Leadership News Hausa:
2025-11-02@19:36:14 GMT

’Yansanda Sun Kama Sojan Gona Da Motocin Sata 3 A Jigawa

Published: 18th, September 2025 GMT

’Yansanda Sun Kama Sojan Gona Da Motocin Sata 3 A Jigawa

Tun a ranar 7 ga watan Satumba, 2025, wani mutum mai suna Hussaini Manager ya kai rahoto ofishin ’yansanda na Kafin Hausa cewa an sace masa mota ƙirar Golf mai launin shuɗi mai lambar MGA 108 JG a Agura Motor Park, Kafin Hausa.

Bincike ya gano cewa ɗaya daga cikin mutanen na yin sojan gona ne, yana kiran kansa Lance Corporal Kabiru Musa, alhali kuma ɗan asalin unguwar Rimin Kebe ne a Jihar Kano.

Lokacin da aka cafke su, an samu mota, katin ATM guda bakwai, lasisin tuƙi guda biyu, da wasu abubuwa da ake zargin na damfara ne a hannunsu.

Bayan kammala bincike, an gurfanar da su a gaban kotu.

Kwamishinan ’yansandan Jihar Jigawa, Dahiru Muhammad, ya yaba wa jami’an Kafin Hausa bisa ƙwazo da ƙwarewar da suka nuna wajen cafke mutanen.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Yansanda Jigawa

এছাড়াও পড়ুন:

Dalilin Da Ya Sa Hukumar NIWA Ta Fara Gyaran Hanyoyin Ruwa A Jihar Legsa

Manajar  ofishin na NIWA,  da ke a jihar ta Legas Injiniya Sarat Braimah ta bayyana cewa, tura ma’ikatan hukumar domin yin aikin, zai taimaka wajen gudanar da aikin a cikin inganci.

Kazalika, ya sanar da cewa, hakan zai kuma bayar da damar yin safarar kaya a cikin sauki da kuma safarar matafiya da ke bin hanyar ruwa ta yankin na Ikorodu.

“Mun yi nazari a cikin kwanciyar hankali kan yadda za a tabbatar da an cire fulawar da ke a cikin kasan ruwan ba tare da wata miskila ba tare da kuma bai wa jiragen ruwan damar yin zirga-zirgarsu a hanyoyin ruwan, ba tare da wata matsala ba, “ Inji Injiya Braimah.

“ Aikin ya wuce batun fannin samar da saukin yin sufurin jiragen ruwan har da tabbatar da an kiyaye janyo matsala ga ayyukan kamun Kifi a hanyoyin na ruwan, “ A cewar Inji Manajar.

Ta kara da cewa, babban shugabanmu na hukumar ta NIWA,  Bola Oyebamiji, ne tuni ya riga ya bayar da kwangilar yin aikin, ba wai a jihar Legas kawai ba, har da a sauran hanyoyin ruwa  da ke a sassan kasar.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Tsokaci Dangane Da Juyin Mulki A Nahiyar Afirka November 2, 2025 Labarai Barazanar Amurka Kan Kisan Kiristoci A Nijeriya: Tinubu Da Trump Za Su Gana Kwanan Nan — Bwala November 2, 2025 Manyan Labarai An Kashe Mutum 3 Yayin Da ‘Yan Bindiga Suka Kai Hari Kan Iyakokin Kano November 2, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kisan Kiristoci: Ba zan yaƙi ƙasar iyayena kan labaran ƙarya ba — Sojan Amurka
  • Dalilin Da Ya Sa Hukumar NIWA Ta Fara Gyaran Hanyoyin Ruwa A Jihar Legsa
  • Gwamna Namadi Ya Bada Motocin Aiki Goma Ga Rundunar ‘Yan Sanda
  • Gwamnatin Jigawa Ta Bada Motocin Aiki Goma Ga Rundunar ‘Yan Sanda
  • An Cafke Ma’aikatan Gidan Marayu Da Suka Sayar Da Yara 4 A Kan Naira Miliyan 3
  • Gwamnatin Jigawa Za Ta Gina Gidaje 52 A Babban Birnin Jihar
  • ’Yan bindiga sun sace fasinjoji a cikin motocin bas a Kogi
  • Ƴansanda Sun Kama  Wani Mai Wasa Da Bindiga AK-47 A Cikin Wani Bidiyo A Adamawa
  • An sake kama shi a cikin ’yan fashi kwana 5 da fitowa daga kurkuku
  • ‘Yansanda Sun Ceto Mutum Ɗaya, Sun Kama Mace Da Zargin Garkuwa Da Mutane A Dajin Kwara