Aminiya:
2025-12-11@07:38:07 GMT

Cin hanci da rashawa sun yi ƙatutu a Najeriya — ICPC

Published: 11th, December 2025 GMT

Hukumar ICPC ta ce da ana aiwatar da dokokin yaƙi da cin hanci da rashawa yadda ya kamata, da kusan kashi 80 na ’yan Najeriya na ɗaure a gidan yari.

Kwamishinan ICPC na Jihar Kaduna, Sakaba Ishaku ne, ya bayyana haka a wani taron horaswa kan yadda ake kula da amana a ƙananan hukumomi.

Kisan Zariya: Na bar Buhari da Allah — Sheikh El-Zakzaky Najeriya za ta buga wasan sada zumunta da Masar kafin fara gasar AFCON ta 2025

Ya ce cin hanci ya yi tasiri sosai a rayuwar ’yan Najeriya, kuma yana haifar da talauci, rikice-rikice, da jinkirta ci gaban ƙasa.

Ya ƙara da cewa yawancin dukiyar da wasu ke taƙama da ita a Najeriya ma da alaƙa da aikata rashin gaskiya, kuma mutane da yawa ba sa son jin batun yaƙi da cin hanci saboda suna jin daɗin aikata shi.

Ishaku, ya soki shugabannin ƙananan hukumomi da ke barin kujerarsu ba tare da sun aiwatar da wani gagarumin aiki ba.

Ya kuma nemi a tsaurara hukunci ga masu satar dukiyar gwamnati, inda ya ce duk wanda ya saci dukiyar jama’a bai kamata a masa hukunci mai sauƙi ba.

Kwamishinan Harkokin Ƙananan Hukumomi na Kaduna, Sadiq Mamman Legas, ya goyi bayan bayanan ICPC.

Ya ce gwamnati ta gyara na’urorin wutar lantarki a wasu yankuna, amma mazauna wajen suka lalata, tare da suka sace wasu.

Ya ce ba za a samu ci gaba ba idan mutane suna lalata dukiyar gwamnati.

Dukkanin jami’an sun yi kira da a ƙara ƙarfafa doka, a kula da ayyukan gwamnati sosai, kuma a wayar da kan jama’a domin rage cin hanci da kare kayayyakin gwamnati.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: ɗauri Gidan Yari gwamnati rashawa

এছাড়াও পড়ুন:

Najeriya za ta buga wasan sada zumunta da Masar kafin fara gasar AFCON ta 2025

Tawagar Super Eagles ta Najeriya za ta buga wasan sada zumunta da ƙasar Masar kafin fara gasar Kofin Afrika da za a yi a Maroko.

Wasan zai gudana ne a ranar 11 ga wata. Disamba, da misalin ƙarfe 7 na dare, a filin wasa na Cairo da ke Masar.

EFCC ta tsare Malami kan binciken kuɗaɗen Abacha Real Madrid  za ta ɓarje gumi da Manchester City a Santiago

Za a yi wasan ne kwana shida kafin a fara gasar da ƙasashe 24 za su fafata a cikinta.

Najeriya za ta fara wasanta na farko a ranar 23 ga watan Disamba da Tanzania.

Ita kuwa Masar za ta buga wasanta na farko da Zimbabwe a ranar 22 ga watan Disamba.

A tarihi, Masar ce tafi lashe Kofin Afrika inda ta lashe gasar sau bakwai, yayin da Najeriya ta lashe sau uku.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe ta Jigawa Ta Nemi Kotuna Su Daina Jan Kafa Wajen Aiwatar da Shari’a
  • Karamar Hukumar Agwara ta Jinjinawa Gwamnati Bisa Tabbatar da Tsaron Rayuka da Dukiyoyin Jama’a
  • Najeriya za ta buga wasan sada zumunta da Masar kafin fara gasar AFCON ta 2025
  • Najeriya da Saudiyya sun rattaba hannu kan yarjejeniyar samar da tsaro
  • Zanga-zanga ta ɓarke kan zargin sojoji da kashe mata a Adamawa
  • Majalisar Dattawa ta amince Tinubu ya tura sojojin Najeriya zuwa Jamhuriyar Benin
  • Yara masara zuwa makaranta barazana ne ga kasa — Shettima
  • NAJERIYA A YAU: Yadda Abincin Da Mutane Ke Ci Ke Zamewa Guba
  • NAJERIYA A YAU: Kudaden Da Samar Da ‘Yansandan Jihohi Zai Lashe