Kungiyar AU Ta yi Tir Da Harin Da RSF Takai A Makarantar Kananan Yara Da Ya Kashe Mutane 80
Published: 8th, December 2025 GMT
Kungiyar Tarayyar Afrika ta AU ta yi tir da harin RSF kan wata makarantar kananan yara a kudancin Sudan da ya kashe dimbin fararen hula tare da jikkata da dama, mafi muni a baya-bayan nan da kungiyar ta kai a kokarin da ta ke yi na ci gaba da kwatar yankuna a sassan Kasar.
Akalla mutane 80 mafiyawancinsu kananan yara ne suka mutu a harin da mayakan RSF suka kai bayan da suka jefa bama-bamai kan wata makarantar kananan yara da ke garin Kalogi na yankin Kordafan a kudancin Sudan.
Rahotanni sun ce hare-hare 3 da RSF ta kai a yankin lokaci guda, inda a farko mayakan suka jefa bama-bamai a makarantar kananan yara gabanin kai hari wani asibiti kana daga bisani suka sake jefa wani bom kan wadanda ke kokarin kai dauki a makarantar kananan yaran.
Shgaban gwamnatin garin na Kalogi da harin ya faru Essam al-Din al-Sayed ya ce yanzu haka babu sadarwa a garin sai dai ta hanyar amfani da Starlink, kuma tsagin RSF da Abdelaziz al-Hilu ke jagoranta ne ke kaddamar da hare-haren kan mata da kananan yara a yankin.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka MِِِِDD: Kisan Kare Dangin Da Isra’ila Ta yi A Gaza Shi Ne Farko Da Yafi Jan Hankalin duniya December 8, 2025 Kasashen Iran Da Azarbaijan Sun Amince Da Ci Gaba Da Tuntubar Juna Domin Warware Duk Wani Rikici December 8, 2025 Iran Da Kasashen Afrika Sun Daura Dammarar Karfafa Alakar Kimiyya Tsakaninsu December 8, 2025 Ecowas Ta Tura Sojoji Zuwa Jamhuriyar Benin Don Dakile Juyin Mulki December 8, 2025 IRGC: Makaman Iran Sun Fada Kan Matatan Man Haifa Har Sau Biyu A Yakin Kwanaki 12 December 8, 2025 Najeriya: Gwamnatin Tarayya Ta Bada Sanarwan Kubutar Da Yan Makaranta 100 Da Aka Sace December 8, 2025 Iraki Ta Musanta Cewa Ta Tushe Asusun Hizbullah Da Ansarallah December 8, 2025 Sabon Fada Ya Barke A Tsakanin Thailand Da Cambodia December 8, 2025 Iran Ta Yi Allawadai Da Kisan Fararen Hula A Kasar Sudan December 8, 2025 Macron Na Faransa Ya Yi Wa Najeriya Alkawalin Taimakawa Akan Matsalolin Tsaro December 8, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: a makarantar kananan yara
এছাড়াও পড়ুন:
Sabon Fada Ya Barke A Tsakanin Thailand Da Cambodia
Sojojin kasar Thailand sun sanar a yau Litinin cewa, son kai wani sabon hari akan iyakar da take da sabani da makawabciyarta Cambodia.
Wannan sanarwar ta sojojin Thailand ya biyo bayan da kasashen biyu suka rika zargin juna da cewa sun keta dakatar da wutar yaki, da shugaban Amurka Donald Trump ya shiga tsakani.
Sojojin Thailand sun ce; sabon fadan da ya barke ya yi sanadiyyar mutuwar sojan kasar daya, yayinda wasu 4 su ka jikkata. Haka nan kuma sojojin na Thailand sun zargi takwarorinsu na Cambodiya da fara tsokana ta hanyar bude musu wuta.
A halin yanzu sojojin na Thailand sun fara amfani da jiragen sama na yaki wajen kai hare-hare.
Tun a ranar 5 ga watan Yuli ne dai fada ya barke a tsakanin kasashen biyu saboda sabanin kan iyaka. Wancan fadan dai ya yi sanadiyyar kashe mutane 48 da kuma tilasta wa mutane fiye da 300,000 yin hijira.
Kasashen biyu dai suna da sabani ne akan iyakarsu ta kasa da tsawonta ya kai kilo mita 817,wacce aka Shata tun wajen 1907 a lokacin da Faransa ta yi wa Cambodia Mulkin mallaka.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran Ta Yi Allawadai Da Kisan Fararen Hula A Kasar Sudan December 8, 2025 Macron Na Faransa Ya Yi Wa Najeriya Alkawalin Taimakawa Akan Matsalolin Tsaro December 8, 2025 Rasha Ta Yi Maraba Da Cire Sunanta A Matsayin ” Barazanar Da Amurka Teke Fuskanta December 8, 2025 Majid Majidi Na Iran Ya Sami Kyauyar Girmamawa Daga Cibiyar Fina-finai Na “Eurasia Dake Kasar Rasha December 8, 2025 Benin : Har yanzu Shugaba Patrice Talon ne a kan mulkin_fadar shugaban kasa December 7, 2025 Dole ne Amurka ta amince da ‘yancin Iran na samar da makamashin nukiliya cikin lumana (Araghchi) December 7, 2025 Hamas : ‘’Babu batun kwance damarar makamai matuƙar Isra’ila ta ci gaba da mamaya’’ December 7, 2025 Iran : sabbin dabarun tsaron Amurka cimma maradun Isra’ila December 7, 2025 Masar : ba za mu bari a yi amfani da iyakar Rafah ba don korar Falasdinawa December 7, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan(a) 168 December 7, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci