Aminiya:
2025-12-13@14:17:18 GMT

’Yan sanda sun ba da tabbacin isasshen tsaro a zaɓen ƙananan hukumomin Borno

Published: 13th, December 2025 GMT

Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Borno ta yi kira ga mazauna da su fito cikin kwanciyar hankali domin kada kuri’arsu a zaɓen ƙananan hukumomin da ake gudanarwa a yau Asabar.

Tundunar ta tabbatar da cewa za a samar da isasshen tsaro a lokacin zaɓen da kuma bayan kammalawarsa.

Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar, CP Naziru Abdulmajid, ya yi wannan kira ne a yayin wani taron tsaro mai muhimmanci da aka gudanar tare da ƙungiyoyi, kwamandojin tsaro, shugabannin sassa, da dukkan DPOs a faɗin jihar, kafin zaɓen ƙananan hukumomi da ake gudanarwa a yau Asabar, 13 ga Disamba, 2025.

“Rundunar tana kira ga jama’a da su fito ba tare da wani shakka ba domin aiwatar da nauyin da ke kansu cikin lumana,” in ji sanarwar, wadda kakakin Rundunar, ASP Nahum Kenneth Daso, ya fitar a Maiduguri

Ya kuma gargadi mazauna jihar da su kasance cikin taka tsantsan, tare da kauce wa labaran ƙarya da ka iya kawo cikas ga zaman lafiyar jama’a.

Rundunar ta bayyana cewa an riga an fara amfani da dabarun tura jami’an tsaro da sanya idanu a fadin jihar domin tabbatar da cewa zaɓen ya gudana cikin kwanciyar hankali ba tare da wata matsala ba.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Yan Sanda Zaɓe Zaɓen Ƙananan Hukumomi

এছাড়াও পড়ুন:

Sojoji sun daƙile harin ’yan ta’adda a Borno

Dakarun Sojin Operation HADIN KAI sun daƙile wani hari da ’yan ta’addan ISWAP suka kai sansanin soji na Mairari da ke Jihar Borno.

Harin ya fara ne daga daren ranar Juma’a zuwa safiyar Asabar.

’Yan sanda sun ba da tabbacin isasshen tsaro a zaɓen ƙananan hukumomin Borno Kotu ta sa ranar yanke hukunci a Shari’ar Abba Kyari da NDLEA

A cewar rundunar, ’yan ta’addan sun yi ƙoƙarin shiga sansanin ta hanyar amfani da motoci biyu da suka cika su maƙil abubuwan fashewa.

Jami’in yaɗa labarai na Operation HADIN KAI, Laftanar Kanal Sani Uba, ya ce sojoji sun gano motocin kuma suka tarwatsa su kafin su kai ga shiga sansanin.

Rahotanni sun nuna cewa an kashe ’yan ta’adda da dama, yayin da wasu suka jikkata.

Waɗanda suka tsira sun kwashe gawarwaki da waɗanda suka ji rauni a wajen bayan tafka artabu.

Bayan daƙile harin, sojoji tare da haɗin gwiwar sauran jami’an tsaro, sun gudanar da bincike a yankin.

A yayin binciken, sun gano gawar ’yan ta’adda tare da ƙwato makamai da kayayyaki da dama da suka bari.

Kayayyakin da aka ƙwato sun haɗa da bindigogi, harsasai, gurneti, babura, na’urorin sadarwa, kayan yaƙi, da kayayyakin jinya.

Laftanar Kanal Uba, ya ce ƙwato waɗannan kayayyaki ya rage ƙarfin ’yan ta’addan da ikonsu na ci gaba da kai hare-hare a yankin.

Ya ƙara da cewa dakarun sun lalata motocin da aka maƙare da kayan fashewa, wanda ya jawo lalacewar wasu wurare biyu, amma ba su yi nasarar shiga sansanin sojin ba.

Ya ce a halin yanzu sojoji na ci gaba da yin sintiri domin hana sake kai hare-hare tare da bai wa al’ummar yankin tabbacin tsaro.

Rundunar sojin ta jaddada ƙudirinta na kawar da ’yan ta’adda tare da dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin Arewa maso Gabas.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Sojoji sun daƙile harin ’yan ta’adda a Borno
  • Gwamnatin Jigawa Ta Amince da Sama da Naira Biliyan 2.6 Domin Aikin Hajjin 2026
  • Iyaye Sun Yi Fitowar Farin Dango Don Yi Wa “Yayansu Allurar Rigakafi a Sule-Tankarkar
  • Zaɓen 2027 ya hana ni korar wasu ma’aikata – Bago
  • Ƴan Bindigar Daji: Jihohin Arewa 7 Sun Kaddamar Da Rundunar Fatattakar Su
  • Gwamnonin Arewa Sun Yi Rawar Gani A Kafa Gidauniyar Fuskantar Matsalar Tsaro
  • ‘Sojojin Najeriya da na Ivory Coast 200 sun shiga domin tsaftace Jamhuriyar Benin’
  • Hukumomin Ilimi a Jihar Jigawa Sun Kare Kasafin Kudinsu a Gaban Majalisa
  • Ma’aikatar Mata da Walwalar Jama’a ta Jihar Jigawa ta Kare Kasafin Kudinta a Gaban Majalisa