2025-12-13@14:34:51 GMT
إجمالي نتائج البحث: 3194

«Yan uwa»:

    Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Borno ta yi kira ga mazauna da su fito cikin kwanciyar hankali domin kada kuri’arsu a zaɓen ƙananan hukumomin da ake gudanarwa a yau Asabar. Tundunar ta tabbatar da cewa za a samar da isasshen tsaro a lokacin zaɓen da kuma bayan kammalawarsa. Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar, CP Naziru...
    Wani kwalekwale da ke ɗauke da fasinjoji takwas ya kife yayin da yake ƙetare kogin da ke kan iyaka da garin Gamboru na Najeriya da Fotokol a ƙasar Kamaru, inda mutane uku suka mutu. Lamarin ya faru ne da misalin qarfe 6:30 na yamma lokacin da kwalekwalen, wanda wani Mamman Nur Abbagana na Kasuwan Katako,...
    Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin Shirin na duniyarmu a yau shiri wanda yake kawo maku labarai masu muhimmanci a makon da ya gabata, wadanda suka shafi siyasa tattalin arziki zamantakewa tsaro da sauransu. Sannan daga karshe idan akwai lokaci mu ji ra’ayin masana dangane da su. Da...
    PDP wanda ke da gwamnonin 11 bayan zaben 2023, yanzu tana da biyar kawai tare da karin wasu suna nuna suna son barin jam’iyyar. Yawancin gwamnonin da suka sauya sheka a cikin wannan lokaci sun koma APC, yayin da jam’iyyar Accord ta samu guda daya. Gwamnonin da suka bar PDP zuwa APC su ne Umoh...
    Wani abun lura ma a nan shi ne yadda a matsayinta na kasa mai tasowa ta farko a tarihin duniya da ta cimma nasarar samun wadata cikin lumana, Sin ta samar da wata taswira mai inganci, wadda sauran kasashe masu tasowa za su iya bi domin raya kansu cikin lumana, kuma karkashin hakan ne take...
    Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya zargi ‘yan siyasan Nijeriya da zagon kasa ga ci gaban kasar ta hanyar daukar mukaman gwamnati a matsayin gadon gidansu a maimakon amanar jama’a. Da yake jawabi a ranar Laraba a yayin taro karo na 15 mai taken, “ya Isa haka” da ya gudana a jihar Legas,...
    Ya ce, wanda ake kara ya nema kuma an bashi kudin fansa har Naira miliyan 15 daga iyalan wanda aka kashe kafin su kashe shi.   “Sun bugi wanda aka kashe a kai da ƙirji da sanda sannan daga baya suka binne gawar a gidan Adamu da ke Dawakin Kudu,” in ji mai gabatar da...
    Hukumar kwallon kafa ta Nigeria (NFF) ta taya Osimhen murnar samun wannan babbar nasarar a kwallon kafa ta hanyar sanya hoton Osimhen a babban shafinsu na Facebook da yake da mabiya fiye da miliyan daya, Osimhen na daga cikin yan wasan da kocin tawagar ta Super Eagles Eric Chelle ya gayyata domin buga gasar kofin...
    Tafarkin samun ci gaba mai karfi da inganci, da karuwar kuzarin kirkire-kirkire da ci gaba da fadada bude kofa, su ne suka hadu suka samar da wani sabon matsayi ga tattalin arzikin kasar Sin a taswirar tattalin arzikin duniya. Ci gaba mai inganci da fadada bude kofa, ba muhimman jigon ne dake ingiza tattalin arzikin...
    Ministan harkokin wajen Turkiya Hakan Faidan ne ya bayyana cewa; kasarsa za ta iya daukar nauyin wararen matsalar Falasdinu, kuma a shirye take ta aike da sojoji zuwa yankin na Gaza idan bukatar hakan ta taso. Fidan ya fada wa kamfafen watsa labaru cewa; Tukriya a shirye take ta yi duk abinda za ta iya...
    Ministan taron  Haramtacciyar Kasar Isra’ila Ben Gafir ya sha alwashin rushe kabarin Sheikh Izzuddin al-Kassam dake kusa da birnin Haifa. Ben Gafir ya wallafa hotonsa na tsokana a shafinsa n asada zumunta a kusa da makwancin shahararren malamin addinin mususuluncin tare da motar buldoza a kusa da shi, tana rusa wata hema da aka gina...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A kwanakin baya, Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da sabon tsarin jadawalin karatu ga makarantun firamare da sakandare. Sabon tsarin, wanda Ma’aikatar Ilimi ta ƙasa ta tsara, yana da nufin inganta koyarwa da koyo, da rage nauyin lodi ga dalibai, da kuma tabbatar da cewa malamai suna da isasshen...
    Hukumar Kula da Ayyukan ’Yan Sanda ta Najeriya, tare da haɗin gwiwar Rundunar ’Yan Sandan Kasar sun buɗe shafin neman aiki domin ɗaukar sabbin ’yan sanda na constables da kuma ma’aikata masu kwarewa ta musamman. A kwanan nan Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin ɗaukar sabbin ’yan sanda 50,000 a fadin ƙasar...
    Daga Usman Muhammad Zaria Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu, Dr. Builder Muhammad Uba, ya umarci a gaggawata gyaran bututun da suka hada tashar tacewa da samar da ruwa yankunan Dutsawa da Kantudu. Wannan mataki ya biyo bayan matsalolin da ake yawan fuskanta sakamakon lalacewar wutar lantarki da na’urar janareto, wanda ke hana jama’a samun...
    Shugaban kasar |iran Mas’ud pezeshkiyan da yake Magana a wajen taron ranar mata a kasar iran ya bayyana cewa maza ta da mata suna taka rawa iri daya wajen ciyar da alumma gaba, kan kyawawan ayyukan, kana ya jaddada cewa mata musamman iyaye suna taka muhimmiyar rawa wajen samar da matasa masu tasowa da kuma...
    Jami’ai sun ce mutane sama da dubu 500 ne kawo yanzu aka tursasawa barin muhallansu a Thailand da kuma Cambodia a yayin da rikicin kan iyaka tsakanin ƙasashen biyu ke ƙara ƙamari. Rundunar sojin Thailand ta ce Cambodia ta harba mata dubban makaman roka tun bayan da suka soma rikici da juna. Dubban mutane ne...
    Taron kasa da kasa na musamman wanda aka gudanar a wata Jami’a a nan Tehran dangane da nasarar da JMI ta samu kan HKI da Amurka a yakin kwanaki 12 a cikin watan yulin da ya gabata ya jawo hankalin kasashen duniya da dama, sannan ya sauya yadda ake daukar HKI a yankin, musaman a...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A kwanakin nan, tawagar ’yan majalisar dokokin Amurka ta kawo ziyara Najeriya domin tattaunawa kan tsaro da tashin hankalin da ake ta fama da shi a yankunan Arewa da tsakiyar ƙasar, musamman rikice-rikicen da suka yi sanadiyyar kashe-kashe da duniya ke fargabar suna iya daukar salo na kisan...
    Jaridar Daily Trust da gidan talabijin na Trust TV, dukkansu mallakar kamfanin Media Trust, a bana ma sun sake yin fice bayan ’yan jaridansu suka lashe kyautar binciken kwakwaf ta Wole Soyinka ta bana. ’Yan jaridar na Daily Trust da Trust TV, Afeez Hanafi da Muslim Muhammad Yusuf, sun lashe gasar ne a matsayin zakaru...
    Kakakin rundunar sama ta tarayyar Najeriya, wato ‘Nagerian Air Force’ Ehiment Ejodame ya bayyana cewa jirgin wani jirgin saman rundunar dauke da mutane 11 ya yi saukan gaggawa a kasar Burkina Faso a ranr litinin da ya gabata. Jiridar Daily Trust ta Najeriya ta nakalto Ejodame yana fadar haka a yau Talata ya kuma kara...
    Gwamantin Nigeria ta aike da jiragen yaki zuwa kasar Benin domin taimaka wa gwamnatin farar hula domin dakile yunkurin juyin mulkin da aka yi a kasar. Aikin da jiragen yakin su ka fara yi, shi ne shimfida ikonsu a sararin samaniyar kasar Benin a ranar Lahadin da ta gabata,adaidai lokacin da sojoji da suke biyayya...
    A wani rahoton da jaridar Jerissalam Post” ta buga ta ambaci cewa; Tun bayan farmakin 7 ga watan Oktoba 2023, ana kara samun matalauta da talauci. Rahoton ya yi nuni da cewa karuwar talaucin yana da alaka ne da yadda farmakin 7 ga watan Oktoba ya yi tasiri a cikin tattalin arziki “Isra’ila”. Haka nan...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A yau al’ummar mu na fuskantar barazana ta wata siga da ba kasafai ake gane ta ba, wato guba da ke shiga jikin ɗan Adam ta hanyar abinci irin su nama, kifi, madara da sauran kayayyakin da muke ci a kullum. Sau da yawa dabbobi ko kifaye suna...
    Daga Aliyu Muraki  Gwamna Abdullahi Sule na Jihar Nasarawa ya ce gwamnonin Arewa sun amince su sayi na’urorin zamani na tsaro da kuma daukar matasa aiki don tallafawa ayyukan tsaro domin magance matsalolin rashin tsaro a yankin. Gwamnan ya bayyana hakan ne a zaman Majalisar Zartarwa ta Jihar da aka gudanar a Lafia, babban birnin...
    Daga Nasir Malali An kashe ’yan bindiga guda goma sha takwas a wani samame da Rundunar Hadin Gwiwa ta Operation Fansan Yamma ta kai a kauyen Kurawa da ke Karamar Hukumar Sabon Birni ta Jihar Sokoto. A wata hira ta wayar tarho, wani shaida daga yankin, Malam Aminu Muhammad, ya shaida wa Rediyon Najeriya a...
                Daga Bello Wakili Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi ganawar sirri da gwamnonin jihohi shidda daga sassan ƙasar a ci gaba da tattaunawar da ake yi domin ƙarfafa batun tsaro a ƙasa. Gwamnonin da suka halarci taron sun hada da Gwamna Monday Okpebholo na jihar Edo, Umar...
    Dakarun kare juyin juya halin musulunci na kasar Iran ya bayyana cewa makamai masu linzamu na dakarun sun fada kan matatar man fetur na Haifa a HKI har sau biyu a yakin kwanaki 12 da ta fafata da Iran a cikin watan Yunin wannan shekara. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Burgediya...
    Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bada sanarwan kubutar da yan makaranta 100 daga cikin wadanda ‘yan ta’adda suka sace a wata makaranta a jihar Naija a cikin watan Nuwamban da ya gabatata. Tashar talabijan ta almayadeen ta kasar Lebanon ta nakalto kamfanin dillancin labaran reuters na cewa jami’an tsaron kasar sun sami nasarar kubutar da yan...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Batun samar da ‘yansandan jihohi na ƙara ɗaukar hankalin ‘yan Najeriya, musamman a dai-dai lokacin da matsalar tsaro ke ƙara ta’azzara a sassa daban-daban na ƙasar nan.   Sai dai, samar da ‘yansandan jihohi ba abu ne mai sauƙi Kamar yadda wasu ke tunani ba. Gwamnatocin jihohi na...
    Masana harkokin siyasa, jakadu da ƙungiyoyin fararen hula sun bayyana cewa rashin shugabanci nagari da son mulki na dogon lokaci su ne manyan dalilan da ke haddasa yawaitar juyin mulki a yankin Afirka ta Yamma. Wannan na zuwa ne bayan yunƙurin juyin mulki da aka yi a Jamhuriyar Benin a ranar Lahadi, wanda ya jefa...
    Rundunar Sojin Saman Najeriya (NAF), ta ce ta taka muhimmiyar rawa wajen daƙile yunƙurin juyin mulki a Jamhuriyar Benin, bayan wasu sojoji sun bayyana hamɓarar da Gwamnatin Shugaba Patrice Talon. Gungun sojojin, sun bayyana cewa ta rushe gwamnati tare da dakatar da kundin tsarin mulki, da rufe iyakokin ƙasar. An gano gawar malamin Islamiyya da...
    ’Yan bindiga sun kai sabon hari wasu yankuna na Jihar Sakkwato, inda suka kashe mutane huɗu tare da yin awon gaba da mata huɗu. Wani mazaunin Gatawa, ya shaida wa Aminiya ce harin ya faru ne a daren ranar Asabar, lokacin da ’yan bindiga sama da goma suka shiga garin a kan babura. Mutum 5...
    ’Yan bindiga sun kai sabon hari wasu yankuna na Jihar Sakkwato, inda suka kashe mutane huɗu tare da yin awon gaba da mata huɗu. Wani mazaunin Gatawa, ya shaida wa Aminiya ce harin ya faru ne a daren ranar Asabar, lokacin da ’yan bindiga sama da goma suka shiga garin a kan babura. Mutum 5...
    Gwamnatin Jamhuriyar Benin ta bayyana cewa ta dakile wani yunkurin juyin mulki, bayan da wasu sojojin ƙasar suka sanar da cewa sun hambarar da shugaba Patrice Talon a gidan talabijin na kasar. Talon, mai shekaru 67, tsohon dan kasuwa ne wanda aka yiwa lakabi da “Sarkin Auduga na Cotonou”, zai mika mulki a watan Afrilun...
    An harbe wani jami’in ɗan sanda har lahira, yayin da yake tsaka da binciken ababen hawa a Benin a Jihar Edo. Kakakin rundunar, CSP Moses Yamu, ya ce lamarin ya faru da misalin ƙarfe 12 na ranar Juma’a, lokacin da jami’an rundunar suka tsayar da wata baƙar mota ƙirar Lexus, amma ta ƙi tsayawa. ’Yan...
    ’Yan sanda sun ceto yara 2 da aka yi garkuwa da su, masu shekaru hudu da biyar, a Jihar Borno. An ceto yaran ne a yayin wani samame da ’yan sanda suka kai a Ƙaramar Hukumar Jere, inda masu garkuwar suka je karbar kuɗin fansa. Sanarwa da ASP Nahum Kenneth Daso, kakakin rundunar ya fitar...
    Gwamnatin Kano ta tabbatar da kama Muhuyi Magaji Rimingado, tsohon shugaban hukumar yaƙi da cin hanci ta jihar ranar Juma’a, inda ta yi zargi wasu ‘yansiyasa da hannu a kamen nasa. Wata sanarwa daga ofishin Kwamashinan Shari’a Abdulkarim Maude ta ce jami’an ‘yansanda ne suka kama lauyan a ofishinsa da ke kan titin Zariya da...
    Makwanni biyu bayan da masu garkuwa su ka sace kananan yara ‘yan mamaranta an bayyana cewa;har yanzu da akwai 250 a hannun barayin mutanen. A ranar 21 ga watan Nuwamba ne dai masu dauke da makamai su ka kutsa cikin wata makaranta ta majami’ar Roman Katolika, su ka yi awon gaba da dalibai 300 da...
    Shugaban kasar Rasha Vladmir Putin wanda ya kai ziyarar aiki kasar India ya bayyana cewa kasar tasa da kuma abokiyar kawancenta India za su bunkasa kasuwancinsu.  Ziyarar ta shugaban kasar Rasha a Indiya, tana a karkashin taron da kasashen biyu suke yi ne daga lokaci zuwa lokaci wanda wannan shi ne karo na 23 da...
    Babban magatakardar kungiyar Hizbullah Sheikh Na’im Kassim wanda ya gabatar da jawabi a jiya Juma’a da marece ya yi suka akan yadda aka shigar da farar hula dan kasar Lebanon a cikin kwamitin dake sa ido akan tsagaita wutar yaki da Haramtacciyar kasar Isra’ila, yana mai bayyana hakan da cewa; ya sabawa dukkanin bayanan da...
    Fadar  gwamnatin kasar Iraki ta sanar da cewa ba ta masaniya akan yadda aka shigar da sunayen Ansarullah na Yemen da kuma Hizbullah ta kasar Lebanon a cikin jerin sunayen kungiyoyin ‘Yan ta’adda da aka rike kudadensu dake bankunan kasar. Bayanin fadar gwamnatin kasar ta Iraki ya kuma kara da cewa; Matakai irin wadannan da...
    Daga Usman Muhammad Zaria Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, ya yaba da gagarumin cigaba a harkar noma da Gwamna Umar Namadi ya samar cikin shekaru biyu kacal na mulkinsa. Ya bayyana haka ne a masarautar Gumel cikin Jihar Jigawa, yayin kaddamar da sabon masallacin Juma’a da Gidauniyar Kashim Shettima ta gina a matsayin wani ɓangare...
    Shugaba Bola Ahmad tinubu na tarayyar Najeriya ya nada wasu karin jakadu 65 wadanda suka hada da sanatoci masu ci da kuma tsoffin gwamnoni har’ila yau da kwararrun jakadu. Jaridar Premium times ta Najeriya ta bayyana cewa shugaban ya aikawa majalisar dokokin kasar wasika dangane da hakan, wasika wacce shugaba majalisar dattawa Godswill Akpabio ya...
    Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnatin Jihar Jigawa ta gudanar da bikin bude tayin bada kwangilar samar da wutar lantarki a wasu garuruwa dake kananan hukumomin Jihar. A lokacin da yake jawabi a yayin gudanar da bikin daya gudana a sakatariyar Jihar dake Dutse, Shugaban hukumar, Injiniya Zubairu Musa ya bayyana cewar tayin bada kwangilar samar...
    Rundunar ’yan sandan jihar Borno ta kama matashin nan da ake zargi da kashe makwabciyarsa a unguwar Shuwari II, a garin Maiduguri babban birnin jihar, ta hanyar daba mata wuka. Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, ASP Nahum Kenneth Daso, ya ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11:00 na dare a ranar Talata. Amurka...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Masu iya magana kan ce banza ba ta kai zomo kasuwa. In ba haka ba, me ya kai matasan da ake zargi da aikata manyan laifuffuka ofishin ’yan sanda, suka kuma fit oba tare da wani ya harae su ko ya yi mutsu tsawa ba, balle ya saka...
    Dan wasan taekwando na kasar iran  Abolfazl zandi ya samu lambar yazo ta zinariya a ranar farko ta gasar takwando ta duniya  da ake gudanarwa a birnin Nairobi na kasar kenya , kuma ita ce lambar yabonsa na biyu a cikin kwanaki 35, Gasar tana gudana ne a filin wasa na moi international sport center...
    Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa (mai ritaya), ya ce ba zai bai wa ’yan Najeriya kunya ba, saboda ƙwarin guiwar da suke da shi a kansa. Musa, wanda Shugaba Bola Tinubu ya naɗa ministan tsaro, ya bayyana haka ne a ranar Laraba lokacin da aka tantance shi a Majalisar Dattawa. Tsaro: Gwamnonin Arewa na shirin...
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Yobe, ta ce ta samu rahoton laifuka 25 na cin zarafin mata da ƙananan yara a Ƙananan Hukumomin Jakusko, Fika, Potiskum da Tarmuwa, inda aka kama mutum 28 da ake zargi da aikata laifukan. Kakakin rundunar, SP Abdulkarim Dungus, ya ce an kama masu laifin ne cikin watanni uku da suka...
    Daga Bello Wakili Shugaba Bola Tinubu ya rantsar da Shugaban Hukumar Kidaya ta Kasa (NPC) da kwamishinoni biyu na hukumar, tare da sabbin manyan  sakatarori guda biyar da aka nada a gwamnatin tarayya. Daga nan ya jagoranci taron Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) a fadar shugaban kasa da ke Abuja. Bayan karanta takardar tarihin rayuwarsu,...