2025-12-01@08:02:45 GMT
إجمالي نتائج البحث: 7

«Jami ar MAAUN»:

    Ana ci gaba da ta ƙaddama kan Naira dubu ɗari bakwai da hamsin da Jami’ar Amurka ta Maryam Abacha  (MAAUN) da ke Jihar Kano ta wajabta wa ɗalibanta da suka kammala karatu biya a matsayin kuɗin bikin yaye ɗalibai. Jami’ar MAAUN ta sanya wa kowane ɗalibin da ya kammala karatu biyan Naira dubu ɗari bakwai da hamsin a matsayin kuɗin bikin yaye ɗalibai, kafin ta ba shi takardar shaidar kammala karatu da gabatar da bayanansa domin samun damar halartar aikin yi wa ƙasa hidima (NYSC). Sai dai kuma, Hukumar Karɓar Ƙorafi ta Jihar Kano (PCACC) ta umarci iyayen ɗaliban cewa su dakata da biyan kuɗin har sai ta kammala bincike kan ƙorafin da suka gabatar mata a kan lamarin. Sanarwar...
    Shugaban Hukumar Gudanarwa Filayen Jiragen Sama ta Kasa (FAAN), Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya sake tabbatar da kudirin Gwamnatin Tarayya na dawo da tsohon martabar Filin Jirgin Sama na Malam Aminu Kano. Dakta Ganduje ya bayyana hakan ne yayin wata ziyarar duba aiki da ya kai filin jirgin a Kano. Ya jagoranci wata tawaga mai ƙarfi ta jami’an FAAN domin tantance halin da filin jirgin yake ciki yanzu, ciki har da ayyukan da ake gudanarwa da kuma waɗanda aka bari da nufin samar da cikakken tsari na zamani da dorewar ci gaba. Ya bayyana a matsayin ɗaya daga cikin tsofaffin filayen jiragen sama masu tarihi a Najeriya da yankin Yammacin Afirka, wanda a da yake ɗaya daga cikin manyan cibiyoyin...
    Daya daga cikin manyan jiga-jigan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) kuma ɗan kasuwa mai taimakon al’umma, Abdussalam Abdulkarim Zaura, wanda aka fi sani da AA Zaura, ya yi kira ga ’yan Nijeriya da su ba da cikakken goyon bayansu ga gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, yana mai bayyana kwarin gwiwa cewa shugaban na da kwarewa da hangen nesa wajen farfado da tattalin arzikin ƙasar da inganta jin daɗin jama’a. Zaura ya yi wannan kiran ne lokacin da wata tawaga daga Tinubu/Shettima Campaign Group ta kai masa ziyarar ban girma a ofishinsa, inda ya jaddada cewa haɗin kan ’yan Nijeriya na da matuƙar muhimmanci domin samar da ci gaba mai ɗorewa da kuma tabbatar da matsayi irin na ƙasashen da ke...
    A yayin taron rattaba hannun, Farfesa Gwarzo ya bayyana manufar wannan yarjejeniya, inda ya ce hadin gwiwar za ta bai wa dalibai da ma’aikata damar cin moriyar albarkatu da kwarewa daga kasashen waje.   “Wannan hadin gwiwar alama ce ta jajircewarmu wajen hada jami’o’inmu da manyan cibiyoyi na duniya domin bunkasa kirkire-kirkire da bincike a rukunin jami’o’inmu na MAAUN,” in ji shi.   A karkashin wannan yarjejeniyar, cibiyoyin biyu za su rika raba kwarewar su tare da tallafa wa juna don cimma manufofi na bai daya. Muhimman bangarorin hadin gwiwar sun hada da samar da koyarwar harshen Turanci ta yanar gizo ga daliban MAAUN, samar da hanyoyi don ci gaba da karatu a Seneca, da bayar da shawarwari kan harkokin...
    Kamfanin jirgin sama na British Airways ya hana fasinjoji 58 hawa jirginsa da zai tashi daga Abuja zuwa Landan saboda matsala da ƙofar jirgin ta samu. Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Najeriya (NCAA), ta ce kamfanin jirgin ya bar wasu kujeru babu kowa saboda dalilan tsaro. Matsalar tsaro na iya hana mu ci gaba da rijistar masu zabe a Borno – INEC Jama’a ba sa yaba wa kokarinmu na hana aikata laifi – Babban Sufeton ’Yan Sanda Daraktan Yaɗa Labarai da Kare Haƙƙin Fasinjoji na NCAA, Mista Michael Achimugu, ya wallafa a shafinsa na X cewa matsala ce ta sa aka hana fasinjojin hawa jirgin. Ya ce an bai wa fasinjoji 30 wajen kwana a wani otel, yayin...
    An gabatar da Tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Abdullahi Ganduje, a matsayin Shugaban Kwamitin Hukumar Kula da Filayen Jiragen Sama ta Ƙasa (FAAN). Wannan naɗin ya biyo bayan murabus ɗin da Ganduje ya yi daga shugabancin APC kwanan nan, inda ya bayyana cewa ya yi hakan saboda wasu muhimman dalilai na ƙashin kansa. 2027: Idan ADC na son lashe zaɓe dole ta bai wa ɗan Arewa takara — Okonkwo Biza: UAE ta ƙaƙaba wa ’yan Najeriya sabbin takunkumai Jam’iyyar ta maye gurbinsa da Ali Bukar Dalori a matsayin shugaban riƙon ƙwarya. Gbenga Saka, mai bai wa Ministan Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo, shawara kan harkokin dijital, ya wallafa bidiyon bikin rantsar da Ganduje a shafin X. Ganduje, wanda tsohon...
    Gwamnatin Tarayya, ta dakatar da zirga-zirgar jiragen Max Air na tsawon wata uku, bayan ɗaya daga cikin jiragen kamfanin, tayarsa ta yi bindiga yayin sauka a filin jirgin saman Malam Aminu Kano a daren ranar Talata. Jirgin Max Air ƙirar Boeing 734 mai lamba 5N-MBD ne ya samu matsalar kamar yadda rahotanni suka bayyana. Za a dawo da ’yan Najeriya sama da 5,000 da ke zaune a Amurka Jami’an tsaro sun mamaye sakatariyar PDP bayan ɓarkewar rikici Dukkanin fasinjoji 53 da ke cikin jirgin sun kuɓuta cikin ƙoshin lafiya. Wannan shi ne karo na uku da jirgin Max Air ke fuskantar matsala cikin watanni uku da suka gabata. Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Ƙasa (NCAA), ta sanar da...
۱