Farfesa Gumel Ya Zama Sabon Shugaban Jami’ar Tarayya Da Ke Dutse
Published: 14th, December 2025 GMT
Daga Usman Muhammad Zaria
Majalisar Gudanarwa ta huɗu ta Jami’ar Tarayya da ke Dutse (FUD) a Jihar Jigawa ta amince da naɗa Farfesa Ahmed Muhammed Gumel a matsayin shugabar jami’ar na huɗu.
Shugaban Majalisar Gudanarwar jami’ar, Farfesa Shuaibu Oba Abdulraheem, ya bayyana cewa an bi tsari mai tsauri da cikakken bincike wajen zaɓen sabon shugaban jami’ar.
A cewarsa, an tantance ’yan takara 2, inda a ƙarshe Farfesa Gumel ya fito a matsayin sabon Shugaban Jami’ar ta FUD.
Farfesa Uba ya taya sabon shugaban jami’ar murna, tare da yi masa fatan Allah Ya mishi jagora da nasara wajen sauke nauyin da aka dora masa.
A nasa jawabin, sabon Mataimakin Shugaban Jami’ar, Farfesa Ahmad Muhammad Gumel, ya gode wa Allah Madaukakin Sarki bisa zaɓensa a matsayin sabon shugaban jami’ar.
Ya kuma miƙa godiyarsa ga kwamitin haɗin gwiwar zaɓe, Shugaban Majalisar Gudanarwa, shugaban jami’ar mai ci, da dukkan mambobin majalisar jami’ar bisa amincewa da suka nuna masa.
Ya ƙara da cewa zai yi iya ƙoƙarinsa wajen ci gaba da gina nasarorin da shugaban jami’ar mai barin gadi ya samar.
Gidan Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa Farfesa Ahmad Mohammed Gumel tsohon ɗalibi ne na Jami’ar Malaya da ke ƙasar Malaysia, inda ya samu digiri na biyu (Master) a fannin Kimiyyar Halittu ta Biotechnology da kuma digiri na uku (Ph.D) a Industrial Biotechnology, tare da ƙwarewa a Biocatalysis da Bioprocess.
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Jigawa sabon Shugaban Jami ar sabon shugaban jami ar
এছাড়াও পড়ুন:
Samarwa Sojoji Manyan Makamai Ne Mafita – Shugaban Ƙaramar Hukumar Bukuyum
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Abubuwan Da Ba Ku Ji Ba Kan Rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi December 13, 2025
Labarai Haɗin Kan Musulmai Da Kirista A Nijeriya Zai Kawo Saukin Matsalar Tsaro — Shehu Sani December 13, 2025
Manyan Labarai Shugaba Tinubu Ya Karrama Shugaban NPA Da Lambar Yabo Ta Musamman December 13, 2025