Matsalar Tsaro: Tinubu Ya Yi Ganawar Sirri da Gwamnonin Jihohi Shidda
Published: 8th, December 2025 GMT
Daga Bello Wakili
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi ganawar sirri da gwamnonin jihohi shidda daga sassan ƙasar a ci gaba da tattaunawar da ake yi domin ƙarfafa batun tsaro a ƙasa.
Gwamnonin da suka halarci taron sun hada da Gwamna Monday Okpebholo na jihar Edo, Umar Namadi na Jigawa, Nasir Idris na Kebbi, Ahmed Ododo na Kogi, Lucky Aiyedatiwa na Ondo, da Ahmed Aliyu na jihar Sokoto.
Taron, wanda ya ɗauki kusan mintuna 40, ya mayar da hankali ne kan muhimman matsalolin tsaro da ke shafar jihohinsu, duk da cewa ba a bayyana cikakkun bayanai ba.
Wakilin Rediyon Najeriya da ke fadar shugaban kasa ya ruwaito cewa wannan zaman na daga cikin kokarin shugaban kasa na ƙara haɗin kai da jihohi wajen magance matsalolin tsaro.
Wannan cigaban ya biyo bayan nasarar da Gwamnatin Tarayya ta samu na kubutar da dalibai 100 da aka yi garkuwa da su a Jihar Neja, baya ga wanda aka yi a Jihar Kebbi.
Ci gaba da irin waɗannan tattaunawa na shugaban kasa na nuna jajircewar gwamnati wajen tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali a fadin ƙasar.
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Gwamnoni Taron Sirri
এছাড়াও পড়ুন:
Nakiya ta hallaka yara 4 a Borno
Wata nakiya da ta fashe a garin Banki, da ke Ƙaramar Hukumar Bama, a Jihar Borno, ta yi sanadin mutuwar yara huɗu tare da jikkata wani yaro guda ɗaya.
Rundunar ’yan sandan jihar, ta tabbatar da aukuwar lamarin a ranar Juma’a.
Kwastam ta kama jirgin ruwan Brazil ɗauke da hodar iblis a Legas Ranar Sabuwar Shekara za mu rufe duk na’urar POS mara rajista —GwamnatiLamarin ya faru da misalin ƙarfe 12:40 na rana a bayan tashar motar Banki da ke yankin Wajari.
Wani mazaunin garin, Babagana Mohammed, ya kai rahoton fashewar nakiyar da misalin ƙarfe 1 na rana, wanda hakan ya sa aka tura jami’an tsaro zuwa yankin.
DPO na Banki tare da ƙwararrun sashen cire bam, sun killace wajen domin kare jama’a da kuma fara bincike.
An gano cewa wani yaro mai shekaru 12, Mustapha Tijja, ya samu munanan rauni, kuma an kai shi asibitin FHI 360 da ke Banki, inda ake kula da shi.
Rahotanni sun nuna cewa yaron da ya tsira da ransa, yana tare da abokansa huɗu a bayan tashar motar.
Sun samu wani abun fashewa da ake zargin ajiye shi aka yi a wajen, wanda ya fashe yayin da suke wasa da shi.
Yaran da suka rasu sun haɗa da Awana Mustapha mai shekaru 15, Malum Modu mai shekaru 14, Lawan Ibrahim mai shekaru 12 da Modu Abacha mai shekaru 12
Rundunar ’yan sandan jihar, ta ce al’amura sun daidaita a yankin, yayin da a gefe guda ta ke ci gaba da bincike.
Kwamishinan ’yan sandan Jihar, CP Naziru Abdulmajid, ya bayyana alhininsa kan faruwar lamarin, tare da bayyana cewa rundunar tana gudanar da bincike.
Ya gargaɗi jama’a cewa: “A guji taɓa ko wasa da duk wani abu da ba a saba gani ba. Duk abun da ake zargi, a gaggauta sanar da jami’an tsaro.”
Rundunar ta bayyana lambobin kiran gaggawa da jama’a za su yi amfani da su don kai rahoto: 0806 807 5581 da 0802 347 3293.
Kakakin rundunar, ASP Nahum Kenneth Daso, ya ce rundunar za ta ci gaba da aiki tuƙuru wajen tabbatar da tsaro da hana irin waɗannan abubuwan faruwa a gaba.