’Yan kasar Chadi 3 sun mutu a hatsarin kwalekwale a Borno
Published: 13th, December 2025 GMT
Wani kwalekwale da ke ɗauke da fasinjoji takwas ya kife yayin da yake ƙetare kogin da ke kan iyaka da garin Gamboru na Najeriya da Fotokol a ƙasar Kamaru, inda mutane uku suka mutu.
Lamarin ya faru ne da misalin qarfe 6:30 na yamma lokacin da kwalekwalen, wanda wani Mamman Nur Abbagana na Kasuwan Katako, Gamboru ke tuƙa shi ya kife a tsakiyar ruwa tare da jefa dukkan fasinjoji cikin ruwa.
Majiyoyin tsaro sun tabbatar da cewa dukkan fasinjoji takwas ’yan ƙasar Chadi ne da ke tafiya daga Jos, Jihar Filato, a kan hanyarsu ta zuwa N’Djamena, Jamhuriyar Chadi.
An ceto fasinjoji biyar, waɗanda aka tabbatar da suna raye ba su mutu ba.
Yadda za ku cike neman aikin jami’an lafiya a Hajjin 2026 da NAHCON Kotu ta sa ranar yanke hukunci a Shari’ar Abba Kyari da NDLEAWata mata mai suna Alphosine Makebu Beboroum, mai shekaru 34, da ’ya’yanta mata biyu Centich Mamajibe, mai shekaru 3, da Mamajilem Bebaroum, ‘yan watanni 10, sun nutse kuma har yanzu ba a gano su ba har zuwa Kammala wannan rahoto, duk da ana cigaba da gudanar da aikin ceto da bincike.
A halin yanzu, hukumomin ’yan sanda sun kuma tabbatar da kama mai tuƙa kwale-kwalen saboda karya umarnin gwamnatin Jihar Borno na tilasta wa duk masu aikin kwalekwale da su yi amfani da jakar ceto.
Kakakin rundunar ASP Nahum Kenneth Daso ya ce ana ci gaba da gudanar da bincike kan musabbabin faruwar lamarin.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Kamaru kwalekwale
এছাড়াও পড়ুন:
Kotun Koli ta soke afuwar da Tinubu ya yi wa Maryam Sanda
Kotun Kolin Najeriya ta soke afuwar da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya yi wa Maryam Sanda, inda ta ce shugaban ya wuce makadi da rawa ta hanyar yin afuwa ga wacce har yanzu kararta ke gaban kotu.
A hukuncin da aka yanke ranar Juma’a, kotun ta yanke hukunci da rinjayen alƙalai huɗu cikin biyar, inda ta tabbatar da hukuncin kisa da Babban Kotun Abuja ta yanke, kuma Kotun Daukaka Kara ta tabbatar.
‘Haduwata da masu garkuwa da ɗan uwana a dajin Zamfara’ Jam’iyyar PDP ta tabbatar da mutuwar mataimakin Gwamnan BayelsaAn yanke wa Sanda hukunci ne a shekarar 2020 bisa laifin kashe mijinta, Bilyaminu Bello, a lokacin rikicin cikin gida a gidansu da ke Abuja.
Kotun ta yi watsi da ƙarar da ta shigar, tana mai cewa masu gabatar da ƙara sun tabbatar da laifin kisan kai ba tare da wata shakka ba.
A hukuncin jagoran alkalan, Mai Shari’a Moore Adumein ya ce Kotun Daukaka Kara ta yi daidai wajen tabbatar da hukuncin kotun farko.
Ya ce shiga tsakani na shugaban ƙasa bai dace ba a irin wannan yanayi.
Mai Shari’a Adumein ya ce: “Ba daidai ba ne ga bangaren zartarwa ya yi ƙoƙarin amfani da ikon afuwa kan laifin kisan kai, wanda har yanzu kararsa na gaban kotu.”
A watan Oktoba, an rage hukuncin Maryam zuwa shekaru 12 a kurkuku bayan Shugaba Tinubu ya amince da jerin sunayen wadanda ya yi wa afuwa.
Wannan mataki ya biyo bayan nazari da ya fara da sunaye 175, kafin daga baya a cire wasu saboda irin laifukan da suka aikata.
A lokacin, Mai Ba da Shawara na Shugaban Ƙasa, Bayo Onanuga, ya ce rage hukuncin Sanda “ya dogara ne da tausayi saboda amfanin ’ya’yanta da kuma kyakkyawan halinta,” sannan ya ce ta nuna “nadama.”
Wannan mataki ya janyo suka a fadin Najeriya, ciki har da adawa daga dangin marigayi Bello.
Hukuncin na Kotun Kolin yanzu dai ya soke afuwar ta Shugaban Ƙasa.
Maryam Sanda ta shafe kusan shekaru shida a kurkuku, kuma hukuncin da aka rage zai bar ta da kusan shekaru shida nan gaba. Amma da hukuncin na ranar Juma’a, an dawo da hukuncin kisa da aka yanke mata tun farko.