Aminiya:
2025-12-10@17:05:22 GMT

Najeriya da Saudiyya sun rattaba hannu kan yarjejeniyar samar da tsaro

Published: 10th, December 2025 GMT

Gwamnatin Tarayyar Najeriya da Masarautar Saudiyya sun sanya hannu kan wata sabuwar yarjejeniya domin ƙarfafa dangantakar tsaro da haɗin gwiwar soja tsakanin ƙasashen biyu.

A wata sanarwa da mataimaki na musamman ga Karamin Ministan Tsaro, Bello Matawalle kan yaɗa labarai Ahmed Dan Wudil ya fitar, ta bayyana cewa yarjejeniyar za ta shafi muhimman fannoni kamar musayar bayanan leƙen asiri, horas da sojoji, haɗin gwiwa a harkar samar da kayan yaki da kuma gudanar da ayyukan tsaro tare.

Zanga-zanga ta ɓarke kan zargin sojoji da kashe mata a Adamawa ’Yan jaridar Daily Trust da Trust TV sun lashe kyautar binciken ƙwaƙwaf ta Wole Soyinka ta bana

Minista Matawalle ne ya sanya hannu a madadin Najeriya, yayin da Dakta Khaleed H. Al-Biyari ya sanya hannu a madadin Gwamnatin Masarautar Saudiyya.

Ministar ya bayyana cewa, wannan ci gaban babbar dama ce da za ta ƙara ƙarfafa dangantaka tsakanin ƙasashen biyu da kuma taimakawa wajen fuskantar ƙalubalen tsaro da Najeriya ke fuskanta a halin yanzu.

Ya ce, ma’aikatar tsaron Najeriya tana maraba da wannan ci gaba, tare da fatan hakan zai taimaka wajen kawo ƙarshen matsalolin tsaro da ake fama da su a sassa daban-daban na ƙasar.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Bello Matawalle Masarautar Saudiyya

এছাড়াও পড়ুন:

Uwargidan Gwamnan Jihar Zamfara Ta Taya Oluremi Tinubu Murnar Nadin Sarauta a Ile-Ife

Daga Aminu Dalhatu

Uwargidar Gwamnan Jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal, ta taya Uwargidar Shugaban Kasa, Sanata Oluremi Tinubu, murna bisa nadin ta a matsayin Yeye Asiwaju Gbogbo Ile Oodua a Ile-Ife na  Jihar Osun.

Nadin ya kasance wani bangare na bukukuwan cikar shekaru 10 na Mai Martaba Ooni Adeyeye Enitan Ogunwusi Ojaja II akan karagar mulki na Ooni Ife, wanda ya jawo sarakunan gargajiya, manyan jami’an gwamnati da fitattun mutane daga sassan kasar nan.

A wata sanarwa da sakatariyar yada Labarai ta Uwargidar Gwamnan, Rabi Yusuf, ta fitar, ta bayyana karramawar da aka yi wa Sanata Oluremi a matsayin abin yabawa, inda ta ce karramawar ta yi daidai da jajircewarta wajen ci gaban kasa, tallafawa mata, da kuma gudummawarta wajen karfafa iyalai da al’umma ta hanyar aikace-aikacen jin kai da manufofin raya al’umma.

Ta kuma yaba wa Ooni na Ife bisa zabar Sanata Oluremi Tinubu domin wannan girmamawa, tana mai cewa wannan zabe ya nuna irin jagoranci, tasiri da dogon lokacin da ta shafe tana hidima ga kasa.

A cewar Hajiya Huriyya, wannan zabe ya nuna rawar da masarautu ke takawa wajen gane karrama wadanda suka yi wa al’umma  hidima.

Bikin ya nuna al’adun Yarbawa da kuma muhimmancin gudunmawar da masarautu ke bayarwa wajen gina hadin kan kasa.

Manyan shugabannin gargajiya da suka halarci bikin sun hada da Sarkin Musulmi, Olu na Warri, da Soun na Ogbomoso, da sauransu, wadanda suka hadu domin bikin cikar Ooni shekaru 10 a kan karaga da kuma nadin Sanata Oluremi Tinubu.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Uwargidan Gwamnan Jihar Zamfara Ta Taya Oluremi Tinubu Murnar Nadin Sarauta a Ile-Ife
  • DAGA LARABA: Ko Ziyarar Tawagar Amurka Za Ta Kawo Karshen Matsalar Tsaro A Najeriya?
  • Iya sojojin da ke tsaron Seyi Tinubu sun isa su samar da tsaro a Benin – Soyinka
  • Iya sojojin da ke tsaron Seyi Tinubu sun isa su samar da tsaro a Jamhuriyar Benin – Soyinka
  • Matsalar rashin tsaro ce ta sa na yi waqar “Arewa”-SKD Arewa
  • Matsalar Tsaro: Tinubu Ya Yi Ganawar Sirri da Gwamnonin Jihohi Shidda
  • Najeriya: Gwamnatin Tarayya Ta Bada Sanarwan Kubutar Da Yan Makaranta 100 Da Aka Sace
  • Rashin Tsaro: Gwamnatin Tarayya ta gaza — Kwankwaso
  • NAJERIYA A YAU: Kudaden Da Samar Da ‘Yansandan Jihohi Zai Lashe