Dalilin yawaitar juyin mulki a Afirka ta Yamma
Published: 8th, December 2025 GMT
Masana harkokin siyasa, jakadu da ƙungiyoyin fararen hula sun bayyana cewa rashin shugabanci nagari da son mulki na dogon lokaci su ne manyan dalilan da ke haddasa yawaitar juyin mulki a yankin Afirka ta Yamma.
Wannan na zuwa ne bayan yunƙurin juyin mulki da aka yi a Jamhuriyar Benin a ranar Lahadi, wanda ya jefa ƙasar cikin rudani.
Gwamnatin Benin ta ce ta shawo kan lamarin bayan wasu sojoji sun bayyana a talabijin na ƙasar cewa sun kifar da Shugaba Patrice Talon. Wannan na zuwa ne makonni kaɗan bayan juyin mulki a ƙasar Guinea-Bissau.
Majiyoyin tsaro sun tabbatar da kama sojoji kusan 12, ciki har da shugabannin yunƙurin da bai yi nasara ba. Talon, tsohon ɗan kasuwa mai shekaru 67, na shirin miƙa mulki a watan Afrilu mai zuwa bayan shekaru 10 a kan karagar mulki da ake ganin ya kawo ci gaban tattalin arziki da kuma ƙaruwar hare-haren masu iƙirarin jihadi.
Juyin mulki: An kama sojojin da suka yi yunƙurin kwace mulki a Benin Yadda muka daƙile yunƙurin juyin mulki a Benin — Sojin Saman NajeriyaSojojin da suka kira kansu Kwamitin Soja na Sake Tsarawa (CMR) sun bayyana a talabijin cewa sun yanke hukuncin cire Talon daga mulki.
Sai dai daga baya fadar shugaban ƙasa ta tabbatar da cewa Talon yana cikin koshin lafiya, ya ƙ bayyana masu yunƙurin a matsayin “ƙananan mutane da suka mamaye talabijin kawai.”
Ra’ayin masanaJakadan Najeriya a ƙasashen yankin, Ambasada Suleiman Ɗahiru, ya ce juyin mulki na yawaita ne saboda raunin dimokuradiyya da kuma rashin nagartar shugabanci.
“Dimokuradiyya ba ta kafa tushe yadda ya kamata a Afirka ta Yamma. Shugabanni da aka zaɓa ba sa tafiyar da ƙasashensu yadda ya dace, hakan ya haifar da ƙin yarda daga jama’a,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa zaɓe ya rasa amincewa a ƙasashe da dama, inda shugabanni ke ƙin sauka daga mulki. Ya kawo misali da Kamaru, inda shugaban ƙasa mai shekaru 92 ya ci zaɓe, da Gambiya, inda shugabanni ke nuna rashin niyyar sauka daga mulki.
Suleiman Ɗahiru ya ce sai shugabanni sun yi mulki da gaskiya da adalci, in ba haka ba, juyin mulki zai ci gaba da dawowa.
Ƙalubalen ECOWASTsohon jakadan Najeriya, M.K Ibrahim, ya bayyana cewa yawaitar juyin mulki babban koma baya ne ga yankin da kuma ƙungiyar ECOWAS.
Ya ce tun bayan kafa ECOWAS a 1975, an samu aƙalla juyin mulki 45 a yankin, sai dai tsakanin 2000 zuwa 2008 ne kawai aka samu zaman lafiya ba tare da juyin mulki ba.
Ibrahim ya ce yunƙurin da bai yi nasara ba a Benin ya sake bayyana raunin dimokuradiyya a yankin. Yanzu ƙasashe huɗu na ECOWAS ke ƙarƙashin mulkin soja, kuma idan Benin ta faɗi, da za a ce sun zama biyar.
Ya ce Najeriya na da nauyi na musamman wajen tabbatar da ci gaba da rayuwar ECOWAS, duk da matsalolinta na siyasa da tattalin arziki.
Ra’ayoyi kan matakan ECOWASIbrahim ya bayyana cewa akwai ra’ayoyi biyu a cikin ƙungiyar:
– Wasu na ganin dole a tsaya kan ka’idojin dimokuraɗiyyar da nagartar shugabanci, ko da hakan zai sa ƙasashe su fice daga ECOWAS.
– Wasu kuma na ganin ka’idojin sun yi tsauri, suna ba da shawarar tattaunawa maimakon fitar da ƙasa nan take.
Sai dai Ibrahim ya bayyana matsayinsa: “ECOWAS ba za ta ci gaba ba ta hanyar juyin mulki. Dimokuraɗiyya da nagartar shugabanci ne kawai za su tabbatar da haɗin kai da ci gaba.”
Dalilan yawaitar juyin mulkiYa ce raunin dimokuraɗiyyar, talauci, rashin tsaro da matsalolin Sahel na daga cikin manyan dalilan da ke sa jama’a su rungumi alkawarin sojoji duk da rashin tabbas.“Ba za a iya cewa akwai wata ƙasa a Afirka da ta tsallake barazanar juyin mulki ba,” in ji shi.
Daga: Sagir Kano Saleh, Joshua Odeyemi, Baba Martins, Dalhatu Liman (Abuja) & Salim Umar Ibrahim (Kano)
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: ECOWAS Najeriya yawaitar juyin mulki tabbatar da
এছাড়াও পড়ুন:
Afirka Ta Kudu: An Kashe Mutane 11 A Wani Bude Wuta Na Kan Mai Uwa Da Wabi
Rahotanni da suke fitowa daga birnin Pretoria sun ce, adadin mutanen da su ka kwanta dama sanadiyyar bude wuta ta kan mai uwa da wabi, sun kai 11 daga cikinsu har da karamin yaro dan shekaru uku.
Jami’an ‘yan sandan kasar ta Afirka Ta Kudu ne su ka sanar da cewa an bude wutar ne a cikin wani gidan shan barasa dake birnin Pretoria a jiya Asabar. Haka nan kuma sun sanar da kama wasu mutane uku da ake zargin suna da hannu a abinda ya faru.
Kananan yara uku ne dai kisan ya hada da su, biyu daga cikinsu shekarunsu uku-uku ne, sai daya mai shekaru 12. Kuma da akwai wata buduruwa ‘yar shekaru 16 da ita ma lamarin ya rutsa da ita.
Wani sashe na sanarwar ya ce da akwai wasu mutane 14 da su ka jikkata sanadiyyar bude wuta na daban da aka yi a garin Solsifl.
Kasar Afirka Ta Kudu dai tana fuskantar matsaloli irin wannan na bude wuta akan mutane.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Dubban Mutane Suna Guduwa Daga Gabashin DRC Saboda Barkewar Sabon Fada December 7, 2025 Mutane Biyar Ne Suka Mutu A Wata Musayar Wuta Tsakanin Sojojin Afghanistan Da Pakistan December 6, 2025 Iran Da Masar Sun yi Kira Da Kawo Karshen Keta Hurumin Gaza da Labanon da Isra’ila ke yi December 6, 2025 Qatar Tayi Gargardi Game Da Gakiyar Yarjejeniyar Gaza Matukar Isra’ila Bata Janye Ba December 6, 2025 Gwamnatin Najeriya Za ta Karbi Sabon Bashin Dala Miliyan 500 A Bankin Raya Kasashen Afrika December 6, 2025 Kungiyoyin Kare Hakkin Bil Adama Sun Yi Gargadi Game Da Yunkurin Isra’ila Na Kashe Barghusi December 6, 2025 Gasar FIFA: Iran Ta Fada Cikin Group Mai Sauki A Gasar Kwallon Kafa Ta FIFA 2026 December 6, 2025 Kasashen Musulmi 8 Sun Ki Amincewa Da Korar Falasdinawa Daga Gaza December 6, 2025 Sojojin Afganistan Da Pakistan Sun Yi Musayar Wuta A Tsakaninsu Duk Tare Da Tsagait Wuta December 6, 2025 Rasha Tace Ta Kakkabo Jiragen Drones Na Ukrai 116 A Daren Jiya December 6, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci