2025-12-03@11:49:18 GMT
إجمالي نتائج البحث: 50
«na Tarayyar»:
Wata sabuwar badakala ta sake bata sunan kungiyar Tarayyar Turai, inda ‘yan sanda suka farmawa gidan toshuwar shugaban kula da manufofin harkokin wajen na kungiyar Federica Mogherini, tare da tsare ta a ranar Talata, a Belgium. Mogherini wacce ta yi aiki a mukamin tun daga 2014 zuwa 2019, Ita da wasu abokan aikinta biyu ana binciken su kan yadda aka yi amfani da kudaden Tarayyar Turai ba bisa ka’ida ba, cin hanci da rashawa. Federica Mogherini, jami’ar diflomasiyya ‘yar Italiya mai shekaru 52, ana tsare da ita tare da Stefano Sannino, babban jami’i a Hukumar da kuma mataimakin darakta na Kwalejin Turai. An kama su, su ukun a wani bangare na binciken da Ofishin Mai Gabatar da Kara na Tarayyar...
Gammayar ministocin harokin wajen kungiyar tarayyar Turai sun fitar da wata sanarwa da aciki suka soki hare haren da yahudawa yan share wuri zauna suke kai wa falasdinawa a gabar yammacin kogin Jodan da isra’ila ta mamaye kuma yake kara ci gaba fiye da kowanne lokaci a baya, Sanarwar ta fito ne daga minsitocin kasashen birtaniya, jamus , faransa da kuma italiya inda manyan jami’an diplomsiyarsu suka bayyana hare-haren a matsayin mataki ne na tada fitina da kuma ta’addanci. Haka zalika sun yi kira ga fira ministan isra’ila Benjamin na tanyaho da yayi aiki da nauyin da ya rataya a wuyansa karakshin dokokin kasa da kasa, kuma ya kiyaye hakkin falasdinwa dake zaune a bangarorin da aka mamaye. Daga karshe...
Shugaban Hukumar Tarayyar Afirka, Mahmoud Ali Youssouf, ya yi Allah wadai da juyin mulkin da sojoji suka yi a Guinea-Bissau a ranar Alhamis, inda ya yi kira da a gaggauta sakin hambararren shugaban kasar Umaro Sissoco Embaló da sauran jami’an da ake tsare da su. A cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar, ta sake nanata cewa kungiyar Tarayyar Afirka ba za ta amince da duk wani sauyi na gwamnati da ya saba wa kundin tsarin mulkin kasar ba. Ya jaddada muhimmancin mutunta tsarin zabe da ake gudanarwa da kuma tabbatar da tsarin mulkin kasar, kamar yadda hukumar zabe ta kasar ta tanada. Youssouf ya yi kira ga dukkan bangarorin da su yi taka tsantsan don hana ci gaba da...
Daga Khadijah Aliyu Gwamnatin Jihar Kano ta kaddamar da Kwamitin Jagorancin Shirin Ilimi da Ƙarfafa Matasa a Arewa maso Yammacin Najeriya (EYEPINN) wanda kungiyar Tarayyar Turai ke daukar nauyinsa domin fadada damar samun ingantaccen ilimi da kuma karfafa gwiwar matasa a yankin. An gudanar da bikin kaddamarwar ne a Kano, karkashin jagorancin Kwamishinan Ilimi na Jihar, Dakta Ali Haruna Abubakar Makoda. Yayin jawabinsa, Dakta Makoda ya bayyana shirin EYEPINN a matsayin “Alƙawari mai Manufa”, yana mai cewa manufar shirin ita ce cike gibi a fannin ilimi, karfafa haɗin kai, da kuma baiwa matasa kwarewar da ta dace domin rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a jihar. Ya ce sabon kwamitin da aka kaddamar zai yi jagoranci kan dabaru,...
Kungiyar tarayyar Afirka ta bayyana matukar damuwarta akan yadda al’amurra suke tabarbarewa a cikin kasar Mali, tana mai yin Ishara da yadda ‘yan ta’adda su ka killace iyakokin kasar da hana shigar da muhimman kayan bukatun rayuwa na yau da kullum. Tarayyar Afirka ta kuma yi tir da yadda ake kashe farafen hula a kasar ta Mali da hakan yake haddasa rashin zaman lafiya da tsaro. Bugu da kari, tarayyar Afirkan ta nuna cikakken goyon bayanta ga al’umma da kuma gwamnatin kasar Mali da iyalan wadanda aka kashe. Kungiyar ta Afirka ta kuma nuna cewa a shirye ta bayar da dukkanin taimakon da ake bukatuwa da shi a kasar ta Mali domin samun zaman lafiya. Kungiyar “Jama’atu Nusratul-Islam Wal Muslimin”...
Tarayyar Afirka Ta Yi Kiran Da A Girmama ‘Yancin Kai Na Najeriya Da Rashin Tsoma Baki A Harkokin Gidanta
Tarayyar Afirka ta yi kira da a girmama ‘yancin kai na tarayyar Najeriya kuma ta yi watsi da barazanar Trump Kwamitin Tarayyar Afirka ya bayyana damuwarsa game da kalaman da Amurka ta yi kwanan nan game da zargin gwamnatin Najeriya da hannu a kisan Kiristoci da kuma nuna alamun yiwuwar shiga tsakani na soja a karkashin hujjar “kare ‘yancin addini.” A cikin wata sanarwa a hukumance, wacce Al Jazeera ta samu kwafinta, Kwamitin ya jaddada jajircewarsa ga ka’idojin ‘yancin kai, rashin tsoma baki, ‘yancin addini, da kuma bin doka, kamar yadda aka tsara a cikin Dokar Tsarin Mulki ta Tarayyar Afirka da sauran kayan aikin da suka shafi hakan. Sanarwar ta tabbatar da cewa: Tarayyar Najeriya kasa ce mai muhimmanci...
Tarayyar turai ta bayyana cewa ma’aikatan Agaji ba za su iya isha cikin garin Al-fahar ba,kuma birnin ya zama tamkar makabarta. Tarayyar turai din ta bakin mai Magana da yawunta Eva Herneserova ta kuma ce; Sudan ta zama daya daga cikin kasashen da gudanar da ayyukan agaji ya tsananta a duniya,kuma har yanzu da akwai fararen hula da aka killace su adaidai lokacin da ake ci gaba da kai wa asibitoci hare-hare. Eva Herneserova ta kuma ce; Babu sauki ko kadan a kokarin shiga cikin birnin domin isar da kayan agaji. Ma Magana da yawun kungiyar tarayyar turai din ta kuma yi gagradi akan cewa bai kamata a rika amfani da yunwa da kuma kisan kiyashi a matsayin makamin yaki...
Tawagar masu sa ido ta Tarayyar Afirka ta sanar a ranar Laraba cewa zaɓen Tanzania “bai cika ƙa’idodin dimokraɗiyya ba,” tana mai tsokaci kan zaɓen da aka yi jayayya a kansa wanda ya haifar da zanga-zanga mai tsanani kwanan nan. An ayyana Shugaba Samia Suluhu Hassan a matsayin wadda ta lashe zaɓen da gagarumin rinjaye a zaɓen da aka gudanar a ranar 29 ga Oktoba, amma ‘yan adawa sun zargi gwamnati da yin magudi a zaɓen, kuma zanga-zangar ta ɓarke bayan da aka soke manyan abokan hamayyarta. Tawagar ta ƙara da cewa “a wannan matakin farko, tawagar ta kammala da cewa babban zaɓen 2025 a Tanzania bai yi daidai da ƙa’idodin Tarayyar Afirka da tsarin ƙa’idoji na kasa da kasa...
Memba a Majalisar Tarayyar Turai ya bayyana cewa: Zaman lafiya na gaske yana buƙatar ɗaukar matakin hukunta Isra’ila Dan Majalisar Dokokin Turai ta Ireland (MEP) Barry Andrews ya jaddada cewa: Daukan matakin hukunta haramtacciyar kasar Isra’ila kan munanan laifukan da ta aikata a Zirin Gaza ita ce hanya daya tilo da za a cimma zaman lafiya na gaskiya da dorewa, yana mai kira ga Tarayyar Turai da ta ci gaba da zabar sanya takunkumi kan Isra’ila. Jawabin Andrews ya zo ne a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Anadolu na kasar Turkiyya, wanda ya yi daidai da taron Tarayyar Turai da aka gudanar a Brussels ranar Alhamis da ta gabata, wanda ya tattauna makomar dangantakar Tarayyar Turai da Isra’ila...
Kamfanin Gine-Gine Na CCECC Ya Fara Gina Wani Titin Mota Da Zai Rage Cunkoso A Birnin Abuja Na Tarayyar Najeriya
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Masanin Ilimin Physics Chen Ning Yang Ya Rasu Yana Da Shekaru 103 October 18, 2025 Daga Birnin Sin Kasar Sin Ta Gargadi Amurka Game Da Yunkurin Samarwa Yankin Taiwan Makamai October 18, 2025 Daga Birnin Sin Mataimakin Firaministan Sin Ya Zanta Da Sakataren Baitul-mali Da Wakilin Cinikayyar Amurka October 18, 2025
Bayan juyin mulkin da aka yiwa Andry Rajolina a kasar Madagaska kungiyar tarayyar Afirka ta bada sanarwan jingine kasar daga zama mama a cikinta har zuwa abinda hali yayi. \ Tashar talabijin ta Almayadin ta nakalto majiyar kungiyar AU na bada wannan sanarwan, kwana guda bayan da sojoji suka yi juyin mulki wa shugaba Andria Rajolina juyin mulki a tsibirin Madagaska. Sabon shugaban kasar Madagaska Micheil Rondri Yorinina ya bayyana cewa zai yi rantsuwar kama aiki a matsayin shugaban kasar zuwa lokacinda kasar zata koma cikin hayyacinta. Sannan a san abinda za’a yi. Mutanen kasar Madagaska dai sun dade suna zanga-zangar bukatar Rajolina ya sauka tunda ya kasa kyautata rayuwar mutanen kasar. Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login...
’Yan Majalisar Tarayya uku daga Jihar Kaduna sun sauya sheka daga Jam’iyyar PDP zuwa APC. Shugaban Majalisar Wakilai Abbas Tajuddeen ya sanar a ranar Talata cewa masu sauya shekar sun hada da Honorabul Abdulkarim Hussain Mohammed, Aliyu Mustapha Abdullahi da kuma Sadiq Ango Abdullahi. Tajuddeen, wanda shi ma dan asalin Jihar Kaduna ne, ya sanar da cewa, Gwamnan jihar, Uba Sani ya halarci zaman majalisar domin shaida dawowar ’yan majalisar zuwa APC daga PDP. Masu sauya shekar sun bayyana cewa rikin cikin gida da rabuwar kai da suka dabaibaye tsohuwar jam’iyyarsu ta PDP ce ta sa suka yanke shawarar sauya sheka. Shugaban Hukumar Zaɓen Yobe Jihar Yobe ya rasu Faɗa ya ɓarke tsakanin Palasɗinawa da Hamas bayan sulhu da Isra’ila...
Ɗan Majalisar Tarayya mai Wakiltar Sabon Gari Daga Jihar Kaduna, Sadiq Ango Abdullahi, ya fice daga Jam’iyyarsa ta PDP. Honorabul Abdullahi wanda shi ne Mataimakin Shugaban Kwamishinan Hukumar Kula da Hanyoyi (FERMA) ya alaƙanta ficewarsa da rikicin cikin gida da rabuwar kai da ya ki ci ya ƙi cinyewa a jam’iyyar. A ranar Litinin ya aike da wasikar ta ficewa ga Shugaban PDP na Mazabar Hanwa da ke Ƙaramar Hukumar Sabon Gari, yana mai cewa rikicin ya hana shi taɓukawa matsayin zaɓaɓɓen ɗan Majalisar Tarayya. Ya cewa saboda haka yana dacewar ficewarsa daga jam’iyyar ba tare da la’akari da siyasa ba, domin amfanin ɗauƙacin al’ummar mazabar. Majalisar Shura ta fara ganawar sirri da Malam Triumph Zaben Kamaru: Issa Tchiroma Bakary...
Bayan tattaunawa ta wayar tarho da ministan harkokin wajen kasar iran Abbas Araqchi yayi da babbar jami’ar diplomasiyar kungiyar tarayyar turai kaja kallas ta maimaita bukatar kungiyar na sa ido kan tashohin nukiliyar iran, kana tayi gargadin cewa kofar diplomasiya tana gab da rufewa, matsayin da iran taki amincewa da shi kuma ta bayyana shi a matsayin mara inganci, Iran a matsayinta na member a NPT ta yi aiki da nauyin da ya rataya akanta, karkashin yarjejeniyar JCPOA yayin da Iran ke jiran kungiyar tarayyar turai ta yi aiki da abin da ya hau kanta kuma ta cire takunkumi, amma hakan bai samu ba, kasashen turai da hadin bakin Amurka suna barazanar sake dawo da takunkumai don matsin lamba ga...
Hukumar tarayyar turai ta gabatar da shawara ga kasashe mambobi da su jingine aiki da yarjejeniyar da aka kulla ta kasuwanci da HKI saboda yakin Gaza. A yau Laraba ne dai hukumar tarayyar turai din ta bijiro da wannan shawarar ga kasashen mambobi,sai dai kuma babu cikakken goyon baya daga mafi yawancin kasashen kungiyar da zai sa a yi aiki da shi. Ita kuwa jami’ar harkokin wajen ta tarayyar turai din Kaya Kalas ta gabatar da shawarar a kakaba takunkumi akan wasu ministoci biyu na HKI da kuma ‘yan share wuri zauna da suke amfani da akrfi akan Falasdinawa. Da akwai kungiyoyin kare hakkin bil’adama guda 84 da suke yin kira a yanke duk wata alaka ta kasuwanci da zuba...
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya sanar da yiwuwar sake yin wani taro da babbar jami’ar kungiyar tarayyar Turai kan harkokin waje Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya sanar da yiwuwar sake ganawa da babbar jami’ar harkokin wajen kungiyar tarayyar turai Kaya Kalas. A cikin wata sanarwa da ya fitar a yammacin jiya Juma’a, Araqchi ya ce, “Akwai yiwuwar sake yin wani taro da jami’ar harkokin wajen kungiyar tarayyar Turai, kuma hakan ya dogara ne da shawarar Turai. Dangane da tattaunawar da aka yi a birnin Alkahira, ya ce, wadannan shawarwarin masu muhimmanci ne sosai, da kuma shawarwarin da ake yi a bayan yaki, inda hotunan shahidai ke wucewa a kan idonun mutane daya bayan daya, ba tattaunawa...
Kasar Sin Na Fatan EU Za Ta Yi Aiki Da Ita Bisa Alkibla Guda Da Tsara Hadin Gwiwa Na Shekaru 50 Masu Zuwa
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun, ya bayyana a yayin gudanar da taron manema labaru na yau da kullum da aka yi yau Litinin cewa, bana shekara ce ta cika shekaru 50 da kulla huldar diflomasiyya tsakanin Sin da Tarayyar Turai EU. Kuma taron kolin kasar Sin da EU karo na 25 na karatowa. Kasar ta Sin tana fatan kungiyar EU za ta yi aiki tare da ita bisa alkibla guda, da cimma matsaya, da kawar da bambance-bambance, da kuma tsara shirin hadin gwiwa tare cikin shekaru 50 masu zuwa. Bayan cimma yarjejeniya tsakanin Sin da kungiyar EU, shugaban majalisar Tarayyar Turai António Costa da shugabar hukumar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen, za su...
Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da lafta wa Tarayyar Turai da kuma Mexico harajin kashi 30 kan kayayyakin da ake shiga da su da su ƙasar daga ranar 1 ga Agusta. Bayanai sun ce ana ganin wannan matakin zai iya haddasa rikici mai tsanani tsakanin Amurka da biyu daga cikin manyan abokan kasuwancinta. An sanya dokar hana fita a Adamawa Tinubu ya dawo Najeriya bayan ziyarar aiki a Saint Lucia da Brazil Trump ya yi cikakken bayani kan wadannan haraje-harejen ne a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, yana mai cewa matuƙar ba a cimma wata tartibiyar matsaya ba, ba shakka zai ƙara lafta musu harajin. Wannan na daga cikin jerin sabbin haraje-haraje da...
Kazem Sajjadpour Ya ce: Iraniyawa Suna Daukan Tarayyar Turai Ma Goyon Bayan Harin Zaluncin Isra’ila Kansu
Mai ba da shawara ga ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Tarayyar Turai ta zama abokiyar gudanar da ta’addancin ‘yan sahayoniyya kan kasar Iran Kazem Sajjadpour, mai baiwa ministan harkokin wajen kasar Iran shawara ya bayyana dabi’ar Turai a lokacin da yahudawan sahayoniyya suke kai wa Iran hari a matsayin abin da ba za a amince da shi ba, saboda matakin da suka dauka na goyon bayan ‘yan sahayoniyya lamarin da mayar da ita mai hannu wajen kai hare-haren. Sajjadpour ya ce: Turai ba ta da wani matsayi a manufofin ketare na Amurka kuma Donald Trump bai ma ambaci Turai ba a cikin wannan tsari. A wani taron karawa juna sani na yanar gizo da aka gudanar a...
Kasar China ta maida martani ga takunkuman tattalin arziki na wasu kayakin kiwon lafiya wadanda tarayyar Turai da dorta maya. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto majiyar kasar ta Chaina na fadar haka ta kuma kara da cewa gwargwadon takunkuman da suka dorawa kasar gwargwadon maida martanin kasar ta China. Labarin ya kara da cewa wannan haramcin ba zai shafi kamfanonin turai da suke samar da kayakin aikin kiwo lafiya a cikin kasar China ba. A cikin watan Yunin da ya gabata ne kungiyarn EU ta hana gwamnatocin kasashe kungiyar sayan kayakin aikin likita fiye da dalar Amurka miliyon 5 tare da bukatar kasar china ta daina nuna bambanci a cikin ahrkokin kasuwanci da ke tsakaninsu.
Minstan harkokin wajen Iran Abbas Arakci ya mayar da martani da kakkausar murya akan furucin jami’ar diplomasiyya ta tarayyar turai Kaya Jallas na cewa Iran ta dakatar da shirinta na makamashin Nukiliya, yana mai cewa; Jallas ta jahilci abinda dokokin NPT su ka kunsa. Abbas Arakci ya ce; Idan manufar ganawa da kwamitin hadin gwiwa akan yarjeniyar Nukilar iran shi ne kawo karshen Shirin makamashin Nukiliyar Iran, to kuwa Jallas ta jahilci abinda yake kunshe a cikin yarjejeniyar hana yaduwar makaman Nukiliya. Ita dai babbar jami’ar harkokin wajen tarayyar turai Jallas ta rubuta sako a shafinta na X cewa; Ya zama wajibi a bude tattaunawa da sauri da Iran akan yadda za ta kawo karshen shirinta na makamashin Nukiliya, kuma...
Wasu jami’an diplomasiyyar turai sun yi wa gwamnatin Benjamin Netanyahu da cewa za ta fuskanci Karin matsin lamba idan har ba ta sauya halayyarta akan Gaza ba. Jaridar “Washington Post” ta Amurka ta ambato jami’an diplomasiyyar turai suna cewa; sabon tsarin da ake yin aiki da shi na raba kayan agaji a Gaza, ya juya ya zama harigitsi kuma ana bude wuta akan mutane da hakan ya yi sanadiyyar jikkatar Falasdinawa da dama.” Har ila yau jami’an diplomasiyyar na turai sun ce, ko kadan ba su da aniyar bayar da kayan agajinsu ga masu tafiyar da tsarin da su ne Isra’ila da Amurka.” Bugu da kari, majiyar diplomasiyyar ta tarayyar turai ta ci gaba da cewa; Hotunan masu ban tsoro...
Bayan sabon farmakin da Isra’ila ta kai a zirin Gaza, kasashen Yamma na kokarin kara matsin lamba kan Isra’ila, wacce ta kauda kai kan kiraye kirayen da duniya ke yi na ta dakatar da yakin a Gaza. Kungiyar ta EU, ta kara mastin lamba ta hanyar sake nazari kan yarjejeniyarta da Isra’ila ta tsawon shekaru 25 dake a tsakaninsu. Tunda farko dama kasashen kasashen Canada-Faransa da Ingila sun sanar da yin Allah wadai da farmakin kasa na soja na sojojin Isra’ila a Gaza. Baya ga hakan kuma Birtaniyya a ranar Talata ta sanar da kawo karshen yarjejeniyar ciniki cikin ‘yanci da Isra’ila. Ita ma kiasar Sweden, ta yi kira da a kakaba takunkumi ga membobin gwamnatin Isra’ila. Bayanai sun ce...
Bayan sanarwar ba-zata da Amurka ta yi a makon da ya gabata, Tarayyar Turai ta ce za ta dage takunkumin da ta kakaba wa Syria. Ministocin harkokin waje da ke taro a Brussels ne suka yanke shawarar dage dukkan takunkumin tattalin arzikin kan Siriya. “Muna son taimakawa al’ummar Siriya wajen sake gina sabuwar Siriya,” in ji jami’ar kula da harkokin wajen Tarayyar Turai Kaja Kalas. Tarayyar Turai ta kuma yi alkawarin bayar da Yuro biliyan biyu da rabi domin sake gina kasar. Matakin dage wannan takunkumin da aka kakabawa gwamnatin Bashar al-Assad tun daga shekara ta 2011, zai bada damar sakin kadarorin kasar da har yanzu ke daskare, sannan kuma zai baiwa hukumomin kasar damar neman zuba jarin da suke...
Yau Juma’a, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci bukukuwan cika shekaru 80 da cimma nasara a yakin kishin kasa na tsohuwar Tarayyar Soviet. An gudanar da faretin soja na ranar samun nasara, wanda ke ayyana cika shekaru 80 da samun nasara a yakin kishin kasa na Tarayyar Soviet ne a birnin Moscow. Shugabanni daga kasashe da hukumomin duniya sama da 20 ne aka gayyata domin halartar bukukuwan. (Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
An Yi Taron Musayar Al’adu Da Cudanyar Jama’a Na Bikin Cika Shekaru 80 Da Nasarar Yakin Da Sinawa Suka Yi Kan Zaluncin Japan Da Yakin Ceton Kasa Na Tsohuwar Tarayyar Soviet
An gudanar da taron musayar al’adu da cudanyar al’umma na murnar cika shekaru 80 da samun nasarar yakin turjiya na jama’ar kasar Sin a kan zaluncin kasar Japan da kuma kazamin yakin ceton kasa na tsohuwar tarayyar Soviet, wanda babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin (CMG) da kamfanin gidajen talabijin da rediyo na kasar Rasha suka shirya a birnin Moscow. An karanta wasikun taya murna daga shugaban kasar Sin Xi Jinping da na Rasha Vladimir Putin a wajen taron. A jawabinsa, babban darektan CMG, Shen Haixiong, ya bayyana cewa, yayin da bikin shekarar al’adun Sin da Rasha ya kankama, bari mu dauki ruhin sakon wasiku na taya murna a matsayin jagora, karkashin jagorancin shugabannin kasashen biyu....
Jami’ar siyasar waje ta tarayyar turai Kaja Kallas ta bayyana cikakken goyon baya ga warware batun makamashin Nukiliyar Iran ta hanyar diplomasiyya. Jami’ar ta wallafa a shafinta na X cewa: Na tattauna da ministan harkokin wajen Iran Abbas Arakci domin tabbatar da goyon bayan kungiyar tarayyar turai akan aiki da hanyar diplomasiyya domin warware batun Nukiliyar Iran da kuma rage rikice-rikice a cikin wannan yankin.” Haka nan kuma Kallas ta jaddada abinda a baya tarayyar turai din ta rika riyawa da ba shi da tushe na cewa, Iran tana bai wa Rasha taimakon soja tana mai cewa: ” Na kuma yi kira ga Iran da ta dakatar da bai wa Rasha taimakon soja.” Iran dai ta sha yin watsi da...
Ƙungiyar Tarayyar Afirka (AU) ta janye takunkuman da ta ƙaƙaba wa Gabon bayan dakatar da ƙasar ta Tsakiyar Afirka saboda juyin mulkin da aka yi a watan Agustan 2023. Wani taro da aka yi na Kwamitin Zaman Lafiya da Tsaro kan sauyin siyasa a Gabon “ya yi nazari kan ayyukan tare da gano cewa sun yi nasara,” in ji shashen Siyasa da Zaman Lafiya da Tsaro na AU a shafin X a ranar Laraba. Dokta Bashir ya zama shugaban Majalisar Shari’ar Musulunci ta Nijeriya Dalilin da manyan ’yan siyasa ke barin NNPP — APC Sanarwar ta ce za a yi maraba da Gabon “ta dawo nan da nan, ta ci gaba da shiga ayyuka” a sakatariyar Tarayyar Afirka. An dakatar...
Kungiyar Tarayyar Afirka ta dage takunkumin da ta kakabawa kasar Gabon tare da maida ta a cikin cibiyoyinta. AU, ta sanar da hakan ne yayin taron kwamitin zaman lafiya da tsaro na kungiyar yau Laraba a Addis Ababa. Hakan dai ya karshen dakatarwar da aka yi wa kasar ta Gaban daga kungiyar, watanni 20 bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a watan Agustan 2023. Kwamitin zaman lafiya da tsaro na AU, ya yi la’akari da mika mulki da ya hambarar da Ali Bongo “gaba daya cikin nasara,” saboda haka ya yanke shawarar dage takunkumin nan take. ‘’Tsarin siyasar Gabon yana da ” gamsarwa” inji sanarwar kungiyar. Wannan matakin na AU ya zo ne kwanaki uku gabanin rantsar da Janar...
Kasashen kungiyar Tarayyar Turai sun amince da cewa kungiyar za ta kaddamar da matakan yaki da harajin da shugaban Amurka Donald Trump ya dora mata. Kungiyar mai kasashe mambobi 27 tana fuskantar kashi 25% na harajin shigo da kayayyaki kan karafa, aluminium, da motoci, da kuma karin harajin kashi 20% akan kusan duk wasu kayayyaki karkashin manufofin Trump. Domin mayar da martani, Tarayyar Turai za ta aiwatar da ayyuka, galibi an saita su a kashi 25%, kan nau’oin kayayyakin da ake shigo da su daga Amurka, wanda zai fara daga ranar Talata mai zuwa a matsayin martani na musamman ga harajin karafa na Amurka. Kungiyar har yanzu tana kimanta tsarinta na magance tasirin karin haraji. Kayayyakin na Amurka da tsarin...
Tarayyar Turai Ta Yi Maraba Da Tattaunawa Tsakanin IRAN da Amurka Kan Shirinta Na Makamashin Nukliya
Kungiyar tarayyar Turai ta yi maraba da tattaunawa tsakanin Amurka da JMI dangane da shirinta na makamashin Nukliya, tare da kara jaddada cewa hanyar diblomasiyya kadai ta rage don warware wannan matsalar. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa a halin yanzu dai kungiyar tarayyar ta Turai ta na ci gaba da takurawa JMI da takunkuman tattalin arziki, masu tsanani, a lokaci guda tana fadar cewa hanyar Diblomasiyya ce kadai ta rage wajen warware matsalar shirin makamashin nukliya na kasar Iran, wanda ya tabbatar da fuska biyu na kasashen na Turai. Labarin ya kara da cewa, wani mai magana da yawun kungiyar ta EU wanda kuma baya son a bayyana sunansa, ya fadawa kamfanin dillancin labaran IRNA...
An kori jakadan Isra’ila a Habasha Avraham Neguise daga taron kungiyar Tarayyar Afirka da aka gudanar a wannan Talata a Addis Ababa domin tunawa da kisan kiyashin da aka yi a Rwanda. An fitar da Neguise daga dakin taro na Mandela da ke hedikwatar Tarayyar Afirka bayan da kasashe da dama suka nuna rashin amincewarsu da halartarsa a taron shekara-shekara kan kisan kiyashin da aka yi a kasar Rwanda. Jakadan na Isra’ila ya shiga wurin taron ne ba zato ba tsammani, ba tare da an gayyace shi ba, a cewar majiyoyin diflomasiyyar da suka halarci taron. Majiyar ta kara da cewa tawagogin kasashen Afirka da dama sun nuna rashin amincewa da zuwansa, lamarin da ya sa aka dakatar da taron...
Wakilan kungiyar tarayyar Afirka sun isa birnin Juba na kasar Sudan ta Kudu, a kokarin da suke yi na shiga tsakanin hana komawa yakin basasa. Tarayyar Afirkan ta fara kokarin shiga tsakani ne, bayan daurin talala da aka yi wa mataimakin shugaban kasa Riek Machar a gidansa,lamarin da ya sake jefa kasar cikin zaman dar-dar. Gwamnatin Salva Kir tana zargin Machar da cewa yana rura wutar wani sabon yaki a cikin kasar. A ranar Laraba ta makon da ya shude ne dai aka yi wa mataimakin shugaban kasar daurin talala a gidansa saboda fadan da ake yi a yankin Upper Nile tsakanin sojojin gwamnati da kuma masu dauke da makamai na rundunar “White Army”. A lokacin yakin basasar da kasar...
Jami’an tsaro a tarayyar Najeriya a birnin Kano sun haramta daban da aka saba yi a karshen watan azumi a birnin. Jaridar Premium times ta Najeriya ta nakalto Jami’an tsaron kasar suna bada wannan sanarwan ne bayan da sarki na 15 Wato Aminu- Ado Bayero ya bada sanarwan janye daban da ya shirya gabatarwa a kwanakin salla Karamah. Shugaban Jami’an tsaron ya bayyana haka ne a wani taron yan jarida da ya gabatar a jiya Jumma’a ya kuma kara da cewa baza su amince da gudanar da taron Durba a karamar sallah a wannan shekara ba. Kakakin yansada na jihar Kano Haruna Kiyawa, ya sanya sanarwan a shafinsa na Facebook. Kafin haka aranar 18 ga watan Maris da muke ciki...
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta kafa runduna ta musamman a kasar don magance matsalolin tsaro daban-daban wadanda kasar take fama das u. Jaridar Premium times ta Najeriya ta nakalto ministan tsaron kasar Muhammad Badaru yana fadar haka a lokacinda yake kaddar da wani bangaren na rundunar a barikin Kabala da ke barikin Jaje a kusa da birnin Kaduna daga arewacin kasar a jiya Litinin. Badaru ya kara da cewa gwamnatin kasar tag a akwai butara da samar da irin wannan rundunar, saboda magance matsalolin tsaro daban-daban wadanda aka dade ana fama das u, ko kuma wadanda suke tasowa nan da ca. Ya kara da cewa rundunar da aka kaddamar a jiya litinin bangare ne na runduna mai sojoji 800 da za’a...
Kungiyar ta ce a maimakon neman cin mutuncin Uguamaye kamata ya yi gwamnatin tarayya ta dukufa neman kawo sauyin da zai rage wa jama’a wahalhalun da suke fuskanta da magance matsalolin tattalin arziki da kasar ke ciki. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Shugaba Bola Ahmed Tinubu A Tarayyar Najeriya Ya Bada Umurnin A Gudanar Da Bincike Kan hatsarin Daren Laraban da Ta Gabata A Abuja
Shugaban tarayyar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bada umurnin a gudanar da bincike don gano abinda ya hadda hatsarin day a faru a kan gadar Karuk an titin Abuja Keffi a daren Labaran da ta gabata, wanda yayi sanadiyyar mutuwar mutane da kuma jikatan wasu. Jaridar Premium Times ta nakalto shugaban kasar yana fadar haka tabakin mai bashi shawara kan al-amuran watsa labarai Bayo Onanuga a jiya Alhamis. Shugaban ya bayyana alhininsa ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu da kuma fatan murmurewar wadanda suka ji rauni. Ya kuma bukaci a gaggauta gudanar da bincike don sanin abinda ya haddasa hatsarin day a kai da wannan asarar, don daukar matakan hana aukuwar irinsa nan gaba.
Mutane Fiye Da 30 Ne Suka Rasa Rayukansu A Lokacinda Motar Dawkar Gas Ta Yi Bindiga A Abuja Na Tarayyar Najeriya
Mutane fiye da 30 ne aka tabbatar damutuwarsu a jiya Laraba a Abubja babban birnin tarayyar Najeriya sanadiyyar bindigan da wata motar daukar iskar gas ta yi a kan gadar Karo da misalign karfe 7:15 a jiya Laraba. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa hatsarin na jiya ya aukune a dai dai lokacinda direba wata motar dakon mai ta Burma kan wasu ababen hawa a kan gadar Karu dake kan hanyar Abuja-Keffi, sannan ta yi bindiga wanda ya tarwatsa wuta kan motocin da ta tsarewa hanya da dama daga cikin motocin su kuma da wuta kuma mazauna cikinsu sun kasa fita. Ya zuwa yanzu dai jami’an kwana-kwana da kuma majiyar asbitoci a Asokoro da Asbitin kasa...
Jumhuriyar Najer Ta Bukaci Tarayyar Najeriya Ta Taimaka Don Warware Matsalar Karancin Makamashi A Kasar
Kimani makonni biyu Kenan jumhuriyar Najer tana fama da karancin man fetur a gidajen man kasar, wanda ya rage zirga-zirgan ababen hawa a duk fadin kasar har da Yemai babban birnin kasar, har’ila yau ya shafi harkokin tattalin arzikin kasar. Shafin yana labarai na yanar gizo IR News, ya bayyana cewa bayan da gwamnatin sojojin kasar ta kasa magance matsalar a cikin gida, ta tura wata tawaga karkashin jagorancin Ministan man fetur na kasar zuwa tarayyar Najeriya tare da bukatar ta aiko mata tataccen man fetur don magance matsalar. Labarin ya kara da cewa, gwamnatin tarayyar Najeriya dai tuni ta amince da bukatar, tare da bada umurnin a aikawa Jumhuriyar ta Niger tankunan man fetur har 300. Wasu wadanda suka...
Jami’ar kula da manufofin ketare ta Tarayyar Turai, Kaya Kalas, ta tabbatar da cewa, EU za ta iya sake kakaba takunkumi kan kasar Syria, idan aka samu tabarbarewar lamurra, tana mai nuni da yadda ake cin zarafin fararen hula a gabar tekun Syria. Kaya Kalas ta shaidawa kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya cewa, “Muna shirye-shiryen mayar da takunkumi kan Syria, idan muka ga tabarbarewar lamurra na ci gaba, inda ta jaddada cewa, dole ne mika mulki ya kasance cikin lumana da kuma hadin kai, kuma dole ne a kare fararen hula a kowane hali.” Ta bukaci dukkan masu ruwa da tsaki na waje da su mutunta hadin kan Syria, da kuma iko da iyakokinta.”
Shuwagabannin Kasashen Kungiyar tarayyar Turai Sun Bukaci Karin Kudade A Bangaren Tsaro A Rigimarsu Da Amurka
Shuwagabannin kasashen Turai, sun amince da kara kudade mai yawa a bnaren tsaro da kuma tallafawa kasar Ukraine, a yakin da take yi da kasar Rasha, saboda janyewar Amurka dukkan taimakon da take bawa kasar ta Ukraine. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar taron shuwagabannin kasashen na Turai, sun zuba kudade dalar Amurka biliyon $860 (Euro 800bn) don karfafa kasashen Turai da kuma Ukrania. Shugaban kungiyar ta EU Ursula von de Leyen yace a karon farko tsaron kasashen yake komawa kansu bayan da Amurka ta dauki nauyin hakan tun bayan yakin duniya na II. A halin yanzu gwamnatin kasar Amurka tace ba zata ci gaba da kashewa wadannan kashe kudade don tsarunsu ta kungiyar tsaro ta...
Shugaban kasar Najeriya Bola Tinubu ya bayar da umarnin bayar da lasisin kafa sabbin jami’o’i 11 a cikin kasar. Ministan ilimi na kasar ta Nijeriya Tunji Alausa ya bayyana cewa; amincewa da kafa sabbin jami’oin da shugaban kasa ya yi, yana nuni ne da yadda ya mayar da hankali wajen ganin ilimi ya isa ga koma. Wani abu da gwamnatin tarayyar ta amince da shi, shi ne ware kudade da su ka kai dala miliyan 1.67 domin harba tauraron dan’adam da zai rika kula da wuraren hako ma’adanai.
Kungiyar Hamas ta jinjinawa kungiyar tarayyar Afrika ta AU kan yin Allah wadai da kisan kiyashin da Isra’ila ke yi a Gaza bayan da kungiyar ta soki Isra’ila da keta dokokin kasa da kasa a jawabin rufe taron da ta yi na kwanaki biyu a Addis Ababa. Hamas ta ce tana matukar godiya da matsayin da kasashen Afirka suka dauka a kan Isra’ila da “mummunan” ayyukanta a Gaza. A cikin sanarwar da ta fitar, kungiyar ta AU ta ce tana adawa da keta dokokin kasa da kasa da kuma “kai hari kan fararen hula da kayayyakin more rayuwa da Isra’ila ke yi”. Kungiyar dai ta yi Allah Wadai da duk wani Shirin tilastawa Falasdinawa gudun hijira daga muhallinsu Batun neman...
Kungiyar Tarayyar Afirka ta yi Allah Wadai da duk wani Shirin tilastawa Falasdinawa gudun hijira daga muhallinsu Batun neman tilastawa Falasdinawa gudun hijira daga kasarsu ta gado yana ci gaba da fuskantar tofin Allah da Allah wadai a duk fadin duniya da kuma a taruka daban-daban, kuma batun Falasdinu shi ne kan gaba a ajandar taron kolin Afirka karo na 38 da aka yi a birnin Addis Ababa fadar mulkin kasar Habasha. A yayin bude zaman taron kolin kungiyar tarayyar Afirka, shugaban hukumar Tarayyar Afirka, Moussa Faki, ya yi gargadi game da kiraye-kirayen da ake yi na tilastawa Faladinawa gudun hijira, yana mai jaddada cewa ci gaba da tauye wa Falasdinawa ‘yancinsu abin kunya ne ga bil’Adama, yana mai sukar...
Kungiyar Tarayyar Afirka ta bayyana cewa: Sudan ce kasar da aka fi fama da matsalar jin kai a duniya A zaman tattaunawa da Kungiyar Tarayyar Afirka ta gudanar ta bayyana yakin basasar Sudan a matsayin “mafi girman matsalar jin kai a duniya,” inda ta yi gargadin irin mummunar illar da yake yi kan fararen hula, musamman kananan yara masu fama da rashin abinci mai gina jiki. Wadannan kalamai sun zo ne a yayin wani taron tattaunawa da kungiyar Tarayyar Afirka ta gudanar, inda aka yi karin haske kan rikicin da ake yi tsakanin sojojin Sudan da dakarun kai daukin gaggawa, wanda ya yi sanadiyyar raba mutane kimanin miliyan 12 da matsugunan su. Yakin dai ya kawo cikas wajen kai agajin...
Dan Majalisar Tarayya mai Wakiltar Zangon Kataf/Jaba daga Jihar Kaduna, Honorabul Amos Gwamna Magaji ya sauya sheka daga jam’iyyar adawa ta PDP zuwa APC mai mulki. A safiyar Talata Shugaban Majalisar, Abbas Tajuddeen ya sanar da sauya shekar, yana mai bayyana rikicin cikin gidan PDP a mastayin dalilin ficewar dan majalisar daga jam’iyyar. Dan majalisar ya bayyana cewa kafin ya sauya shekar sai da ya tuntubi al’ummar mazabarsa inda suka ba shi hadin kai da kuma amincewa.
Kungiyar Tarayyar Turai EU ta yaba wa ƙoƙarin Gwamna Babagana Umara Zulum wajen farfado da harkokin rayuwar al’ummar Jihar Borno bayan tashe-tashen hankulan ’yan ta’adda da jihar ta yi fama da shi. EU ta buga misali da cibiyar koyar da sana’o’i ta Muna da ke horar da matasa musamman waɗanda rikicin Boko Haram ya shafa na tsawon fiye da shekaru goma. Ya je Maiduguri daga Legas a kan keke Rikicin rusau ya yi ajalin mutum 4 a Kano Shugaban tawagar Tarayyar Turai a Borno, Ambasada Gautier Mignot ne ya yi wannan yabon a Maiduguri a lokacin da yake zantawa da manema labarai a cibiyar koyar da sana’o’i ta Muna. Ambasada Mignot ya ce tawagarsa ta yi matuƙar farin ciki da...
Majalisar Dokokin Tarayyar Turai Ta Amince Da Bukatar Kawo Karshen Rikicin Jin Kai Cikin Gaggawa A Gaza
Majalisar Dokokin Tarayyar Turai ta yi kira da a kawo karshen rikicin jin kai na Gaza cikin gaggawa Majalisar dokokin Tarayyar Turai ta amince da wata shawara a jiya Larabar da ta aka gabatar da ta bukaci kawo karshen rikicin jin kai na yara, mata da fursunoni a Zirin Gaza, sakamakon kisan kare dangi da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta yi a yankin sama da watanni 15. Cibiyar yada labarai ta Falasdinu ta watsa rahoton cewa: An tattauna shawarwarin da suka yi kira da a kawo karshen rikicin jin kai da ya shafi yara, mata da fursunoni a Gaza, a babban taron Majalisar Dokokin Tarayyar Turai. A kuri’ar da aka kada, an amince da kudurin da rinjayen kuri’u 90, inda...