NLC Ta Shirya Zanga-Zangar Rashin Tsaro A Faɗin Ƙasa Ranar 17 Ga Disamba
Published: 12th, December 2025 GMT
Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa (NLC) ta bayyana cewa za ta gudanar da zanga-zangar ƙasa baki ɗaya a ranar 17 ga Disamba, 2025, domin nuna damuwarta kan taɓarɓarewar tsaro a Nijeriya. Wannan sanarwa ta fito ne daga saƙon da NLC ta aikawa dukkanin majalisun jihohi a ranar 10 ga Disamba, bayan taron NEC da ta gudanar a ranar 4 ga watan.
Kungiyar ta nuna baƙin ciki kan ƙaruwar hare-haren ƴan daba da satar mutane da ke ci gaba da addabar al’umma.
NLC ta mayar da hankali musamman kan sace ɗalibai mata a wata makarantar kwana da ke Jihar Kebbi a ranar 17 ga Nuwamba, inda ta bayyana mamaki cewa an janye jami’an tsaro daga makarantar kafin harin. Ta ce wannan lamari ne mummunan kuma abin takaici da ya kamata a bincike shi sosai tare da gurfanar da duk masu hannu a ciki. Ƙungiyar ta zargi gwamnati da gaza ɗaukar matakan da suka dace wajen kare rayukan ɗalibai a makarantu.
Gwamnonin Arewa Sun Yi Rawar Gani A Kafa Gidauniyar Fuskantar Matsalar Tsaro Tinubu Na Ɗaukar Ƙwararan Matakai Don Magance Matsalar Tsaro A Nijeriya – ShettimaSanarwar ta ƙara da cewa an umarci dukkan rassan NLC da ƙungiyoyin ƙwadago da su “shirya cikakke” domin zanga-zangar. Ƙungiyar ta bayyana cewa yawaitar sace yara a makarantu ya kai wani mawuyacin matsayi da ba za a amince da shi ba. Ta jaddada cewa gwamnati na da nauyin kare makarantu, musamman waɗanda suke a karkara ko yankunan da ke fama da hare-hare.
ADVERTISEMENTNLC ta ce dole ne gwamnati ta ɗauki mataki cikin gaggawa ta kammala bincike game da janye jami’an tsaro daga makarantar da aka kai harin, tare da ladabtar da masu laifi. A cewarta, rashin tsaron da ake fuskanta ya zama barazana ga rayuwa, da ilimi da ci gaban ƙasa. Saboda haka NEC ta umarci dukkan ƙungiyoyi da majalisun jihohi su fita ƙwansu da ƙwarƙwatarsu wajen zanga-zangar ranar 17 ga Disamba domin nuna rashin gamsuwarsu da yadda gwamnati ke tafiyar da batun tsaro.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Yadda APC Da ADC Ke Amfana Da Rikicin Jam’iyyar PDP December 12, 2025কীওয়ার্ড: ranar 17 ga
এছাড়াও পড়ুন:
Katsina Ta Amince Da Bayar Da Alawus Na Naira 30,000 Duk Wata Ga Malaman Karkara
Suleiman-Jibia ya ƙara sanar da cewa, majalisar ta amince da kafa Cibiyoyin Horar da Malamai a Katsina, Daura, da Funtua.
“Cibiyoyin za su taimaka wajen haɓaka tsarin koyarwar malaman domin samar da ingantaccen ilimi ga ɗalibai a faɗin jihar,” in ji shi
ShareTweetSendShare MASU ALAKA