman shinkafa mai nuna da wuri, ana kuma sa ran samun karin girbin hatsi.
Xi Jinping, ya jaddada cewa, zamanantarwa irin ta kasar Sin ba za a iya raba ta da zamanantar da aikin gona da kauyuka. Don haka dole ne kwamitocin JKS, da gwamnatoci na sassan kasar su aiwatar da shawarwari da tsare-tsare na kwamitin kolin JKS, da tsayawa tsayin daka wajen raya aikin gona da kauyuka, da kyautata manufofi don karfafawa, da amfana, da wadatar da manoma, da karfafa goyon bayan kayayyakin aikin gona na kimiyya da fasaha, da mayar da hankali kan inganta cikakken karfin samar da amfanin gona, da aiwatar da matakai da dama don inganta ayyukan yi, da kara samun kudin shiga na manoma, da kuma sa kaimi ga farfadowar kauyuka a dukkan fannoni. (Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: kwamitin kolin
এছাড়াও পড়ুন:
An gudanar da bikin ɗaga tutar Falasɗinu a Birtaniya
Tawagar jami’an diflomasiyyan Falasɗinu ta gudanar da bikin ɗaga tutar ƙasar a Litinin ɗin nan a birnin Landan kamar yadda kafar labarai ta DW ta ruwaito.
Bikin ɗaga tutar na zuwa ne kwana guda bayan da Birtaniya ta amince da Falasɗinu a matsayin kasa mai cin gashin kanta.
CAC ta soma yi wa kamfanoni rijista da fasahar AI Dalilin da muke goyon bayan Tinubu kan karɓo bashi — Majalisar WakilaiShugaban tawagar jami’an diflomasiyyan Falasdinawa a Burtaniya Husam Zomlot, ya daga wani allo mai ɗauke da rubutun ‘Ofishin jakadancin Falasɗinu’ sannan kuma ya ce nan ba da jimawa ba za a buɗe ofishin a hukumance bayan kammala wasu sharudda dangane da dokoki da kuma tsarin gudanarwa.
Mista Zomlot ya yi jinjina ta musamman ga matakin Burtaniya na amincewa da kasar Falasɗinu da aka daɗe ana jira.
Ya ƙara da cewa yin hakan zai kawo ƙarshen zalunci na dogon lokaci, a daidai gabar da Falasɗinawa ke fuskantar matsananciyar wahala.
Birtaniya wadda ta daɗe tana goyon bayan Isra’ila ta juya mata baya, sakamakon hare-haren da Isra’ilar take kai wa Zirin Gaza, wanda ya samo asali bayan da ƙungiyar Hamas ta kai wani mummunan hari a ranar 7 ga watan Oktoban 2023.
Tun a watan Yulin wannan shekarar Firaministan Birtaniya, Keir Starmer ya ce zai goyi kafa ƙasar Falasɗinu yana mai gindaya wa Isra’ilar sharaɗin yanke wannan shawarar.
A wancan lokacin Starmer ya ce zai amince da ƙasar Falasɗinu muddin Isra’ilar ba ta ɗauki wani ƙwaƙƙwaran mataki na cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da Hamas ba kafin babban taron Majalisar Dinkin Duniya na watan Satumba.
Sai dai a ranar Lahadi, Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu ya zargi ƙasashen da suka sanar da aniyar amincewa da ƙasar Falasɗinu a matsayin masu ƙarkafa wa ta’addanci gwiwa.
Haka kuma, Netanyahu ya sake nanata cewa muradin samar da ƙasar Falasɗinu ba zai taba cika ba, tare da yin barazanar faɗaɗa mamayar Gabar Yamma da Kogin Jordan.
A yayin da Birtaniya, Australia da kuma Canada suka bi sabun sauran ƙasashen duniya sama da 140 domin amincewa da Falasɗinu a matsayin ƙasa mai ’yanci, a nahiyar Afirka kuwa, yanzu haka ƙasashe 52 daga cikin 54 ne suka amince da wannan ’yanci.