Yadda za ka dawo da kuɗinka da ka yi kuskuren turawa wa wani
Published: 20th, September 2025 GMT
Kimiyyar sadarwa ta kawo sauƙin rayuwa a harkokin kasuwanci da mu’amalar kuɗi ta banki. Yawaitar amfani da wayar hannu wajen yin hada-hadar banki a Nijeriya ya sa mutane da dama ke tura kuɗi cikin sauƙi.
A shekarar 2024 kaɗai, rahoton Hukumar Biyan Hada-hadar Banki ta Ƙasa (NIBSS) ya nuna cewa darajar kudin da aka tura ta hanyar waya ta kai Naira tiriliyan 41.
Sai dai kuma hakan na iya kawo matsala, musamman idan aka yi kuskure aika kuɗi zuwa wani asusu daban. Wannan na faruwa sosai, musamman idan aka rubuta lambar asusu ko sunan mai asusu ba daidai ba.
Shin me ya kamata mutum ya fara yi idan ya yi kuskuren aika kuɗi zuwa wani asusu daban?
Takari: Rayuwar baƙin haure ’yan Najeriya mazauna Saudiyya Laifukan kisan ƙare dangin da Isara’ila ta yi a Gaza — Rahoton MƊDAbu na farko shi ne gaggauta sanar da bankinka sannan ka kai rahoto ga bankin wanda ya samu kudin.
Dole ne ka rubuta ƙorafi a hukumance, ka bayar da cikakken bayanin mu’amalar, sannan ka haɗa da shaidu kamar rasir, bank statement, ko sakon alat na fitar kuɗin. Wannan zai tabbatar wa bankin cewa ba ka shirya aika kuɗin ba, kuskure ne kawai.
Da zarar banki ya samu rahoton irin wannan kuskure abin da zai fara yi shi ne sanya ‘PND’ a kan asusun wanda ya samu kuɗin. Wannan na nufin ba zai iya cire kuɗi ta yadda abin da zai rage bai kai abin aka yi kuskuren tura masa ba, har sai an kammala bincike.
Idan wanda ya samu kuɗin ya amince da cewa kuɗin ba nasa ba ne, banki zai mayar da kuɗin kai tsaye. Amma idan ya ƙi amincewa, banki ba zai iya ƙwace kudin ba sai da umarnin kotu.
Wani hanzari ba gudu ba, yana da kyau a sani cewa dokokin kare sirri sun haramta wa banki ya bayar da bayanan tuntuɓa na mai asusun kamar lambar waya ko adireshin email.
Banki kawai zai iya tuntuɓar sa domin tabbatar da gaskiyar rahoton da aka kai. Don haka, ka bi matakan doka maimakon bin ta bayan fage.
Idan mai asusun da ya samu kuɗin bai yarda a dawo da su ba, me za a yi?
Idan haka ta faru, dole sai ka nemi lauya wanda zai taimaka maka ka shigar da ƙara a kotu. Lauyan zai rubuta ‘application’ tare da affidavit (rantsuwar gaskiya) da ke dauke da cikakken bayani da shaidu – rasit, takardar bayanan kuɗi a banki da kuma takardar ƙorafin da ka rubuta wa banki.
Kotu za ta duba shaidar da ka gabatar sannan ta yanke hukunci ko za a dawo da kudin.
Shin wace kotu ake kai irin wannan kara?
Ya danganta da inda aka yi mu’amalar da kuma adadin kuɗin da aka tura.
Idan a Legas ne, idan kuɗin bai kai Naira miliyan 10 ba, ana iya kai ƙara a kotun Magistrate. Idan ya fi haka kuma, sai a Babba Kotu (wato High Court).
A Abuja kuma, idan kuɗin bai kai Naira miliyan 5 ba, ana iya kai ƙara a kotun yanki. Idan ya fi kuma, sai a ‘High Court.’
A dukkan wuraren, idan mutum ya so, zai iya shigar da ƙara kai tsaye a High Court, musamman idan kuɗin na da yawa.
Me mutum zai nuna a matsayin shaida kafin kotu ta amince da mayar da kudin? Amsa ita ce za ka nuna abubuwa masu muhimmanci guda hudu:
1. Shaidar cewa kuɗin ya fita daga asusunka (ta bank statement ko debit alat).
2. Bayani cewa ba ka da wata mu’amala ko yarjejeniya da wanda ya samu kuɗin.
3. Cikakken bayanin asusun wanda ya samu kuɗin (banki, suna, lambar asusu).
4. Hujja cewa ka kai rahoto ga banki kafin ka garzaya kotu.
Idan ba ka kawo waɗannan shaidun ba, kotu ba za ta bayar da umarnin dawo da kudin ba.
Shin me zai faru bayan kotu ta bayar da umarnin dawo da kuɗi?
Da zarar kotu ta yanke hukunci, dole ne ka kai takardar hukuncin ga bankin wanda ya samu kuɗin. Banki zai dauki matakin mayar da kudin cikin gaggawa. Idan bankin ya ƙi aiwatarwa, hakan za a ɗauke shi a matsayin saɓa wa umarnin kotu, wanda zai iya jawo wa bankin hukunci mai tsanani.
Sai dai kuma akwai abin da zai iya jawo tsaiko wajen dawo da kuɗin bayan umarnin kotun. Kamar idan ba a kai wa banki ko mai asusun da ya samu kuɗin umarni ko hukuncin kotu ba.
Idan ba a san adireshin wanda ya samu kuɗin ba, kotu na iya bayar da umarnin a isar da saƙon gare shi ta hanyar bankinsa.
Matakan kariyaShawararmu ga mutane domin kauce wa irin wannan kuskuren ita ce:
1. A duba sau biyu kafin a aika kuɗi ta waya ko ATM.
2. A tabbatar da sunan mai asusu ya yi daidai da wanda ake son aika wa.
3. A kiyaye da saurin aika kuɗi ba tare da dubawa ba.
4. A adana shaidun mu’amala (saƙon alat, rasit, bayanin mau’amalar banki).
A takaice, idan mutum ya yi kuskuren aika kudi cikin wani asusu daban, kada ya yi shiru ko ya yi sakaci da lamarin.
Matakin farko shi ne gaggauta sanar da banki, sannan a nemi umarnin kotu idan wanda ya samu kuɗin ya ki mayar da su.
Duk da cewa tsarin yana ɗan wahala, shari’a na bayar da dama domin ƙwato haƙƙin mai asusun da ya yi kuskuren.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: takarda wanda ya samu kuɗin da ya samu kuɗin umarnin kotu
এছাড়াও পড়ুন:
’Yan bindiga sun sako ma’auratan da suka sace a Katsina bayan biyan N50m
Wani ɗan kasuwa a Jihar Katsina mai suna Anas Ahmadu da matarsa, Halimatu wadda ke ɗauke da juna biyu, da kuma ’yarsu mai shekaru biyu, sun kuɓuta daga hannun ’yan bindiga, bayan sun shafe kwanaki 21 a hannunsu.
An sako su ne a daren ranar Laraba bayan biyan kuɗin fansa Naira miliyan 50, kamar yadda wani ɗan uwansu ya bayyana wa Aminiya.
Gobara ta kashe manyan jami’an hukumar FIRS 4 a Legas NAJERIYA A YAU: Wadanne Kalubale Gwamna Fubara Zai Fuskanta Bayan Dawowa Mulkin Ribas?“Alhamdulillah! Anas, Halimatu da ’yarsu sun kuɓuta. Yanzu haka suna kan hanyarsu ta zuwa gida, amma sai da aka biya ’yan bindigar kuɗin fansa Naira miliyan 50,” in ji shi.
An sace su ne a ranar 26 ga watan Agusta, 2025 a gidansu da ke Filin Canada Quarters, a Jihar Katsina.
Da farko, mahafan sun nemi Naira miliyan 600, daga baya suka rage kuɗin zuwa miliyan 100, sannan daga ƙarshe suka amince aka biya su miliyan 50.
Saboda dalilan tsaro, ’yan uwansu ba su bayyana inda aka sako su ba.