Tsaro: Abba ya kafa runduna ta musamman da za ta ke tsaron tashoshin mota a Kano
Published: 14th, December 2025 GMT
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da kafa wata runduna ta musamman da za ta ke tsaro a tashoshin mota da sauran wuraren jama’a a faɗin jihar.
Mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ne, ya bayyana hakan cikim wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi.
Hukumar Film ta kasa ta horar da marubuta 53 rubutun fim An kashe mai ciki da ɗanta a KanoSanarwar ta ce wannan mataki wani ɓangare ne na ƙoƙarin gwamnatin na daƙile laifuka da kuma kare jihar, musamman manyan hanyoyin shiga da fita na birnin Kano.
An bayyana cewa tashoshin mota na daga cikin wuraren da ake fuskantar barazanar tsaro saboda yawan zirga-zirgar mutane.
Rundunar ta musamman za ta mayar da hankali kan sanya ido, tattara bayanan sirri da gudanar da ayyukan tsaro tare da haɗin gwiwar hukumomin tsaro a tashoshin mota da sauran wurare a jihar.
Haka kuma za ta kula da wurare kamar gidajen mai da sauran wuraren da mutane ke taruwa.
Gwamna Abba, ya ce wannan mataki na nufin daƙile barazanar tsaro, inganta haɗin kai tsakanin hukumomin tsaro, da kuma dawo tabbatar da kwanciyar hankali a jihar.
Ya ƙara da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba mara wa hukumomin tsaro baya wajen kare rayuka da dukiyoyin al’ummar Jihar Kano.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Tsaro Wuraren Taro
এছাড়াও পড়ুন:
NLC Ta Shirya Zanga-Zangar Rashin Tsaro A Faɗin Ƙasa Ranar 17 Ga Disamba
Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa (NLC) ta bayyana cewa za ta gudanar da zanga-zangar ƙasa baki ɗaya a ranar 17 ga Disamba, 2025, domin nuna damuwarta kan taɓarɓarewar tsaro a Nijeriya. Wannan sanarwa ta fito ne daga saƙon da NLC ta aikawa dukkanin majalisun jihohi a ranar 10 ga Disamba, bayan taron NEC da ta gudanar a ranar 4 ga watan. Kungiyar ta nuna baƙin ciki kan ƙaruwar hare-haren ƴan daba da satar mutane da ke ci gaba da addabar al’umma.
NLC ta mayar da hankali musamman kan sace ɗalibai mata a wata makarantar kwana da ke Jihar Kebbi a ranar 17 ga Nuwamba, inda ta bayyana mamaki cewa an janye jami’an tsaro daga makarantar kafin harin. Ta ce wannan lamari ne mummunan kuma abin takaici da ya kamata a bincike shi sosai tare da gurfanar da duk masu hannu a ciki. Ƙungiyar ta zargi gwamnati da gaza ɗaukar matakan da suka dace wajen kare rayukan ɗalibai a makarantu.
Gwamnonin Arewa Sun Yi Rawar Gani A Kafa Gidauniyar Fuskantar Matsalar Tsaro Tinubu Na Ɗaukar Ƙwararan Matakai Don Magance Matsalar Tsaro A Nijeriya – ShettimaSanarwar ta ƙara da cewa an umarci dukkan rassan NLC da ƙungiyoyin ƙwadago da su “shirya cikakke” domin zanga-zangar. Ƙungiyar ta bayyana cewa yawaitar sace yara a makarantu ya kai wani mawuyacin matsayi da ba za a amince da shi ba. Ta jaddada cewa gwamnati na da nauyin kare makarantu, musamman waɗanda suke a karkara ko yankunan da ke fama da hare-hare.
ADVERTISEMENTNLC ta ce dole ne gwamnati ta ɗauki mataki cikin gaggawa ta kammala bincike game da janye jami’an tsaro daga makarantar da aka kai harin, tare da ladabtar da masu laifi. A cewarta, rashin tsaron da ake fuskanta ya zama barazana ga rayuwa, da ilimi da ci gaban ƙasa. Saboda haka NEC ta umarci dukkan ƙungiyoyi da majalisun jihohi su fita ƙwansu da ƙwarƙwatarsu wajen zanga-zangar ranar 17 ga Disamba domin nuna rashin gamsuwarsu da yadda gwamnati ke tafiyar da batun tsaro.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Yadda APC Da ADC Ke Amfana Da Rikicin Jam’iyyar PDP December 12, 2025