Miyetti Allah ta roki Gwamntin Kwara da ta sa baki kan rufe Kasuwar Kara da Shugaban Karamar Hukuma Ya Yi
Published: 20th, September 2025 GMT
An bukaci gwamnatin jihar Kwara da ta gaggauta shiga tsakani kan rufe kasuwar Kara da ke yankin Kwara ta Kudu da shugaban karamar hukumar ya yi domin ceto harkokin kasuwanci daga durkushewa.
Shugaban kungiyar Miyetti Allah reshen jihar Kwara, Alhaji Shehu Garba ne ya yi wannan roko a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Ilorin.
Sanarwar ta ce shirin rufe kasuwannin Kara da ke yankin Kwara ta Kudu da shugaban karamar hukumar ya yi ba tare da sanin sarakunan gargajiya da shugabanni da masu gudanar da aiki ba, bai dace ba.
Ya bayyana cewa kafin daukar irin wadannan shawarwarin da shugaban karamar hukumar ya yi ya kamata a yi shawarwari da yawa don tafiyar da wadanda abin ya shafa.
A cewarsa da yawa daga cikin ‘yan kasuwar ba su da masaniyar wannan hukunci, kuma suna cikin kasuwannin Kara da kayansu suna gudanar da sana’o’insu.
Ta ce rufe kasuwannin Kara a wannan lokaci zai gurgunta harkokin kasuwanci tare da kara fuskantar kalubalen tattalin arziki da ya addabi iyalai a yankin, jihar da ma kasa baki daya.
Yana kira da a gaggauta janye sanarwar da aka fada domin tabbatar da gaskiya da adalci.
Shugabannin kananan hukumomin Ifelodun, Isin, Irepodun, Offa, Ekiti, Oke-Ero da kuma Oyun dake jihar Kwara ta Kudu sun bayar da umarnin rufe kasuwannin Kara ba tare da bata lokaci ba saboda tabarbarewar tsaro.
REL/ALI MUHAMMAD RABIU
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Kwara kasuwannin Kara
এছাড়াও পড়ুন:
Tinubu ya janye dokar ta-ɓaci da ya sanya a Ribas
Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya janye dokar ta-ɓaci da ya ayyana ta tsawon watanni shida a Jihar Ribas.
Tinubu, ya ayyana dokar tun a ranar 18 ga watan Maris, 2025, saboda rikicin siyasa da ya haifar da tsaiko a harkokin mulki tsakanin ɓangaren Zartarwa da Majalisar Dokokin jihar.
NECO ta saki sakamakon jarabawar 2025 Saudiyya ta saki ’yan Najeriya 3 da ta kama kan zargin safarar miyagun ƙwayoyiA jawabin da ya gabatar a Fadar Shugaban Ƙasa a ranar Laraba, Tinubu ya ce matakin dokar ta-ɓacin ya cimma manufarsa, kuma ba za a tsawaita ba ƙarewar wa’adin da aka gindaya.
“Ina farin ciki yau game da bayanan da ke hannuna, an samu yanayin fahimta a tsakanin dukkanin masu ruwa da tsaki a Jihar Ribas domin dawo da mulkin dimokuraɗiyya cikin gaggawa,” in ji Shugaban Ƙasa.
Gwamnan Jihar, Siminalayi Fubara, da mataimakiyarsa Ngozi Nma Odu, tare da ‘yan majalisar dokokin jihar, za su koma kan kujerunsu daga ranar Alhamis, 18 ga watan Satumba, 2025.
Tun da farko, dokar ta-ɓacin ta dakatar da manyan jami’an gwamnati da masu madafun iko na jihar sakamakon rikici da aka daɗe ana yi a jihar.
“Da ban ayyana wannan dokar ta-ɓacin ba, da hakan ya zama babbar gazawa a wajena a matsayina na Shugaban Ƙasa.
“Amma yanzu da zaman lafiya da doka suka wanzu, al’ummar Jihar Ribas za su sake cin moriyar dimokuraɗiyya,” in ji Tinubu.
Ya kuma yi kira ga gwamnoni da majalisun dokokin jihohi na faɗin Najeriya da su ci gaba da wanzar da zaman lafiya da haɗin kai tsakanin ɓangaren zartarwa da na majalisa.
Har ila yau, ya jaddada cewa zaman lafiya da kyakkyawan shugabanci su ne tubalin kawo ci gaban dimokuraɗiyya ga al’umma.