2025-12-12@15:48:04 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1500

«Labarin ya kara da cewa»:

    Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa (NLC) ta bayyana cewa za ta gudanar da zanga-zangar ƙasa baki ɗaya a ranar 17 ga Disamba, 2025, domin nuna damuwarta kan taɓarɓarewar tsaro a Nijeriya. Wannan sanarwa ta fito ne daga saƙon da NLC ta aikawa dukkanin majalisun jihohi a ranar 10 ga Disamba, bayan taron NEC da ta gudanar a ranar 4 ga watan. Kungiyar ta nuna baƙin ciki kan ƙaruwar hare-haren ƴan daba da satar mutane da ke ci gaba da addabar al’umma. NLC ta mayar da hankali musamman kan sace ɗalibai mata a wata makarantar kwana da ke Jihar Kebbi a ranar 17 ga Nuwamba, inda ta bayyana mamaki cewa an janye jami’an tsaro daga makarantar kafin harin. Ta ce wannan lamari...
      A Legas farashin shinkafa ya fadi sosai A kasuwannin Mushin da Daleko, farashin buhun shinkafa kilo 50 da ake sayar da shi a da Naira N75,000 cikin Nuwamba, a yanzu ya dawo Naira 54,000.   Jihar Delta A Jihar Delta, musamman a Asaba, farashin kayan abinci ya daidaita a manyan kasuwanni irin su Kasuwar Oko (Hausa), Midwifery Market da Ogbogonogo Market, sai dai a kasuwannin mako-mako na kauyuka. Bincike a babban birnin jihar ya nuna cewa farashin muhimman kayan abinci ya dan daidaita, amma ‘yan kasuwa da masu sayayya sun nuna damuwa kan karancin kudin da ake da shi don sayayya. Kwandon tumatir da ake sayarwa Naira 5,000 a wasu watanni da suka gabata, yanzu ya sakko Naira 4,000....
    Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya zargi ‘yan siyasan Nijeriya da zagon kasa ga ci gaban kasar ta hanyar daukar mukaman gwamnati a matsayin gadon gidansu a maimakon amanar jama’a. Da yake jawabi a ranar Laraba a yayin taro karo na 15 mai taken, “ya Isa haka” da ya gudana a jihar Legas, Sanusi II ya ce manyan ‘yan siyasa a fadin Nijeriya, suna ci gaba da yin zagon kasa ga ci gaban kasa saboda suna fifita kansu, iyalansu da abokan huldarsu fiye da kasar da ‘yan kasarta. Nazarin CGTN: Fahimtar Matsayin Sin Cikin Yanayin Tattalin Arzikin Duniya Na Da Muhimmanci Katsina Ta Amince Da Bayar Da Alawus Na Naira 30,000 Duk Wata Ga Malaman Karkara Ya yi...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A kwanakin baya, Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da sabon tsarin jadawalin karatu ga makarantun firamare da sakandare. Sabon tsarin, wanda Ma’aikatar Ilimi ta ƙasa ta tsara, yana da nufin inganta koyarwa da koyo, da rage nauyin lodi ga dalibai, da kuma tabbatar da cewa malamai suna da isasshen lokaci don isar da darussa tare da kwarewa. Tsarin ya mayar da hankali kan daidaita ranakun makaranta, da tsara lokutan darussa bisa bukatun shekaru da matakin karatu, da kuma kara aiki a kan basira, da kirkire-kirkire, da koyon sana’o’i, domin shirya dalibai su zama masu amfani a harkokin tattalin arziki tun daga matakin makaranta. NAJERIYA A YAU: Yadda Abincin Da Mutane Ke Ci Ke Zamewa...
    Daga Usman Muhammad Zaria Ma’aikatar mata da walwalar jama’a ta jihar Jigawa za ta kashe naira milyan dubu 10 da milyan 599 wajen gudanar da manyan ayyuka da harkokin yau da kullum a sabuwar shekara. Kwamishinar ma’aikatar, Hajiya Hadiza Abdulwahab, ta bayyana hakan lokacin kare kiyasin kasafin kudin ma’aikatar a gaban kwamatin harkokin mata na majalisar dokokin jihar Jigawa. A cewar ta, za su mayar da hankali wajen inganta shirye shiryen bunkasa rayuwar mata da al’amuran da su ka jibinci kananan yara domin bada kariya ga masu rauni a cikin al’umma. Hajiya Hadiza Abdulwahab ta ce ma’aikatar ta samu nasarori wajen aiwatar da tanade tanaden kasafin kudin 2025, yayin da za su ci gaba da daukar matakan da su...
    Shugaban mabiya Shi’a a Najeriya, Sheikh Ibraheem El-Zakzaky, ya ce zai yi hisabi da tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari, a gaban Allah kan abin da ya faru a Zariya a 2015. Rikicin ya fara ne bayan da mambobin IMN sun tare wa tsohon Hafsan Soji, Tukur Buratai, hanya. Najeriya za ta buga wasan sada zumunta da Masar kafin fara gasar AFCON ta 2025 Zanga-zanga ta ɓarke kan zargin sojoji da kashe mata a Adamawa Lamarin fara a matsayin ƙaramin rikici daga baya ya rikiɗe zuwa babban al’amari, lamarin da ya sanya sojoji buɗe wa mabiyan wuta. Ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan adam da kwamitin bincike na jihar, sun bayyana cewa an kashe tare binne ɗaruruwan mambobin IMN a asirce bayan faruwar...
    Daga Aliyu Lawal  Karamar Hukumar Agwara da ke Jihar Neja ta ce za ta ci gaba da hada kai da Gwamnatin Tarayya ta Jiha Neja wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’arta, musamman masu rauni. Shugaban Karamar Hukumar, Alhaji Iliyasu Zakari, ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya rattaba hannu da kansa, wadda ya rabawa manema labarai a Minna, babban birnin jihar Neja. Alhaji Iliyasu Zakari, wanda ya jaddada cewa kare rayuka da dukiyoyin jama’a shi ne ginshikin mulkinsa, ya kuma yaba wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu, Mai Ba Shugaban Kasa Shawara Kan Tsaro (NSA) Nuhu Ribadu, hukumomin tsaro da Gwamna Mohammed Umar Bago bisa rawar da suka taka wajen tabbatar da sakin dalibai ɗari da aka...
    Tawagar Super Eagles ta Najeriya za ta buga wasan sada zumunta da ƙasar Masar kafin fara gasar Kofin Afrika da za a yi a Maroko. Wasan zai gudana ne a ranar 11 ga wata. Disamba, da misalin ƙarfe 7 na dare, a filin wasa na Cairo da ke Masar. EFCC ta tsare Malami kan binciken kuɗaɗen Abacha Real Madrid  za ta ɓarje gumi da Manchester City a Santiago Za a yi wasan ne kwana shida kafin a fara gasar da ƙasashe 24 za su fafata a cikinta. Najeriya za ta fara wasanta na farko a ranar 23 ga watan Disamba da Tanzania. Ita kuwa Masar za ta buga wasanta na farko da Zimbabwe a ranar 22 ga watan Disamba. A...
    Rundunar ’yan sandan yankin Babban Birnin Tarayya Abuja ta kama wani mutum mai suna Ahmed Abubakar mai shekara 32, bisa zargin ƙoƙarin kai harsasai 1,000 ga ’yan bindiga a Jihar Zamfara. Kwamishinan ’yan sanda na birnin, Miller G. Dantawaye, ne ya bayyana hakan ga ’yan jarida a hedikwatar rundunar a Abuja ranar Laraba. Sakkwatawa na murnar kisan da sojoji suka yi wa mataimakin Bello Turji Dalibin jami’a ya rasu a hatsarin motar murnar kammala jarabawa Dantawaye ya ce an kama wanda ake zargin ne a ranar Litinin da misalin ƙarfe 3:30 na yamma, kuma tawagar musamman ta rundunar ce ta kama shi bayan samun sahihin bayanan sirri a Unguwar Dodo da ke ƙaramar hukumar Gwagwalada. Ya ce binciken farko ya...
    Wani dalibin shekarar ƙarshe a Jami’ar Ambrose Alli da ke jihar Edo, ya mutu a wani hatsarin mota bayan shi da wasu dalibai sun yi jerin gwanon motoci domin murnar kammala jarabawar ƙarshe. Aminiya ta samu labari a ranar Talata daga wani mai amfani da Facebook mai suna Inside Edo, cewa hatsarin ya faru ne a ranar Litinin jim kaɗan bayan daliban sun gama jarabawar ƙarshe. Sai dai ba a bayyana sunan dalibin ba. DAGA LARABA: Ko Ziyarar Tawagar Amurka Za Ta Kawo Karshen Matsalar Tsaro A Najeriya? Iya sojojin da ke tsaron Seyi Tinubu sun isa su samar da tsaro a Benin – Soyinka Majiyar ta ce motar ta yi ƙoƙarin wuce wata mota kafin ta kwace ta kuma...
    A yau ne dokar hana yara amfani da shafukan sada zumunta ta fara aiki a Ostiraliya. Firaministan ƙasar ya bayyana dokar a matsayin abin alfahari ga Ostiraliya, yana mai cewa za ta shiga tarihi a matsayin muhimmiyar sauyi. Anthony Albanese ya ce ƙasarsa na kan gaba a duniya wajen ɗaukar wannan mataki. Yara ƙasa da shekaru 16 sun tarar an rufe musu shafukansu a manyan dandanli 10 ciki har da TikTok da Snapchat. Sai dai ko a rana ta farko, rahotanni sun nuna cewa da dama daga cikinsu suna samun hanyoyin kaucewa wannan dokar. Kamfanin Meta, mammallakin Instagram da Facebook, ya ce dokar na tura yara zuwa wasu shafuka da ba su da tsauraran dokoki.
    Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bada sanarwan kubutar da yan makaranta 100 daga cikin wadanda ‘yan ta’adda suka sace a wata makaranta a jihar Naija a cikin watan Nuwamban da ya gabatata. Tashar talabijan ta almayadeen ta kasar Lebanon ta nakalto kamfanin dillancin labaran reuters na cewa jami’an tsaron kasar sun sami nasarar kubutar da yan makaranta har 100 daga cikin wadanda yan ta’adda suka sacesu a wata makarantar cocin Khatolica a cikin jihar Naija. Kafin haka an ce yara kimani 50 sun tsere daga hannun yan ta’addan bayan an sacesu. Tashar talabijin ta ‘Chennel TV ‘ ta bada labarin cewa sakin yan makarantan, amma bata nuna hotunansu ba kuma bata yi wani karin bayani ba. Sannan kungiyar kiristoci ta Najeriya...
    Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma dan takarar shugaban ƙasa na Jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce Gwamnatin Tarayya ta gaza wajen shawo kan matsalar tsaro da ke ƙara ta’azzara a faɗin kasar nan, lamarin da ya ce yana barazana ga haɗin kan ƙasa da zaman lafiya. Kwankwaso, wanda ya taɓa zama Ministan Tsaro, ya bayyana a shafinsa na Facebook cewa yana da “damuwa ta musamman” kan yadda gwamnati ta kasa daƙile ayyukan ’yan ta’adda, ’yan bindiga, rikice-rikicen ƙabilanci da kuma yaɗuwar makamai ba tare da kulawa ba. Ya ce abin da ya fi nuna gazawar gwamnati shi ne yadda aka bar jihohi su kafa ƙungiyoyin sa-kai ba tare da horo na musamman ba, abin da ya ƙara yaɗuwar...
    Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, ta tabbatar da rasuwar wasu mutum biyar sakamakon haɗura uku da suka auku a jihar. Kakakin hukumar, Saminu Yusif Abdullahi, ya ce hatsrin farko ya faru ne da safiyar ranar Alhamis a unguwar Badawa Layin Day by Day ca Ƙaramar Hukumar Nassarawa. Sojoji sun yi yunkurin juyin mulki a Jamhuriyar Benin Jirgin sojin sama ya yi hatsari a Neja Lamarin ya faru ne a wani gida mai faɗin kafa 25 da 20 wanda ya kama da wuta. Ma’aikatan kashe gobara sun ceto wata yarinya mai shekara 10 daga a cikin gidan, amma daga baya ta rasu a asibiti. An bai wa iyayenta gawarta. Hatsari na biyu ya faru ne a Ƙauyen Badume Kanawa da...
    Hukumar Kula da Rajistar Kamfanoni (CAC) ta ba wa  dukkan masu gudanar da harkar kuɗi ta PoS a fadin Najeriya, wa’adin ranar 1 ga Janairu, 2026, su yi cikakken rajista ko ta rufe su. A ranar Asabar, Hukumar ta sanar cewa yawaitar masu PoS marasa rajista a sassan ƙasar nan ya yawaita. Don haka ta jaddada cewa gudanar da PoS ba tare da rajista ba ya saɓa wa Dokar Kamfanoni ta 2020 da kuma ka’idojin Babban Bankin Najeriya (CBN). Hukumar ta kuma zargi wasu kamfanonin fasahar kudi (fintech) da daukar wakilai ba tare da rajista ba, tana bayyana wannan dabi’a a matsayin da sakaci kulawa da kuma barazana ga daidaiton tsarin kuɗi na ƙasar. Ta ce hakan na jefa miliyoyin ’yan...
    Kotu ta yanke wa wani wanda ya yi wa wata yarinya ’yar shekara 12 fyaɗe hukuncin ɗaurin rai-da-rai a Ƙaramar Hukumar Guba ta Jihar Yobe. Babbar Kotun Jihar Yobe da ke zaune a ƙaramar hukumar Gujba ta yanke wa mutumin mai shekaru 31 mai suna Ali Kwano. An gurfanar da shi ne a kan zargin ya kai yarinyar cikin aji a ƙaramar makarantar sakandare ta je-ka-ka-dawo da ke garin Bumsa, inda ya yi lalata da ita da ƙarfi. Ya yaudari yarinyar ce bayan ya gaya mata cewa ta jira shi a cikin aji bisa cewar zai sayi ƙosai. Bayan da ta shiga ajin sai ya kama hannunta, ya rufe bakinta ya danne ta a ƙasa sannan ya yi lalata da...
    Hukumar Tsaro ta DSS ta kama wani likita da ake zargin yana ba da magunguna tare da kula da ’yan bindiga masu garkuwa da mutane da ke wasu sassan jihar Kwara. An kama wanda ake zargin, wanda ba a iya gano sunansa ba a lokacin rahoton, a yankin Jebba bayan rahotannin sirri sun nuna cewa wasu masu safarar kaya suna kai magunguna daga Sakkwato domin kula da ’yan fashin daji da suka samu raunuka a dazukan jihar. Kakakin majalisar dokokin Ribas da takwarorinsa 16 sun fice daga PDP zuwa APC An kashe matashi yayin rikici a wajen raɗin suna a Bauchi Majiyoyin tsaro sun ce da dama daga cikin waɗannan ƙungiyoyin masu laifi sun samu raunukan harbin bindiga a fafatawar...
    Majalisar Dattawa ta amince da wani sabon ƙudiri da ke neman a gyara dokar yaƙi da ta’addanci, domin a ɗauki garkuwa da mutane a matsayin babban laifi na ta’addanci. Ƙudirin, wanda Sanata Opeyemi Bamidele ya gabatar, ya tanadi hukuncin kisa ga duk wanda aka kama da laifin satar mutane, ba tare da wata zaɓin tara ba. Tsaro: Gwamnatin Kano za ta fara amfani da jirage marasa matuƙa a iyakokinta Gobara ta ƙone kasuwar katako a Abuja Sanata Bamidele, ya ce ƙudirin ya yi daidai da yunƙurin gwamnati da majalisa na kawo ƙarshen matsalar tsaro a ƙasar nan. Yayin gabatar da ƙudirin, ya ce garkuwa da mutane na ƙara yawaita, kuma ƙungiyoyin miyagu na amfani da shi wajen tara k6udi, abin...
    Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya ce gwamnatinsa na shirin sayen jirage marasa matuƙa da wasu kayan aiki domin kare yankunan da ke iyakar Kano da Katsina. Kakakin gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ne, ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba. Gobara ta ƙone kasuwar katako a Abuja CBN ya kara yawan kudin da mutum zai iya cirewa a mako zuwa N500,000 Gwamna Abba, ya bayyana haka ne lokacin da ya ziyarci sansanin rundunar haɗin gwiwa ta JTF, domin ganin yadda suke shirin kare al’umma daga hare-haren ’yan bindiga a yankunan Tsanyawa da Shanono. Ya roƙi al’ummar yankunan da abin ya shafa da su riƙa bai wa jami’an tsaro bayanai masu amfani game da duk...
    Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa  ya yi watsi da barazanar Shugaban Amurka Donald Trump na cire Pretoria daga taron G20 na shekara mai zuwa, yana mai sake tabbatar da matsayin Afirka ta Kudu na memba da aka kafa wannan dandali na kasa da kasa tare da ita. Trump ya sanar a ranar Laraba da ta gabata cewa ba za a gayyaci Afirka ta Kudu zuwa taron G20 na 2026 a Florida ba, yana mai ambaton zargin da ake yi wa kasar na kin mika shugabancin G20 ga wakilin ofishin jakadancin Amurka a bikin rufe taron da aka yi a kasar  a baya. Duk da haka, Pretoria ta dage cewa shugabancin da ake yi nak aba-karba  an mika shi ga...
    ’Yan sanda sun gano tare da miƙa wa wata mata zinarenta da kuɗinsu ya kai Naira miliyan 23 da suna ɓace a lokacin wani harin Boko Haram shekara 13 da suka gabata a Jihar Borno. Jami’an tsaro da ke sintiri a kan iyakar Jihar Borno da Nijar ne suka gano kayan zinaren da suka ɓace tuna shakarar 2012, waɗanda suka haɗa da sarƙoƙi da sulallan zinariya a yankin Ƙaramar Hukumar Abadam. Jami’an Ƙaramar Hukumar ne suka sanar a ranar Asabar a Malam Fatori cewa tsabar zinaren da aka gano, darajarsu ta kai Naira miliyan 23, mallakin wata uwa ce mai ’ya’ya shida. Matar, wacce ke zaune a gaɓar Tafkin Chadi, ta ce, “A yau ina cike da farin ciki game...
    ’Yan sanda sun gano tare da miƙa wa wata mata zinarenta da kuɗinwu ta kai Naira miliyan 23 da suna ɓace a lokacin wani harin Boko Haram shekara 12 da suka gabata a Jihar Borno. Jami’an tsaro da ke sintiri a kan iyakar Jihar Borno da Nijar ne suka gano kayan zinaren waɗanda suka haɗa da sarƙoƙi da sulallan zinariya a yankin Ƙaramar Hukumar Abadam. Jami’an Ƙaramar Hukumar ne suka sanar a ranar Asabar a Malam Fatori cewa tsabar zinaren da aka gano, darajarsu ta kai Naira miliyan 23, mallakin wata uwa ce mai ’ya’ya shida. Matar, wacce ke zaune a gaɓar Tafkin Chadi, ta ce, “A yau ina cike da farin ciki game da gano tsabar zinare na masu...
    Daga Bello Wakili  Najeriya ta ƙarfafa ƙoƙarinta na kawar da cutar HIV nan da shekarar 2030, inda Uwargidar Shugaban Kasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta yi kira ga ’yan Najeriya, shugabanni da jami’an lafiya su haɗa hannu wajen cimma wannan manufa. Yayin jawabi a bikin ranar Yaki da Cutar AIDS ta Duniya ta 2025 da aka gudanar a Fadar Shugaban Ƙasa, Oluremi Tinubu ta jaddada cewa za a iya kawar da cutar HIV a Najeriya idan aka ci gaba da yin aiki cikin tsari, haɗin kai da kuma samun tallafi. Ta ce duk da cewa an samu cigaba a fannoni na rigakafi, magani da kulawa, ana buƙatar ci gaba da dagewa domin tabbatar da cewa kowane ɗan Najeriya na samun kariya....
    Ana ci gaba da ta ƙaddama kan Naira dubu ɗari bakwai da hamsin da Jami’ar Amurka ta Maryam Abacha  (MAAUN) da ke Jihar Kano ta wajabta wa ɗalibanta da suka kammala karatu biya a matsayin kuɗin bikin yaye ɗalibai. Jami’ar MAAUN ta sanya wa kowane ɗalibin da ya kammala karatu biyan Naira dubu ɗari bakwai da hamsin a matsayin kuɗin bikin yaye ɗalibai, kafin ta ba shi takardar shaidar kammala karatu da gabatar da bayanansa domin samun damar halartar aikin yi wa ƙasa hidima (NYSC). Sai dai kuma, Hukumar Karɓar Ƙorafi ta Jihar Kano (PCACC) ta umarci iyayen ɗaliban cewa su dakata da biyan kuɗin har sai ta kammala bincike kan ƙorafin da suka gabatar mata a kan lamarin. Sanarwar...
    Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa ya koma jam’iyyar ADC ne saboda ita kaɗai yake gani za ta iya ceto Najeriya daga matsalolin tsaro da na tattalin arziki da take fama da su. Yayin ƙaddamar da ofishin jam’iyyar a Jihar Taraba ranar Asabar, Atiku duk da a baya ya kasance a jam’iyyar APC da PDP, yanzu ya fahimci cewa ba za su kawo wa ƙasar nan mafita ta matsalolin da ake fuskanta. A makon da ya gabata ne Atiku ya karɓi katin zama mamba na ADC, abin da ya tabbatar da shigarsa jam’iyyar a hukumance. Ya yi kira ga jama’ar Taraba, musamman mata da matasa, su shiga ADC domin, a cewarsa, jam’iyyar za ta taimaka wajen inganta...
    Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya buƙaci Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, da ya daina siyasantar da harkar tsaro a jihar. Ya ce kamata ya yi gwamnan ya mayar da hankali kan matsalolin da ke damun jihar. Yadda ’yan mata ke kuɗancewa da kasuwancin fara a Kano DSS ta gayyaci Datti Baba-Ahmed kan zargin kalaman tayar da hankali Barau, ya yi wannan bayani ne bayan gwamnatin Kano ta zarge shi da yin magana inda ya nemi gwamnatin ta mayar da hankali kan tsaro. Ya ce matsalolin tsaro a ƙasar nan, ciki har da hare-haren ’yan bindiga a wasu yankunan Kano, suna buƙatar haɗin kai daga kowa. A cikin wata sanarwa daga mai taimaka masa, Ismail Mudashiru, ya...
    Iran da wasu kasashen yankin Tekun Fasha sun yi Allah wadai da sabon kutse da farmakin da sojojin Isra’ila suka kai ta kasa da kuma ta sama a birnin Beit Jinn da ke kudancin Siriya, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar akalla mutane 13, ciki har da yara. A cikin wata sanarwa, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Esmail Baghai ya jaddada ‘yancin da kasashen Yammacin Asiya ke da shi na kare ‘yancinsu da kuma ‘yancin yankinsu daga harin Isra’ila. Ya kuma soki rashin daukar matakin Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya kan take ‘yancin kai na kasashen yankin, musamman Siriya da Lebanon. A nata bangaren, Qatar ta yi gargadin cewa wannan “yana kara ta’azzara tashin hankali kuma yana kawo cikas ga...
    Rahotanni sun bayyana cewa kasashen larabawa na tekun fasha da kuma kasar Iran sun yi tir da hare-hare  ta kasa da sojojin isra’ila suka kai a wasu yankuna dake kudancin kasar Siriya kamar su bait jinn da ya kai ga mutuwar mutane 13 ciki har da yara kanana. A cikin bayani da ya fitar a jiya jumaa kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar iran Esmail Baghai ya jadda game da hakkin kasashe a yammacin asiya na kare martabar su da yankunansu game da wuce gona da irin Isra’ila. Har ila yau yayi suka game da kasa tabuka komai da kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya kan hare haren da isra’ila ke kai wa kan wasu kasashe kamar labanon da siriya wanda...
    Rahotanni sun bayyana cewa hukumar kwallon kafa ta kasar iran ta sanar cewa  za ta kauracewa taron da za’a yi  a makon gobe a birnin Washington bayan da kasar Amurka ta ki yarda ta bada shedar izinin shiga kasar ga wasu daga cikin wakilanta Kakakin hukumar kwallon kafa ta kasar iran yace mun riga mun sanarwa da hukumar kwallon kafa ta duniya fifa cewa wannan matakin ba shi da wata alaka da wasanni , kuma wakilan kasar iran din ba za su halarci gasar kofin duniya ba . Wannan yazo ne bayan da hukumar kwallon kafa ta kasar iran ta sanar cewa Amurka ta hana wasu daga cikin jami’anta visa shiga Amurka ciki har da shugaban hukumar Mahdi Taj, Ana...
    Hukumar ƙwallon ƙafa ta Afrika (CAF), ta sanar da cewa daga yanzu kowace ƙasa da za ta taka leda a Gasar Cin Kofin Afrika za ta je da ’yan wasa 28, maimakon 23 da ake amfani da su a baya. CAF, ta ce ta ɗauki wannan matakin ne domin rage matsalar samun raunin da ’yan wasa ke samu a lokacin gasar, tare da bai wa masu horaswa damar samun zaɓin ’yan wasa. Gwamnatin Kano ta nemi a binciki Ganduje kan zargin kalaman ta da hankali Yadda mutane suka yi cikar ƙwari don halartar jana’izar Sheikh Dahiru Bauchi Haka kuma, an amincewa kowace ƙasa za ta je gasar da mutum 17 daga cikin masu horaswa da likitoci. Hukumar ta bayyana cewa...
    Kasar Portugal ta kafa tarihi a birnin Doha na Qatar bayan da ta lashe Kofin Duniya na ’yan ƙasa da shekaru 17 (U-17) a karon farko, inda ta doke Austria da ci 1-0 a wasan ƙarshe. An jefa ƙwallon da ta bai wa Portugal nasara ne ta hannun Anisio Cabral, wanda ya ci a minti na 32 da fara buga wasan a filin wasa na Khalifa. Gwamnatin Kano ta nemi a binciki Ganduje kan zargin kalaman ta da hankali Yadda mutane suka yi cikar ƙwari don halartar jana’izar Sheikh Dahiru Bauchi A hanyarta ta kaiwa  wasan ƙarshen, Portugal ta doke Brazil a wasan kusa da na ƙarshe, yayin da Austria ta fitar da Italiya bayan lallasa ta da ci 2-0....
    Shugaban Amurka Donald Trump, ya bayyana cewa yana shirin daina karɓar mutane daga “ƙasashe masu tasowa” gaba ɗaya, ciki har da Afirka, Asiya da sauransu. Ya bayyana haka ne yayin wani taro da ya gudana a fadar shugaban Amurka. Ƙasar Japan ta fara sayar da i njin da ke yi wa mutane wanka A cewarsa, tsohon tsarin shige da fice na Amurka yana rage ƙarfin tsaron ƙasa kuma yana matsa wa makarantun gwamnati, asibitoci, da sauran hidimomin jama’a. Trump ya ce yawan baƙin haure a Amurka ya kai mutane miliyan 53, sannan ya yi zargin cewa mutane daga ƙasashen da ke fama da rikice-rikice, laifuka, da miyagun ƙungiyoyi suna ta zuwa ƙasar. Ya ce shigowar baƙi ya kawo rabuwar kawuna...
    Daga Usman Muhammad Zaria  Shugaban ƙaramar hukumar Birnin Kudu a Jihar Jigawa, Dr. Builder Muhammad Uba, ya aiwatar da wani aiki na da naira miliyan biyar domin tallafa wa aiwatar da Shirin Tallafawa Yara Mata  (AGILE) a yankin. Aikin ya hada da gyaran ajujuwa biyu da samar da muhimman kayan aiki, ciki har da injunan dinki, injin yin surfani wato (monogram) da shirin AGILE ya bayar kyauta wanda Dr. Uba ya shirya, ya taimaka wajen ganin an fara amfani da shi, tare da samar da janareta da tabarmi domin inganta koyarwa da horo. Wannan ci gaban ya biyo bayan wani bincike da tawagar AGILE ta jihar Jigawa ta gudanar a baya, inda ta bayyana cewa wuraren koyon sana’o’in na...
    Daga Salihu Tsibiri Tsohon shugaban masu rinjaye na Majalisar Wakilai, Alhassan Ado Doguwa, ya bayyana tabarbarewar tsaro da ake fuskanta, wato ta’addanci, garkuwa da mutane da kuma hare-haren ’yan bindiga, a matsayin barazana ga  siyasar ƙasar nan gabanin zaɓen 2027. Ya yi wannan tsokacin ne a jawabinsa yayin bude zaman taron musamman na yini biyu da Majalisar Wakilai ta shirya kan halin tsaro da ƙasar ke ciki. Alhassan Ado Doguwa, wanda ya yaba da ayyukan da hukumomin tsaro ke ci gaba da gudanarwa, ya ce halin da Arewa ke ciki abin takaici ne ƙwarai, la’akari da yawan mutanen da ke hannun masu garkuwa da kuma waɗanda ke rayuwa cikin tsananin rashin tabbas. Tsohon shugaban ya jaddada cewa duk da cewa...
    Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, a ranar Litinin ya ziyarci ɗaliban jihar da ke karatu a ƙasar Indiya, inda ya ba kowannen su tallafin Naira 500,000. Gwamnan, wanda ke ziyarar aiki a Indiya, ya fara ganawa da waɗanda suka ci gajiyar shirin tallafin karatu na jihar a Jami’ar Sharda da ke Noida. Ko sisi ba a biya ’yan bindiga ba kafin su saki ɗaliban da suka sace – Gwamnan Kebbi Kotu ta yanke wa mutum 5 hukuncin rataya a Oyo saboda aikata kisan kai Ya tabbatar musu da jajircewar gwamnatinsa wajen kula da walwalarsu domin samun nasarar karatunsu, sannan ya gargade su da su mai da hankali kan karatun nasu. Ya ce, “Na zo nan yau saboda dalili ɗaya,...
    An ceto ’yan matan nan 24 da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a Makarantar sakandaren Gwamnati ta GGCSS da ke yankin Maga da ke Jihar Kebbi. Gwamnan jihar Kebbi Nasiru Idiris a taron manema labarai a ranar Talata fadar gwamnatin jihar ya tabbatar da an karɓo ɗalibban da aka sace a farkon makon nan. Ya ce “an karɓo ɗiyanmu ’yan makaranta waɗanda aka yi garkuwa da su a Maga. Shugaban ƙasa ya baiwa jami’an tsaro umarni a tafi a gano inda yaran suke kuma a karɓo su muna tabbatar wa uwayen yara da al’ummar Kebbi yara sun dawo. “Muna godiya ga shugaban ƙasa da jami’an tsaro musamman sojoji da ’yan sanda da Sibil difens da sauransu da suka...
    Mahukunta a Jakarta, babban birnin Indonesia, sun haramta sayarwa da cin naman karnuka, kyanwa da jemagu, a wani yunƙuri na daƙile yaɗuwar cutar nan ta Mahaukacin Kare da a Turance ake kira rabies. Da yake jawabi a wannan Talatar, Gwamnan Jakarta, Pramono Anung, ya sanar da rattaba hannu kan dokar da ke hana duk wani nau’in kasuwanci ko mu’amala da waɗannan dabbobi a matsayin abinci. An sako ɗalibai 25 da ’yan bindiga suka sace a Kebbi Kano Pillars ta kawo ƙarshen wasanni 8 ba tare da nasara ba Dokar wadda za ta fara aiki bayan wa’adin watanni shida, ta ayyana cewa duk wanda ya karya ta zai iya fuskantar hukunci daga kan gargaɗi na rubuce har zuwa janye lasisin kasuwanci...
    Daga Musa kutama , kalaba Hasana Aminu matashiyar jaruma ce a Masana’antar Kannywood, wacce ta fito a finafina da dama ciki har da fim xin A Duniya da wasu fitattun finafunan Hausa. A zantawarta da Aminiya, Hasana Aminu wadda aka fi sani da suna Nabila ta ce, a halin yanzu tana tauna taura biyu ne a baka Ga yadda girar su ta kasan ce: Sunan Jarumar? Sunana Hasana Aminu, amma an fi sani na da suna Nabila a Masana’antar Kannywood da ke Kano Ta yaya kike gwama karatu da kuma kasuwanci da harkar fim? Eh, to farko ko da na shigo Masana’antar Kannywood sai na ga ai ashe ma ina da damar da zan iya yin karatu yayin da kuma...
    Jam’iyyar PDP ta yi soki matakin rufe makarantu da Gwamnatin Tarayya da wasu jihohi suka ɗauka sakamakon yawaitar sace-sacen dalibai, tana mai gargaɗin cewa hakan na iya taimaka wa ’yan ta’adda cimma burinsu. A taron manema labarai da aka gudanar a Abuja a ranar Lahadi, kakakin jam’iyyar, Ini Ememobong, ya ce, ya buƙaci Shugaba Tinubu da ya ajiye muƙaminsa idan ba zai iya kare rayuka da dukiyoyin ’yan Najeriya. “Muna sake tunatar da Shugaba Tinubu da gwamnatin APC cewa tsaron rayuka da dukiyoyi shi ne aikin farko na kowace gwamnati. Duk lokacin da gwamnati ta kasa yin wannan aiki, dole ta nemi taimako—na cikin gida ko na waje—ko kuma ta yi murabus idan tana da gaskiya da shugabanci,” in ji...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A shekarar 2014, bayan tashin hankalin da ya biyo bayan sace ɗaliban Chibok da kuma yawaitar hare-hare kan makarantun yankin Arewa maso Gabas, gwamnatin tarayya tare da haɗin gwiwar ƙasashen duniya ta ƙaddamar da wani muhimmin shiri mai suna Safe School Initiative.   Manufar wannan shiri ita ce tabbatar da cewa dalibai suna iya zuwa makaranta cikin tsaro ba tare da fargabar hare-hare daga ‘yan ta’adda ko ‘yan bindiga ba. NAJERIYA A YAU: Ba A Yi Ma Nnamdi Kanu Adalci Ba- Emmanuel Kanu DAGA LARABA: Hanyoyin Da Suka Kamata A Bi Wajen Ceto Daliban Kebbi Da Aka Sace Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne akan wannan shiri da...
    Mayaƙan ISWAP sun sace wasu ’yan mata a Ƙaramar Hukumar Askira-Uba a Jihar Borno. Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Borno, Abdullahi Askira, ya tabbatar da sace ’yan matan. Ɗalibai 50 da aka sace a Neja sun kuɓuta — CAN An rufe duk makarantu a Kebbi Ya ce an sace ’yan natan ne yayin da suke aiki a gonakinsu da ke yankin Mussa. A cewarsa, ’yan matan guda 13 masu shekaru tsakanin 15 zuwa 20 sun tafi gona domin girbe amfanin gonarsu, sai maharan suka yi awon gaba da su. Tun da farko an mayar da mutanen Huyim zuwa Mussa saboda matsalar rashin tsaro a garuruwansu. Sai dai ya ce ɗaya daga cikin ’yan matan da aka sace ta tsere kuma...
    Hukumar Raya Kogunan Hadejia da Jama’are (H-JRBDA) ta yi alƙawarin ɗaukar matakan gaggawa don magance matsalar ambaliyar ruwan da ke addabar al’ummar Ƙaramar Hukumar Jahun a Jihar Jigawa. Manajan Daraktan Hukumar, Injiniya Rabi’u Sulaiman Bichi, ya bayyana hakan bayan karɓar roƙon da jama’ar yankin suka miƙa ta hannun Shugaban Ƙaramar Hukumar, Jamilu Ɗan Malam Mai Rice, kan yawaitar ambaliya a yankin. Gwamnatin Yobe ta ba da umarnin rufe makarantun kwana a jihar Gwamnatin Tarayya ta musanta jita-jitar rufe dukkanin makarantu a faɗin Najeriya A cewar Injiniya Bichi, “Mun karɓi kokenku hannu biyu. Matakin da shugabancin Jahun ya ɗauka ya yi dai-dai. Za mu tura ƙwararrun injiniyoyi su yi aikin da ya kamata domin daƙile ambaliyar, tare da inganta noman yankin...
    Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta ƙaryata jita-jitar da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa za a rufe dukkanin makarantu a faɗin Najeriya daga ranar 24 ga watan Nuwamba, 2025. A cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Asabar, ma’aikatar ta ce labarin ƙarya ne, ba shi da tushe daga Gwamnatin Tarayya, Ma’aikatar Ilimi ko kuma wata hukuma ta tsaro. Obi ya yi watsi da hukuncin ɗaurin rai da rai da aka yi wa Kanu Mutane 315 ne suka ɓace bayan hari a makaranta Neja Mai magana da yawun ma’aikatar, Folasade Boriowo, ta shawarci jama’a da su yi watsi da duk wata sanarwa da ba ta fito daga hukumomin gwamnati ba. Ta ƙara da cewa jama’a su riƙa tantance gaskiyar...
    Shugaban Cocin Katolika reshen Kontagora, ƙarƙashin ya ce ɗalibai 88 da aka yi zaton sun tsere yayin harin da ’yan ta’adda suka kai a makarantar St Mary Secondary School da ke Papiri, ƙaramar hukumar Agwara ta Jihar Neja, har yanzu ba a san inda suke ba. A cewar majiyoyi, iyaye da dama sun garzaya makarantar domin kwashe ’ya’yansu bayan harin, amma ba ba su yaran ba. A baya  Aminiya ta ruwaito cewa ’yan bindiga sun kutsa cikin makarantar da daddare a ranar Juma’a, inda suka yi garkuwa da ɗalibai da ma’aikatan makarantar. Shugaban Cocin Katolika ta Kontagora, Mai Girma Bishop Bulus Dauwa Yohanna, ya sanar ta hannun mai taimaka masa, Daniel Atori, cewa an yi garkuwa da ɗalibai 303, malamai...
    Gwamnatin Tarayya ta bayar da umarnin rufe makarantun kwana 47 da ke faɗin Najeriya. Gwamnatin ta ɗauki wannan mataki ne bayan hare-haren da ’yan bindiga suka kai makarantu a jihohin Kebbi da Neja, inda suka sace ɗalibai da ma’aikata, suka kashe mutum ɗaya. Atiku ya nemi a ayyana dokar ta-ɓaci kan satar ɗalibai a Najeriya Gwamnonin Arewa sun yi Allah-wadai da sace ɗalibai a Neja A wata takarda da aka aike wa shugabannin makarantu a ranar Juma’a, Daraktar Makarantun Sakandare, Hajiya Binta Abdulkadir, ta ce Ministan Ilimi, Dokta Tunji Alausa, ya amince da rufe makarantun na wucin gadi saboda barazanar matsalolin tsaro. Takardar ta bayyana cewa an rufe makarantun ne domin kare ɗalibai da malamai daga hare-haren ’yan bindiga, da...
    Gwamna Nasir Idris na Jihar Kebbi, ya nemi ƙarin bayani kan dalilin ɗauke sojojin da ke gadin makarantar GGCSS Maga, gabanin harin da ’yan bindiga suka kai tare da sace ɗalibai 25. Gwamnan, ya ce gwamnati ta riga ta sanar da hukumomin tsaro game da yiwuwar kai hari, amma sojojin suka bar makarantar da misalin ƙarfe 3 na dare. Zargi: Majalisar Kano ta dawo da shugaban ƙaramar hukumar Rano kan kujerarsa Gwamnatin Neja ta zargi makarantar da aka sace wa dalibai da kin bin umarninta “An tura sojoji, amma sun bar makarantar da misalin ƙarfe 3 na dare, sannan ƙarfe 3:45 harin ya faru. Wa ya bayar da izinin su bar makarantar a wannan lokaci mai muhimmanci?” in ji Idris. Ya...
    Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya umarci Ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, da ya koma jihar Kebbi da aiki sakamakon sace ɗalibai ’yan mata 25 da wasu ’yan bindiga suka yi a jihar. Tinubu ya umurci Matawalle, wanda tsohon Gwamnan Jihar Zamfara ne, da ya zauna a Kebbi domin sa ido kan dukkan matakan tsaro da ake ɗauka domin kuɓutar da ɗaliban da aka sace. Babu wani addini da matsalar tsaron Nijeriya ta ƙyale — Fafaroma Za a aurar da marayu 200 a Zamfara ’Yan bindiga sun sace ɗalibai 25 a Makarantar Sakandiren Mata da ke garin Maga na Jihar Kebbi da misalin ƙarfe 4 na Asubahin ranar Litinin. A cewar mai magana da yawun fadar shugaban ƙasa, Bayo Onanuga wanda...
    Daga Bello Wakili Shugaba Bola Tinubu ya umurci Ministan  Tsaro, Alhaji Bello Matawalle, da ya koma Jihar Kebbi biyo bayan sace dalibai  ’yan mata 24  a jihar. An umurci Matawalle, wanda tsohon gwamnan Jihar Zamfara ne, da ya zauna a jihar domin sa ido kan ƙoƙarin  da ake yi na kubutar da ɗaliban da aka sace. ’Yan bindiga sun sace ɗalibai mata 24 na Makarantar Sakandare ta ’Yan Mata da ke garin Maga, Jihar Kebbi, da misalin  ƙarfe 4 na asubar ranar Litinin. Matawalle, wanda ake sa ran zai isa Birnin Kebbi a ranar Juma’a, ya samu ƙwarewa wajen fuskantar matsalar ’yan fashi da garkuwa da mutane a lokacin da yake gwamnan Jihar Zamfara daga shekarar 2019 zuwa 2023. Idan...
    Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnatin jihar Jigawa ta amince da fitar da Naira Biliyan 3 a matsayin  tallafin hadin gwiwa na kowace shekara  domin inganta ilimi a matakin farko, wato UBEC 2025 Matching Grant. A wata sanarwa da Kwamishinan  Yada Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu na Jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed, ya fitar ya bayyana cewa za a yi amfani da kudaden ne wajen gina sabbin azuzuwa, gyare-gyare, haka rijiyoyin burtsatse da kuma samar da kayan koyo da koyarwa ga dalibai da malamai. Ya ce, majalisar ta kuma amince da sama da Naira Miliyan 289 domin gina sabbin ofisoshin gudanarwa da gyare-gyare a kananan hukumomi 9 na jihar. A cewarsa, za a yi amfani da kudaden ne wajen gina ofisoshin...
    Iyalai da ‘yan uwan wadanda aka kashe a lokacin zanga-zangar da ta kawo karshen gwamnatin tsohuwar Firaminstar Bangaledash Sheikh Hasina a bara, sun yi maraba da hukuncin kisa da wata kotun birnin Dhaka ta yanke mata. An samu Sheikh Hasina da laifin cin zarafin bil adama tare da ba ‘yan sanda umurnin kashe masu zanga-zanga, inda aka yanke mata hukuncin a bayan idonta. Gwamnatin Bangaledash ta bukaci Indiya da ta tasa keyar Hasina da ke gudun hijira a can domin ta fuskanci hukuncin. Wakiliyar BBC ta ce  Hukumomin Indiya na cewa suna ci gaba da bibiyar lamarin tsakanin Sheikh Hasina da mahukuntan Bangaledash kuma hakan na nufin Indiya na neman wata hanyar diflomasiyya akan lamarin.   BBC
    Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta sami jagoran haramtacciyar ƙungiyar neman kafa kasar Biyafara ta IPOB, Nnamdi Kanu, da laifukan ta’addanci da aka zarge shi da aikatawa. Da yake yanke hukunci a ranar Alhamis, Mai Shari’a James Omotosho, ya amince da batutuwa uku da aka gabatar a shari’ar, inda ya yanke hukunci a kan su daga bangaren masu gabatar da ƙara. Gwamnatin Kwara ta rufe makarantu a kananan hukumomi 4 saboda matsalar tsaro Wayar wutar lantarki ta kashe mutum 4 a wajen cashiya a Legas Alkalin ya ce barazanar tashin hankali da Kanu ya yi a cikin jawabansa ta haifar da tsoro da damuwa a zukatan jama’a a yankin Kudu maso Gabas. Justice Omotosho ya ƙara da cewa bisa...
    Wata Kotun Tarayya da ke Abuja, ta sanya ranar 15 ga watan Janairun 2026, don fara shari’ar shugabannin ƙungiyar ’yan ta’adda ta Ansaru; Mahmud Usman da Abubakar Abba. Ana zargin su da jagorantar ƙungiyar ta’addanci ta Ansaru, kuma Hukumar DSS ce ta kama su tare da gurfanar da su a kotu. Ribadu ya jagoranci tawaga zuwa Amurka don ƙaryata zargin yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi Hakimi ya lashe kyautar gwarzon ɗan ƙwallon Afirka na bana An tsara faea sauraren shari’ar a ranar Laraba, amma aka ɗage bayan lauyoyin waɗanda ake tuhuma sun nemi a ƙara musu lokaci. Lauyansu, B.I. Bakum, ya bayyana cewa har yanzu suna jiran takardun zargi da wajen DSS. Haka kuma, ya nemi a mayar da...
    Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta yanke wa wani shugaban ISWAP Hussaini Ismaila, hukuncin ɗaurin shekaru 20 a gidan yari bayan samun sa da aikata laifukan ta’addanci. Alƙalin kotun, Mai Shari’a Emeka Nwite, ya yanke hukuncin ne bayan Ismaila, wanda ake kira Mai Tangaran, ya amsa tuhume-tuhume guda huɗu da Hukumar DSS ta gabatar a kansa. Gwamna Abba ya gabatar da N1.36trn a matsayin kasafin 2026 Tinubu ya fasa zuwa taron G20 saboda matsalar tsaro a Najeriya DSS ta ce Ismaila ne, ya jagoranci kai wasu hare-haren ta’addanci a Kano a shekarar 2012. Hare-haren sun haɗa da harin Hedikwatar ’Yan Sanda ta Bompai, Barikin ’Yan Sandan Mopol a titin Kabuga, ofishin ’yan sanda na Farm Centre, ofishin ’yan...
    Kasar Saudiyya ta sanar cewa za ta kara hannun jarinta a Amurka zuwa dala tiriliyan daya, daga dala biliyan 600 da kasar ta zuba a baya. Yariman Saudiyyar ne Mohammed Ben Salman ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai tare da Shugaban Amurka Donald Trump a ziyarar da ya kai fadar gwamnatin Amurka, bayan ganawar sirri da suka yi. A baya ne Trump ya bukaci Saudiyya da ta kara hannun jarinta a Amurka, sannan ya bukaci yariman ya tabbatar, inda shi kuma ya amsa da cewa, “tabbas.” Shugaban na Amurka ya ce Saudiyya za ta zama “babbar kawar kawance wacce ba daga NATO ba,” Ya kuma sanar da karfafa hadin gwiwar soja zuwa wani matsayi mafi...
    Gwamnan Taraba, Agbu Kefas ya sanar da dakatar da sauya sheƙa daga jam’iyyarsa ta PDP zuwa APC a dalilin sace ɗalibai mata ’yan sakandire da aka yi a Jihar Kebbi. Gwamnan ya ce zai ci gaba da tattaunawa da kuma nazari kan lokacin da ya fi dacewa ya sauya sheƙar tare da magoya bayansa. Mutane 7 sun mutu a hatsarin mota a Jigawa Gwamnonin Arewa sun yi Allah-wadai da sace ɗalibai mata a Kebbi Aminiya ta ruwaito cewa, da sanyin safiyar Litinin, 17 ga watan Nuwambar 2025, mahara suka shiga a makarantar sakandare ta ’yan mata da ke garin Maga a Jihar Kebbi, inda bayanai ke nuni da cewa sun yi awon gaba da ɗalibai 25 tare da halaka mataimakin...
    Ministan harkokin wajen Najeriya ya ce kasar ta soma tattaunawa da Amurka, bayan barazanar da Shugaba Trump ya yi na kai wa Najeriya harin soji kan kisan kiristoci da ya ce ana yi a kasar. A wata hira da kamfanin dillancin labarai na AFP, yayi da Yusuf Maitama Tuggar ya ce abin da suke tattaunawa a kai shi ne yadda za su hada kai wajen magance matsalolin tsaro don amfanin duniya. A farkon watan Nuwamban nan Trump ya ce ya bai wa ma’aikatar tsaron Amurka umurnin ta soma tsara yadda za ta kai hari Najeriyar. Sai dai ministan ya ce ba ya tunanin Amurka za ta yi hakan, ” muna ci gaba da tattaunawa, kuma ana samun ci gaba a...
    “Cikin hukuncin Allah, sojojin Daularmu sun kama ‘Kwamandan Runduna’… bayan ya gudu daga harin kwantan-ɓauna… Bayan mun yi masa tambayoyi, Mujahidai suka kashe shi.” An kuma wallafa wani hoto a kafafen sada zumunta da ya nuna Janar Uba a ɗaure. Har yanzu rundunar sojin Nijeriya ba ta fitar da wata sanarwa game da wannan lamari ba. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai ’Yansanda Sun Tura Tawaga Don Ceto Ɗaliban Da Aka Sace A Kebbi November 18, 2025 Manyan Labarai Bai Dace Adalci Ya Zama Na Sayarwa Ba – Tinubu Ga Alƙalai  November 17, 2025 Manyan Labarai Kakakin Majalisar Taraba Da Ƴan Majalisa 15 Sun Fice Daga PDP Zuwa APC November 17, 2025
    Gwamna Ahmed Idris na Jihar Kebbi ya ba da tabbacin cewa jami’an tsaro za su ƙwato ’yan matan da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a Kwalejin ’Yan Mata ta GGCSS Maga da ke Ƙaramar Hukumar Danko Wasu ta jihar cikin ƙoshin lafiya. Gwamnan ya bayar da tabbacin ne a yayin ganawarsa da iyayen ɗaliban kaɗan bayan harin ’yan bindigar a ranar Litinin. Aminiya ta ruwaito cewar da asubahin ranar ’yan bindiga suka kusta cikin harabar makarantar kwana ta ’yan mata ta GGCSS Maga, suka kwashe ɗalibai 25 daga ɗakin kwanansu zuwa cikin jeji. Maharan da suka riƙa harbi a iska kafin su shiga harabar makarantar sun bindige Matakin Shugaban Makarantar, Malam Hassan Yakubu Makuku, wanda ya yi ƙoƙarin...
    Ƙungiyar kare haƙƙin bil’adama ta Amnesty International ta yi kakkausar suka kan sabon harin da ’yan bindiga suka kai makarantar sakandare ta ’yan mata da ke garin Maga a Jihar Kebbi, wanda ya kai ga sace ɗalibai mata sama da 25 tare da halaka mai gadi da mataimakin shugaban makarantar. A wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin, Amnesty ta bayyana lamarin a matsayin abin takaici da kuma nuna gazawar gwamnatin Shugaba Bola Tinubu wajen kare rayuka da dukiyoyin ’yan kasa ballantana kawo ƙarshen ta’addancin ’yan bindiga. CAF ta fitar da ’yan wasa uku da suka rage a takarar gwarzon Afirka na bana Gobara ta laƙume rayukan yara biyu ’yan gida ɗaya a Ribas Ƙungiyar ta ce bincikenta ya gano...
    Gobara ta laƙume rayukan wasu yara biyu ’yan gida ɗaya a unguwar Rumuola da ke ƙaramar hukumar Obio/Akpor a Jihar Ribas. Bayanai sun ce ibtila’in ya auku ne da misalin ƙarfe 10 na dare a ranar Lahadi, lokacin da gobarar ta tashi a ɗaya daga cikin wasu ɗakunan haya da mahaifiyar yaran ta kulle ’ya’yanta huɗu ta tafi sayen kayan girki. Mayaƙan ISWAP sun kashe kwamandan soji a Borno ’Yan sanda sun kama ƙunshi 66 na Tabar Wiwi a Gombe A cewar mazauna yankin, cikin yaran huɗun, biyun da suka riga suka kwanta barci sun ƙone su kurmus, yayin da sauran biyun da ke farke suka samu damar tserewa. Aminiya ta ruwaito cewa, mazauna yankin da sun ankara da gobarar...
      Ya kuma yi Allah wadai da kisan wani jigo na Jam’iyyar APC, Umar Moriki, da kuma sace-sacen jama’a da aka yi a Karamar Hukumar Tsafe ta Jihar Zamfara, inda aka sace iyalai baki daya, ciki har da mata da yara. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai MACBAN Ta Nemi Amurka Ta Cire Sunanta Daga Jerin Waɗanda Ta Ƙaƙabawa Takunkumi November 17, 2025 Manyan Labarai Bai Dace Adalci Ya Zama Na Sayarwa Ba – Tinubu Ga Alƙalai  November 17, 2025 Manyan Labarai Kakakin Majalisar Taraba Da Ƴan Majalisa 15 Sun Fice Daga PDP Zuwa APC November 17, 2025
    Hukumar ƙididdiga ta Najeriya (NBS) ta ce hauhawar farashin kayyayaki a ƙasar ya ragu zuwa kashi 16.05 cikin 100 a watan Oktoban 2025. Cikin rahoton wata wata da hukumar ke fitarwa, ta ce hauhawar farashin ya ragu ne da kashi 1.97 idan aka kwatanta da kashi 18.02 da aka samu a watan Satumba. ’Yan Majalisar Dokokin Taraba 16 sun sauya sheka daga PDP zuwa APC An ɗaura auren Sanata Kawu Sumaila da wata jami’ar soji a Kano A watanin baya-bayan an riƙa samun raguwar hauhawar farashin kayyaki a ƙasar. Aminiya ta ruwaito cewa, tun dai daga watan Yunin bana, hauhawar farashin kayayyaki ke ci gaba da sauka a ƙasar har kawo yanzu. Ana iya tuna cewa, tun watanni kadan da...
    Bonzena ya ƙara da cewa duk da cewa kafin yanzu APC ce ke da rashin rinjaye a majalisar, an ci gaba da aiki cikin zaman lafiya, amma yanzu yana farin cikin ganin cewa dukkan mambobin majalisar sun haɗe ƙarƙashin tsari daya da ya yi daidai da hangen shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Ƴan Bindiga Sun Sace Ɗalibai Ƴan Mata, Sun Kashe Mataimakin Shugaban Makaranta A Kebbi November 17, 2025 Manyan Labarai Mutane 42 Sun Mutu A Wani Hatsarin Tankar Dizal Da Motar Masu Umrah A Hanyar Makka November 17, 2025 Manyan Labarai Ba Mu Samu Labarin Kai Wa Laftanar Yerima Hari Ba – Ƴansanda November 17, 2025
    Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Taraba, Rt Hon. Kizito Bonzena, tare da ’yan majalisar 15 sun sauya sheka daga jam’iyyarsu ta PDP zuwa APC. A saifyar Litinin ne Rt Hon. Kizito Bonzena ya gabatar da takardarsa ta ficewa daga PDP tare da sauran mambobin zuwa APC. Ya bayyana cewa da sauyin shekar tasu, yanzu APC ce ke da daukacin kujeru 24 da ke Majalisar Dokokin Jihar Taraba. Hakan na zuwa ne jim kadan bayan Gwamnan Jihar Taraba, Kefas ya sanar da shirinsa na komawa APC daga PDP. Masu ibadar Umarah 42 sun mutu a hatsarin mota a hanyar zuwa Makka ’Yan ta’adda sun sace dalibai 25 a dakunan kwanansu a Kebbi Sauran mambobin majalisar da suka sauya sheka sun hada da...
    Wasu masu ibadar Umara 42 sun mutu bayan da motarsu ta yi taho-mu-gama da wata tankar mai a kusa da birnin Madina da ke kasar Saudiyya. Dukkan masu ibadar ’yan kasar Indiya ne, kuma hatsarin ya ritsa da su ne a kan hanyarsu ta zuwa Makka bayan kammala ziyara a birnin Madina. Ministan harkokin wajen Indiya Dakta S. Jaishankar ya bayyana cewa mutum daya daga cikin fasinjojin ya tsallake rijiya da baya a hatsarin da ya auku da tsakar daren Litinin. Hatsarin ya auku ne a bayan da motar safa mai daukar mutum 43 da masu ibadar suke ciki ta yi karo gaba-da-gaba da wata tankar mai. ’Yan ta’adda sun sace dalibai 25 a dakunan kwanansu a Kebbi NELFUND ya...
    Rundunar Ƴansandan birnin tarayya ta bayyana cewa babu wani rahoto ko bayanin da ta samu game da yunkurin kashe laftanar Ahmed Yerima, jami’in Sojin ruwa da ya yi taƙaddama da Ministan Abuja, Nyesom Wike, kan wani fili da ake jayayya kansa a Abuja kwanakin baya. Jami’ar hulɗa da jama’a ta rundunar, SP Josephine Adeh, ta fitar da sanarwar ne a ranar Litinin tana mai ƙaryata labarin da ya yaɗu a kafafen sada zumunta. Adeh ta ce babu wani lamari da ya faru ko aka rubuta a koda ɗaya daga cikin wata ƙaramar hukumar da ke cikin birnin, don haka ta buƙaci jama’a da su yi watsi da labarin saboda ba shi da tushe. Ta ƙara da cewa irin waɗannan labaran...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Laftanal Yarima Ya Tsallake Rijiya Da Baya A Abuja November 16, 2025 Manyan Labarai Falana Ya Shawarci Waɗanda Suka Biya Kuɗin Fansa Su Kai Gwamnati Kotu Don Ta Biya Su November 16, 2025 Manyan Labarai Ƴan Bindiga Sun Sace Mutane 14 A Wani Sabon Hari A Zamfara November 16, 2025
    Gwamnan Jihar Taraba, Agbu Kefas, ya ce zai fice daga jam’iyyar PDP tare da sauya sheƙa zuwa APC a hukumance a ranar Laraba, 19 ga watan Nuwamba. Ya bayyana haka ne yayin da yake duba aikin gyaran Filin Wasanni na Jolly Nyame da ke Jalingo a ƙarshen mako. Ba da yawuna PDP ta kori Wike ba — Muftwang Tsohon Minista Kabiru Turaki ya zama sabon shugaban PDP na ƙasa Yayin da yake magana da ’yan jarida, Gwamna Kefas, ya ce ya yanke shawarar ficewa daga PDP ne saboda nemo hanyar da zai amfanar da al’ummar Taraba. Ya ce: “Zan sauya sheƙa a hukumance daga PDP zuwa APC a ranar 19 ga watan Nuwamba. Wannan sauyi zai amfanar da al’ummar Taraba.”...
    Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri na Jihar Adamawa, ya yi watsi da hukuncin da Jam’iyyar PDP ta yanke na korar Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, daga jam’iyyar. Aminiya ta ruwaito yadda PDP ta kori Wike, Sanata Samuel Anyanwu da tsohon Gwamnan Ekiti, Ayodele Fayose, a yayin babban taron PDP da aka gudanar a Ibadan, Jihar Oyo. Cif Olabode George ne, ya gabatar da ƙudirin korarsu, kuma Shugaban PDP na Jihar Bauchi, Samaila Burga, ya mara masa baya. Sai dai bayan sanarwar, Gwamna Fintiri ya fitar da wata sanarwa, wadda ya nesanta kansa daga matakin da jam’iyyar ta ɗauka. Ya ce ba ya goyon bayan korar da aka yi wa Wike, domin hakan zai ƙara haifar da rikici a cikin jam’iyyar....
    Sarki Sanusi II, ya yaba da ci gaban da jami’ar ke samu tare da farin ciki kan yawan mata da suka kammala karatu, yana fatan hakan zai ƙara yawan rawar da mata ke takawa a mulki da sauran ɓangarorin rayuwa. Tun da farko, Shugaban Jami’ar, Farfesa Ajith Kumar, ya bayyana cewa cikin ɗalibai 180 da suka kammala karatun 24 sun samu sakamako daraja ta ɗaya (First Class), tare da bayyana cewa wannan bikin yaye ɗaliban shi ne karo na farko da jami’ar ta raba digiri na biyu tun bayan amincewar Hukumar Kula da Jami’o’i ta Ƙasa (NUC), da ta samu. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai NAF Ta Ragargaza Mafakar Ƴan Ta’adda A Zamfara, Ta Halaka Da Dama November 15,...
    Haka zalika, a 2025, an samu kararraki 28 na ‘yan Nijeriya da suka kashe kansu. Shari’ar ta shafi mutane daga kowane jinsi da kuma masu matsayi daban-daban, ciki har da dalibai da kuma ‘yan kasuwa. Da yake zantawa wani dan jarida, masanin ilimin halayyar Dan’adam, kuma kwararre a kan lafiyar kwakwalwa, Dakta Shuab Waidi ya ce; batun kisan kai a halin yanzu, na bukatar da kulawar gaggawa ga mahukuntan kasa. Ya ce, “Kididdigar na nuna cewa, a kowane minti 33; ana asarar rai a Nijeriya sakamakon kashe kai, don haka, akwai bukatar cikin gaggawa a bude tattaunawa game da kashe kai ta hanyar gwajin lafiyar kwakwalwa. “Cutar tabin hankali, wani bangare ne na kisan kai da kai, amma kashe kai...
    Ta ce, “Kungiyar ta fi kai hare-hare a shagunan EE, inda suke amfani da barazana da tashin hankali wajen tilasta ma’aikata su bude dakunan ajiya na sirri kafin su gudu da wayoyi masu tsada da sauran na’urori.” A jimlace, sun sace kayayyaki da darajarsu ta kai fam miliyan £240,000. Jami’an tsaro sun gano masu laifin ta hanyar shaidar DNA, da kuma bayanan kira da rikodin motocin da suka yi amfani da su. An ce sun ci gaba da bibiyar kungiyar yayin da take shirin sake kai wani hari, inda a ranar 19 ga Nuwamba, 2024, jami’ai suka yi musu kwanton bauna suka kama mutane hudu daga cikinsu a lokacin da suke kokarin yin fashi a wani shagon EE da ke...
    ShareTweetSendShare MASU ALAKA Da ɗumi-ɗuminsa Tsohon Gwamnan Anambra, Willie Obiano, Ya Rasu Yana Da Shekaru 70 November 14, 2025 Manyan Labarai Musulmin da Aka Kashe  A Zamfara, Katsina Da Sokoto Sun Ninka Na Kiristoci A Tsakiyar Najeriya: MACBAN November 14, 2025 Manyan Labarai Kotu Ta Yanke Wa Mutum 4 Hukuncin Kisa Kan Kashe Wani Makanike A Kano November 14, 2025
    Babban taron dandalin kafafen yada labarai na kasashe masu tasowa da kwararru na kawancen Sin da Afirka da aka bude a jiya Alhamis a birnin Johannesburg da ke kasar Afirka ta Kudu, zai lalubo hanyoyin karfafa hadin gwiwa, da fadada yin magana da murya daya a tsakanin kasashe masu tasowa da kuma habaka gudanar da tsarin shugabancin duniya na bai-daya. Wanda kamfanin dillancin labarai na Xinhua, da Tarayyar Afirka (AU) da kamfanin Independent Media na kasar Afirka ta Kudu da sauran abokan hulda suka shirya, taron na kwanaki biyu ya samu halartar wakilai sama da 200 daga kafofin watsa labarai fiye da 160, da kungiyoyin kwararru, da hukumomin gwamnati da sauran cibiyoyi daga kasar Sin da kasashen Afirka 41, da...
    An sanya ranar 25 ga watan Nuwamba a matsayin ranar da za a fara shari’arsa kan zargin karkatar da biliyoyin kuɗi da EFCC ta gabatar. Obiano ya yi gwamna a Jihar Anambra daga 2014 zuwa 2022. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Musulmin da Aka Kashe  A Zamfara, Katsina Da Sokoto Sun Ninka Na Kiristoci A Tsakiyar Najeriya: MACBAN November 14, 2025 Manyan Labarai Kotu Ta Yanke Wa Mutum 4 Hukuncin Kisa Kan Kashe Wani Makanike A Kano November 14, 2025 Manyan Labarai Bayan Barazanar Amurka: Sultan Ya Nemi Hadin Kan ‘Yan Nijeriya Wajen Yaki Da Ta’addanci November 14, 2025
    El-Rufa’i ya kara da cewa mutane amintattu za a ba su mukamai idan ADC ta samu nasarar kwace mulki a hannun APC a 2027, yana mai cewa cewa kashi 40 cikin dari na mukamai za su je ga matasa. Ya yi kira ga magoya bayansa da su kiyaye masu yaudara da ke kokarin raba kan jam’iyyar, yana cewa, “APC ba za ta bar ku ku tafi cikin sauki ba, ku yi hankali.” Haka kuma, ADC ta gudanar da taron masu ruwa da tsaki a Jihar Zamfara, wanda mataimakin sakataren gudanarwa na kasa na jam’iyya ya shirya, don karfafa hadin kai tsakanin ‘yan jam’iyya da kuma karfafa musu gwiwar yin rajista da samun katin zabe. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Tambarin Dimokuradiyya Rikicin...
    Haka zalika, ya kafa hujjojinsa a kan “Rashin biyan ‘yan fansho a kan lokaci”, “Jigata’Yan-fansho Da Sunan Tantancewa”, “Jefa Razani A Zukatan Maikata”, da ”Salwantar Da Kudaden ‘Yan-fanshon”. Wadannan bayanai na Anwar, sun tabbatar da ko dai bai san abin da ya faru a Hukumar Fansho a lokutan da Kwankwaso ya yi Gwamnan Kano ba, ko kuma shi dan kanzagin wani dan siyasa ne da yake so ya kambama, duk da tauraruwarsa ta disashe. Duk wanda ya san yadda mulkin Kwankwaso ya inganta rayuwar ‘yan fansho a Jihar Kano, ya san cewa; duk abubuwan da Anwar ya fada ba gaskiya ba ne. A tarihin biyan fansho da garatuti a Jihar Kano, babu lokacin da ‘yan fansho suka ji dadi; irin...
    Kwamatin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya tsawaita da shekara guda wa’adin aikin tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya. Duk da shakkun da Amurka ta yi, Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, ya tsawaita wa’adin aikin tawagar ta MINUSCA, a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya har zuwa ranar 15 ga Nuwamba, 2026. Duk da haka, Majalisar ta nuna yiwuwar rage wa’adin saboda shiryen shiryen zaben da ake yi a shekarar 2026. An amince da kudurin da kuri’u 14 sai kuma kin amincewa daga Amurka. An samar da tawagar ta MINUSCA a watan Afrilun 2014 don kokarin kawo karshen yakin basasar da ya biyo bayan juyin mulkin da aka yi a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya kan...
    Kasashen Iran da Turkiyye sun jaddada mahimmancin karfafa zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin. Wannan bayyanin ya fito ne bayan tattaunawar wayar tarho data wakana tsakanin ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi, da takwaransu na Turkiyye Hakan Fidan, game da dangantakar dake a tsakanin kasashen biyu da kuma halin da ake ciki a yankin da ma duniya. A yayin tattaunawar ta wayar tarho, Ministocin Harkokin Wajen Iran da Turkiyya sun yi nazari kan dangantakar kasashen biyu kuma sun jaddada muhimmancin karfafawa da bunkasa dangantaka a dukkan fannoni masu amfani. Yayin da yake yaba wa kokarin rage tashin hankali tsakanin Pakistan da Afghanistan, Ministan Harkokin Wajen Iran ya jaddada muhimmancin karfafa shawarwari don kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a...
    Haka zalika, ya buga misali da Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kebbi, da aka yi garkuwa da shi, kuma aka biya wadanda suka sace shi miliyoyin kudade kafin a sako shi, wanda ya bayyana hakan a matsayin babban abin takaici. Dangane da batun Shugaban Amurka Donald Trump, Sultan Sa’ad ya bukaci Nijeriya da kada ta bari wasu kasashe su raba kawunansu, ya kuma bayar da tabbacin cewa; duk da kalubalen da ake fuskanta, Nijeriya za ta ci gaba da kasancewa mai girma da kuma ci gaba da samun hadin kai. Har ila yau, Tsohon Babban Hafsan Sojin Kasa, Abubakar Danbazau, a jawabinsa ya bayar da shawarar cewa; dole ne a magance matsalar rashin tsaro, matsalolin fatara, sauyin yanayi, rashin aikin...
    NDLEA ta bayyana cewa za ta ci gaba da jajircewa wajen yaƙar wannan matsala, tare da wayar da kan jama’a da kula da masu fama da shan ƙwayoyi, domin kare tsaron rayuka da zaman lafiya a ƙasar nan. Daga cikin waɗanda suka halarci taron akwai wakilin shugaban NDLEA, Birgediya Janar Muhammadu Buba Marwa (mai ritaya), wato Kwamanda Muhammadu Tukur; wakilin Gwamnan Jihar Kaduna, da wakilin Mai Martaba Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli, wato Alhaji Umar Muhammad Fagacin Zazzau. Haka kuma, Kwamandan NDLEA na Jihar Kaduna da wakilai daga ‘yansanda, sojoji, DSS, da sauran hukumomin tsaro sun halarta. Masu jawabi a wajen taron sun nuna farin ciki da wannan nasara, tare da yabawa jami’an tsaro, alƙalai, da jama’ar gari bisa...
    Rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna ta cafke wasu mutum uku da ake zargi da safarar bilAdama wadanda aka ceto yara 17 daga hannunsu a garin Zariya. Wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na rundunar, DSP Mansir Hassan, ya fitar, ta bayyana cewa yaran da aka ceto ana zargin an shirya safarar su ne zuwa Abuja da wasu sassan ƙasar da ma ƙetare. An dakatar da Hakimi da Dagaci kan rikicin manoma da makiyaya a Gombe Atiku ya karyata ba sojan da ya yi takaddama da Wike kyautar motar SUV Sanarwar ta bayyana cewa “an tari hanzarin ababen zargin ne da misalin ƙarfe huɗu na yammacin ranar 12 ga watan Nuwamba. “A wannan lokaci ne jami’an sashen Ɗan Magaji da...
    Cibiyar Masu Binciken Adadi ta Nijeriya (NIQS) ta yi kira ga gwamnatin tarayya da Majalisar Dokoki ta Kasa da su samar da mafita wajen kayyade kudin hayar gidaje, musamman a manyan birane, kamar Abuja. Shugaban Cibiyar, QS Kene Nzekwe ne ya yi kiran a ranar Laraba a Abuja a wani taron manema labarai don tunawa da taron NIQS karo na 31 da kuma babban taron cibiyar na kasa. Sau Ɗaya Na Taɓa Da-nasanin Fitowa A Cikin Fim – Tanimu Akawu Babu Wani Abu Kuskure Ga Sojan Da Ya Yi Sa-in-sa Da Ministan FCT – Matawalle Nzekwe, wanda ya bayyana cewa, Cibiyarsa tana bai wa gwamnati shawarwari amma ya nanata cewa, alhakin gwamnati ne ta ɗauki mataki da kuma daidaita kuɗin...
    1. Matsalar Mai Zura Ƙwallo  Ɗaya daga cikin manyan matsala ga magoya baya da masu nazari a wannan kakar shi ne rashin ɗaukar gogaggun ‘yan wasa, musamman a sashin kai mai zura kwallo. Rashin samun mai cin kwallaye wanda za a dogaro da shi ya bar Pillars ba su da ƙarfin kai hari mai hatsari a gaba. Ko da yake ƙungiyar sau da yawa tana saumn rinjayan samun kwallo da kirkirar damar kai hari, amma kash suna gaza amfani da waɗannan damarmaki zuwa nasara. Wanda hakan yake nuna rashin ‘yan wasa masu ƙwarewa da zasu ci kwallon, wanda ya sa ake dogaro da wanda suka kwana biyu kamar Rabiu Ali, yana iya kokarinsa amma ba aikinsa ba ne kuma tsufa...
    Ya yi nuni da rahoton 2021 da Cibiyar Binciken kasa ta Nijeriya ta fitar, wanda ya gano kimanin filaye da gine-ginen gwamnatin tarayya 11,866 da aka yi watsi da su a duk faɗin ƙasar.   Daga cikin manyan kadarorin da ɗan majalisar ya lissafa akwai Cibiyar Sakatariyar Tarayya da ke Ikoyi, Legas; Ginin Otal na Ƙasa da Ƙasa na Nijeriya, Suleja, Jihar Neja; Millennium Tower, Abuja; Ginin Hukumar Haraji ta Tarayya a Jihar Abia; Hedikwatar Dakin karatu na Ƙasa, Abuja; Kamfanin Masana’antar buga Labarai na Nijeriya, Kaduna; Ginin Masaƙa ta Kaduna; da Kamfanin Narka Alluminium na Nijeriya, Jihar Delta. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Lambar Yabo Da LEADERSHIP Ta Ba Mu, Ta Ƙara Zaburar Da Mu – Gwamna Sule...
    Gwamnan Sule ya ce irin wannan jaridar da ke kan gaba ta zaɓo shi a matsayin gwarzon gwamna, abun farin ciki ne sannan ya yaba wa kamfanin bisa tabbatar da sahihancin labarai da daidaitasu wanda hakan yasa ta bambanta ta da takwarorinta. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Kashi 74% Na Marasa Lafiya Sun Gamsu Da Ayyukan Kiwon Lafiya Na Nijeriya — Minista November 12, 2025 Manyan Labarai An Kama Direban Gwamnati Da Hannu A Satar Motar Ofishin Mataimakin Gwamnan Kano November 12, 2025 Manyan Labarai Za Mu Kare Sojojin Da Ke Bakin Aiki — Ministan Tsaro November 12, 2025
    Sauran sun haɗa da: Hon. Ibrahim Adamu Sarki a jam’iyyar PDP daga shiyya ta biyu sai , Nazifi Jibrin Muhammad na jam’iyyar PDP daga shiyya ta biyu da Haruna Dogo Mabo na.jamiyya NNPP daga shiyya biyu sai Honorable Isah Dan Maryam na PRP daga shiyya ta biyu da , Honarabul Isaac Auta Zankai na jam’iyyar SDP da Wilson Iliya Yange na jam’iyyar PDP, da Honarabul Simon Na Allah na jam’iyyar LP, sai Ibrahim Musa na jam’iyyar ADC daga shiyya ta biyu shi ne Sakataren kwamitin.   Da yake jawabi bayan kaddamar da kwamitin, Shugaban jam’iyyar na jihar, Elder Patrick Ambut, ya shawarci mambobin da su kasance masu jajircewa tare da tabbatar da adalci da gaskiya a cikin aikin da aka...
    Taron ya hada bijiman masana, da masu tsara manufofi, da masu ilimi,da masu bincike, da abokan hadin gwiwa na haɓaka harkar ilimi daga Afirka, Kudancin Asiya, da Birtaniya don tattauna dabarun inganta ilimi ta hanyar harshe.   Dr. Alausa, ya jaddada cewa, yayin da kiyaye harsunan asali har yanzu yana da mahimmanci ga al’adu, amma Turanci ya kamata ya zama babban harshen koyarwa tun daga firamare har zuwa makarantun gaba da sakandare don inganta fahimta da gogayyar ilimi a tsakanin Daliban Nijeriya da takwarorinsu na duniya. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai ‘Yansanda Sun Kama Mutane 4 Kan Zargin Fashi Da Makami A Bauchi November 12, 2025 Manyan Labarai Kashi 74% Na Marasa Lafiya Sun Gamsu Da Ayyukan Kiwon Lafiya...
    Ya kuma yi nuni da cewa, a binciken da za a yi na gaba, akwai bukatar gudanar da manyan gwaje-gwaje da za su mayar da hankali ga fadada nemo samfuran da za a yi aiki a kansu. Yana mai cewa, “har yanzu muna bukatar kara tabbatar da tasirin maganin da aka yi amfani da shi da kuma samar da nagartattun hanyoyin warkarwa ta yadda jami’an lafiya za su nakalci sahihin zabin da za su yi amfani da shi wajen magance matsalolin rashin haihuwa mabambanta, da kuma tabbatar da cimma muradun samun haihuwar.” Tabbas, kamar yadda kasar Sin take da sa kwazo cikin abubuwan da take yi, ina da yakinin za a zurfafa wannan bincike domin cike gibin da aka gano...
    A cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Laraba, Sakataren Yada Labarai na ofishin mataimakin gwamna, Ibrahim Shu’aibu, ya bayyana lamarin a matsayin “cin amana a fili da direban da aka kama ya yi.”   “Ofishin Mataimakin Gwamna ya yaba wa binciken gaggawa da rundunar tsaron ta yi ta hanyar amfani da kaifin basira da kwarewa,” in ji sanarwar. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Za Mu Kare Sojojin Da Ke Bakin Aiki — Ministan Tsaro November 12, 2025 Manyan Labarai Bayanan Da Muka Samu Sun Nuna An Fara Samun Tsaro A Nijeriya – Hafsan Sojin Ƙasa November 12, 2025 Manyan Labarai Yadda Ɓarawo Ya Shiga Gidan Gwamnatin Kano Ya Saci Motar Ayarin Mataimakin Gwamna November 12,...
    Daga Usman Muhammad Zaria Majalisar Zartarwa ta Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da Naira Biliyan daya da miliyan dari uku domin gyara da inganta tsofaffin ayyukan wutar lantarki a fadin jihar. Kwamishinan yada labarai, matasa, wasanni da al’adu na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed, ne ya bayyana haka ga manema labarai a Dutse. A cewarsa, wannan mataki na daga cikin jajircewar gwamnatin Malam Umar Namadi wajen inganta samar da wutar lantarki da kuma bunkasa ci gaban al’umma musamman a yankunan karkara. A cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai bayan zaman majalisar, Alhaji Sagir Musa Ahmed ya kara da cewa, aikin na nuna kudirin gwamnatin jihar na tabbatar da karin samun wutar lantarki, kara habakar tattalin arziki,...
    Ya bayyana cewa mutanen sun fita da sassafe don wani aiki, amma ‘yan bindigar suka tare su suka kashe su tare da tserews da babur ɗinsu . Mista Ajeh, ya roƙi hukumomin tsaro da su gano waɗanda suka aikata wannan ɗanyen aiki tare da gurfanar da su a gaban kotu. Haka kuma, ya buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta jiha da su ɗauki matakin gaggawa domin kawo ƙarshen matsalar rashin tsaro da ke ƙara ta’azzara a Jihar Nasarawa. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai ‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi Sama Da 200 A Katsina November 12, 2025 Manyan Labarai Bayanan Da Muka Samu Sun Nuna An Fara Samun Tsaro A Nijeriya – Hafsan Sojin Ƙasa November 12, 2025 Manyan Labarai...
    Gwamnatin Tarayya ta ce za ta kafa ka’idoji da jagorori da za su tsara samarwa da amfani da injinan noma a fadin Najeriya. Ministan Noma da Tsaron Abinci, Sanata Abubakar Kyari, ya bayyana haka a taron shekara-shekara na 45 na Ƙungiyar Injiniyoyin Noma ta Najeriya (NIAE), mai taken “Kafa Ka’idoji da Ƙarfafa Fasahohin da Aka Gwada Don Samar da Abinci da Ƙara Darajar Kayayyaki a Najeriya”, da aka gudanar a Ilorin. Ya ba da shawarar kafuwar cibiyoyin injinan noma a kowanne yanki na ƙasa, domin horo, gyara, da tsara fasahohin aikin gona. A cewarsa, bayan samun injina, mafi muhimmanci shi ne kafa tsarin daidaitawa, haɗa na’urori a gida, da tsarin kulawa, domin tabbatar da cewa kowanne injin da aka tura...
    A wani muhimmin mataki na inganta harkar lafiya a matakin ƙasa, Karamar Hukumar Gwarzo ta kaddamar da sabuwar Cibiyar Kiwon Lafiya ta Farko (PHC) da aka gina a garin Dankado, da ke cikin gundumar Sabon Birni. Taron kaddamarwar, wanda ke nuna wani sabon ci gaba a tsarin raya jama’a, ya samu halartar manyan jami’an gwamnati, sarakunan gargajiya, da wakilan al’umma. Shugaban Karamar Hukumar Gwarzo, Dakta Mani Tsoho Abdullahi, wanda Mataimakinsa, Alhaji Abdulmumin Garba Lakwaya, ya wakilta, ya tabbatar da jajircewar gwamnatin sa wajen tabbatar da cewa kowane yanki a cikin karamar hukumar na da damar samun ingantacciyar kiwon lafiya mai sauƙin samu da araha. Ya yaba wa Kakakin Majalisar Dokoki ta Gwarzo, Ahmad Shehu Sabon Birni, da sauran kansiloli bisa...
    An kama diraben da ke jan motar Shafiu Sharp-Sharp, domin yi masa tambayoyi. “An riga an fara bincike. Ana yi wa direban tambayoyi, yayin da Babban Jami’in Tsaro (CSO) ke duba bidiyon CCTV,” in ji wata majiya. “An miƙa bayanan motar ga jami’an tsaro domin su gano motar da kuma kama ɓarawon.” Kakakin gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa, bai amsa kiran waya da saƙonnin da aka tura masa ba. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Zargin Kisan Kiristoci: Dalilan Da Ya Sa Trump Ba Zai Iya Kai Wa Nijeriya Hari Ba November 12, 2025 Manyan Labarai Bayan Ganawa Da Tinubu, COAS Ya Tabbatar Wa ‘Yan Nijeriya Samun Ingantaccen Tsaro November 11, 2025 Manyan Labarai Cikin Wata Ɗaya,...
    Gwamnan Jihar Legas, Babajide Olusola Sanwo-Olu, ya ce a wannan zamanin na mulkin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, babu wani gwamna ko shugaban ƙaramar hukuma da zai yi ƙorafi kan ƙarancin kuɗi. Sanwo-Olu ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin wani taron ƙarawa juna sani na yini ɗaya da ƙungiyar Arewa Think Tank (ATT) ta shirya albarkacin cikar Nijeriya shekaru 65 da samun ’yancin kai, wanda aka gudanar a Arewa House da ke Kaduna. An buƙaci tsige shugaban APC na Kuros Riba ’Yan bindiga sun kashe mai juna biyu da wasu mutum 4 a Sakkwato Taken taron shi ne: “Shekaru 65 da samun ’yancin kai: Tafiyar Najeriya zuwa yanzu a ƙarƙashin Tsarin Sabunta Fata (Renewed Hope Agenda)”, inda aka haɗa...
    Wasu ’yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun kashe mutum biyar, ciki har da wata mata mai juna biyu a ƙauyen Alkalije da ke Ƙaramar Hukumar Yabo ta Jihar Sakkwato. Lamarin ya faru ne da sanyin safiyar Litinin lokacin da maharan suka mamaye ƙauyen, inda suka fara harbe-harbe kan mai uwa da wabi. An buƙaci tsige shugaban APC na Kuros Riba Mai cutar HIV ya yi wa ’yar shekara 4 fyaɗe a Yobe Wani mazaunin yankin da ya buƙaci a sakaya sunansa, ya ce maharan sun daɗe suna shigowa daga Jihar Kebbi suna kai hare-hare kan al’ummomin yankin. “Sun saba zuwa daga Kebbi da Silame, suna kashe mutane ko su yi garkuwa da su. A wasu...
    Ana fargabar cewa an yi wa wata yarinya ’yar kimanin shekara huɗu fyaɗe a ƙaramar hukumar Jakusko ta Jihar Yobe. Da yake zantawa da manema labarai fyaɗe da safiyar Litinin, mahaifin yarinyar ya bayyana cewa ta samu mummunan rauni a al’aurarta. John Cena ya lashe kambun Intercontinental karon farko a tarihi An ceto mutane 86 daga hannun ’yan ta’adda a Borno Mutumin da ake zargi da wannan aika-aikar mai suna Rabilu Sani, ɗan kimanin shekara 22, an gano cewa yana ɗauke da cutar kanjamau (HIV), kamar yadda mahaifin yarinyar ya tabbatar wa manema labarai. A wata hira da aka yi da mahaifin ta ta wayar tarho, ya bayyana cewa an kai yarinyar asibitin Jakusko tare da wanda ake zargi, inda...
    Alƙalin ya jaddada cewa wajibi ne a bi doka da oda domin kare tsarin dimokuraɗiyya, inda ya yi gargaɗin cewa karya doka na iya jefa ƙasa cikin ruɗani. A baya, Mai shari’a James Omotosho, ya taɓa bayar da irin wannan umarni, inda ya dakatar da PDP da INEC daga gudanar ko amincewa da sakamakon taron saboda rashin bin ƙa’idojin doka, ciki har da gaza bayar da sanarwar kwanaki 21 kafin gudanar da taron kamar yadda doka ta tanada. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Tinubu Ya Aika Wakilai Don Tattaunawa Da Birtaniya Kan Dawo Da Ekweremadu Nijeriya November 11, 2025 Manyan Labarai Faɗa Ya Kaure Tsakanin Boko Haram Da ISWAP, An Kashe Mayaƙa Sama Da 170 November 11, 2025...
    ’Tsohon Ministan Harkokin Cikin Gida, Laftanar Janar Abdulrahman Bello Dambazau (ritaya), ya bayyana damuwarsa kan yadda matsalar tsaro ta ta’azzara a Arewa, inda ’yan bindiga da ’yan ta’adda suka mamaye wasu yankuna suna kafa dokoki tare da karɓar haraji daga hannun jama’a. Janar Dambazau ya yi wannan jawabi ne a taron farko na kan tsaro da aka gudanar a Birnin Kebbi, Jihar Kebbi, mai taken “Barazanar Rayuwa da Tsaron Ƙasa.” Ya ce matsalar tsaro a Arewa ba sabuwa ba ce, domin ta wanzu tsawon sama da shekaru 20. “Ana kashe mutane a masallatai a Katsina, Borno, Zamfara da Kano. Arewa ta sha fama da rikicin manoma da makiyaya, ta’addanci da kuma hare-haren ’yan bindiga. “Mun kai wani matsayi da ’yan...