Aminiya:
2025-12-11@15:36:39 GMT

Manchester United ta shiga zawarcin Sergio Ramos

Published: 11th, December 2025 GMT

Ƙungiyyar Ƙwallon Ƙafa ta Manchester United ta fara zawarcin tsohon ɗan wasan Real Madrid Sergio Ramos, mai shekara 39,wanda ya bar Ƙungiyar Monterrey ta Mexico.

Ramos wanda a shekarun baya, United ta yi ƙoƙarin ɗaukarsa, yanzu haka yana da damar komawa ƙungiyyar a matsayin kyauta.

Zanga-zanga ta ɓarke bayan haɗarin tirela ta kashe mutum a Yobe Kisan Zariya: Na bar Buhari da Allah — Sheikh El-Zakzaky

United dai yanzu haka tana fuskantar matsaloli daga ’yan wasan baya, inda Harry Maguire ke fama da rauni, yayin da sauran ’yan wasan ke tafka kura-kurai.

Manchester dai yanzu haka ta amincewa mai horarwa ta Roben Amorim ya sayi ɗan wasan baya da tsakiya a watan Januairu.

Kawo yanzu dai ƙungiyyar na mataki na 6 da maki 25 cikin wasannin 15 da ta buga a gasar Firimiyya.

A ranar Litinin ƙungiyyar zata karɓi bakuncin Bournemouth a wasan mako na 16 a filin wasanta na Old Trafford.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Sergio Ramos

এছাড়াও পড়ুন:

Real Madrid  za ta ɓarje gumi da Manchester City a Santiago

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid za ta kece raini da Manchester City a wasan mako na biyar a Kofin Zakarun Nahiyar Turai.

Real Madrid da Manchester City sun fuskanci juna sau 14 a gasar  Zakarun Turai, inda Real Madrid ta yi nasara sau biyar, City ta ci huɗu da canjaras biyar.

Najeriya da Saudiyya sun rattaba hannu kan yarjejeniyar samar da tsaro An kama wani mutum a Abuja yana ƙoƙarin kai harsasai ga ’yan bindiga a Zamfara

Sun fuskanci juna a kowace kaka sau huɗu baya a Champions League.

A bara Real Madrid ce, ta fitar da City a zagayen cike gurbi da suka yi 3-2 a wasan farko inda Manchester da yi nasara da ci 3-1 a Sifaniya.

Real Madrid ta yi nasara 13 daga wasa 14 a Champions League a zagayen cikin rukuni a gida da rashin nasara ɗaya.

Kylian Mbappe na taka rawar gani a Champions League inda ya zura ƙwallo tara, wanda ya ci bakwai daga wasa bakwai a gasar da ya fuskanci Man City, tare da har da cin ƙwallo uku rigis a bara da Real Madrid ta yi nasara 3-1.

City ta lashe wasa shida daga fafatawa bakwai a Champions League a zagayen rukuni da ta kara da ƙungiyoyin Sifaniya, inda ta yi rashin nasara ɗaya.

Erling Haaland, ya zura ƙwallo tara a raga a fafatawa tara a karawar da ya yi da ƙungiyoyin Sifaniya a Champions League.

Ya kuma jefa ƙwallo a wasa biyar a gasar a yanzu.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kisan Zariya: Na bar Buhari da Allah — Sheikh El-Zakzaky
  • Najeriya za ta buga wasan sada zumunta da Masar kafin fara gasar AFCON ta 2025
  • Real Madrid  za ta ɓarje gumi da Manchester City a Santiago