Babu Wanda Ya Jawo Ra’ayina Zuwa Masana’antar Kannywood —Umar Hassan (2)
Published: 21st, September 2025 GMT
Wanda zan iya tunawa za su kai goma haka.
Ko akwai wani fim wanda bayan fitar sa ka samu ƙalubale daga dangi ko wajen masu kallo?
Gaskiya a fim dai har yanzu ban samu wani ƙalubale ba, saboda duk abin da nake fitowa a rol na malunta ne. Kawai dai akwai wata waƙa da na yi bidiyonta a kanta ne gaskiya na fuskanci ƙalubale sosai, dan akwai wanda ya taɓa kira na yana hawaye ya ce min me ya ja min wannan harka haka har na fito ina rawa da jaruma?.
Ka canza shawarar barin harkar ta dalilin hakan, ko kuwa ka kalli hakan matsayin jarrabawa tunda ka san baka yi ba?
Gaskiya a lokacin har furta cewa na yi na daina, daga baya ne mahaifiyata bayan ta riƙa ganin irin bidiyoyin, tunda daman da bidiyoyin waƙa na fara, sai ta bani shawarar ko zan yi na juyar da abin tunda ina so na mayar da shi ta wancen ‘part’ ɗin zai fi alkairi, shi ne na koma.
Ba ka ganin za a iya samun ƙalubale game da hakan, musamman yadda aka taɓo ɓangarori daban-daban, duba da yadda a yanzu ake samun rashin jituwa ga wasu malaman ta fannin bambancin Aƙida?
Dan matsala za a iya samun matsala, dalili kuwa shi ne, rigar malamai za a shiga. Sannan kuma abu ne da zai taɓa ɗari’a, izala, shi’a, dole wasu za su ga kamar za a ci mutuncinsu ne. Tunda ba a taɓa samun fim da ya haɗa wannan ra’ayoyin ace zai yi magana akan aƙidun nan gabakiɗaya ba za a samu wannan matsalar. Sai dai kawai abin da nake tunani ba dole su jagororin malamai su fahimta ba, in Allah ya sa su masu kallo da ake yi wa suka fahimci saƙon dake ciki buƙata ta biya. Kuma ni a shirye nake da zagi ko cin mutunci, ko mutuwa, ko ɗauri, akan wannan fim ɗin, matuƙar al’ummar musulmi sun fahimci abin da ake son su fahimta. Kuma ni bana jin ɗar-ɗar akan wannan fim ɗin duk zugar al’ummar duniya ina da yaƙini tunda gaskiya na sa a raina, kuma da manufa ce mai kyau Allah zai taimake ni ya yi mana jagoranci akan wannan fim ɗin.
Ka yi maganar ajjiye harkar fim, kenan kana ganin za ka iya ajjiye harkar fim gabaɗaya da zarar fim ɗin ya fita?
E! ina kyautata zaton hakan. Domin wannan shi ne burina wanda ya rage min a harkar fim, idan wannan fim ɗin ya fita ina kyautata zaton zan iya ajjiye harkar fim a gaba in sha Allah. Tsakanina da ita sai dai in bayar da shawarwari ko kuma in zan zama furodusa ko Darakta, amma dai aktin zan ja baya da shi, in sha Allahu Ta’ala. Shi ya sa ma ban fito na bayyanawa duniya ba. Dan akwai ‘Show’ ɗin Hadiza Gabon ta gayyace ni kuma a kan wannan gaɓar ne to, amma na jinkirta ban je ba saboda ina son lokacin da aka gama fim ɗin aka sake shi, zan furta cewa na daina fim in sha Allah.
Ko akwai wani fim da ya taɓa baka wahala a yayin ɗaukar shirin?
Babu wani fim da ya taɓa ba ni wahala, tunda mafiya yawanci duk abin da za a faɗa kwakwalwata ta saba ɗaukewa. Kuma rol ɗin da nake taka rawa ɗabi’a ta ce ta gaske ta almajirai, na kan zauna gaban dubunnan al’umma na ja musu na fassara musu. Saboda haka ko da na zo ‘camera’ ba ta zame min baƙon abu ba, kawai dai kafin na fahimci yadda ɗaukar ‘see you’ da ‘white shot’ ne ya ɗan wahalar da ni. Amma tunda na fahimta da riƙe ‘dialogue’ da yin ‘acting’ ba ya wahalar da ni.
Wane irin nasarori ka samu game da fim?
E! to, tunda dai har yanzu fuskata ba ta fashe ba, na ɗaukar hoto ne idan an ganni a gaske ace za mu yi hoto. Amma nasara da za a ce na kuɗi ko na mene duk abin da zan samu da bazar alƙur’ani nake samu. Ba zan ce ga wani abu guda ɗaya da fim ya yi min da zan yi alfahari da shi ba, kamar yadda zan danganta riga ta addini ta min. Ko dan na shiga da ƙafar hagu ne, ko kuwa baki ne na mutane da suka yi yawa ba sa sona da harkar na ƙaƙabe sai nayi. Hana ƙarya sau ɗaya watarana na hau mota daga wani waje wayata ta faɗi kuma ban tafi da ATM Card ba, muka haɗu da wani a mota ya ganni na dai hau motar ne ban ma san yadda zan yi ba, kawai in na sauka duk yadda za a yi sai a yi kawai ya ce “Wane kamar na sanka a fim’ na ce “Eh”. Muka fara surutu muna sauka ya biya min kuɗin mota to, sai na ji daɗi. Ni ba abin da zan ce fim ya yi min duk abin da za a ban a cikinsa gaskiya na fi ƙarfinshi, ni ba a taɓa bani kyauta a fim da ta fi ƙarfin wadata ta ba.
Ya ka ɗauki fim a wajenka?
Ni gaskiya ban ɗauki fim sana’a ba na dai ɗauki fim hanyar isar da saƙo, kuma a cikinta idan Allah ya ga dama zai iya haɗa ka da wani da zai yi maka hanyar wani alkhairin. Ban ga abin da fim zai min ba ya shafe abin da Allah ya shafa min na ni’imar addini ba, na abubuwan da nake samu a addini. Fim bai taɓa yi min ba, kuma bana tunanin daga nan har duniya ta tashi wai fim zai mamaye abin da na samu a darajar addini ba.
Mu koma ga ɓangaren waƙa, kamar wacce irin waƙa ka ke yi?
A horewa da baiwa da Allah (SWT) ya ɗan hore ba wacce ba na yi, tun daga kan ta biki, siyasa, ta sarakai da sauransu an ɗan taɓa. Amma waƙar soyayya ma ba layina ba ce saboda ni ba masoyin bane bana soyayya gaskiya.
Ka yi waƙoƙi sun kai kamar guda nawa?
Mutum ba ya zurawa da yawa, amma a taƙaice zan iya cewa sun kai kamar guda Talatin. A cikin waƙoƙin kuma akwai wacce na yi wa Hadiza Gabon wacce na bayar da labarin soyayyar da nake yi mata, duk da ita ma ƴ an jaridu sun sha yi min tambayoyi akan waƙar. Na yi mata waƙoƙi guda goma.
Waɗanne irin tambayoyi aka fi yi maka game da waƙar, kuma ya karɓuwar waƙar ta kasance ga Hadiza Gabon ɗin?
Wasu na tambaya ta, shin soyayyar da na yi mata a waƙar so ne na aure ko so ne na ‘fans’?. Saboda waƙar na yi ta ne me harshen damo, sannan na bayyana ƙalubalen da na fuskanta wajen neman ganinta a cikin waƙar. To, wasu sun kikkira har a gidajen radiyo, shin ƙalubalen dana fuskanta gaske ne ko ba haka bane?. Sannan ita kanta ta san da waƙar amma a lokacin ban wani samu karɓuwa a wajenta ba, saboda wataƙil tunaninta irin mutanen nan ne da suke zuwa da salo domin su sami kuɗi. A iya tunaninta kamar na yi ne domin na samu kuɗi, kuma a lokacin da rufin asirina ba na tunanin za ta yi min wani abu.
Ka iya waƙa sai dai kuma ba ka saka sunanka akan waƙarka, me ya sa hakan?
Mafiya yawancin waƙoƙina ba na saka sunana dukka waƙoƙina haka suke, da na fara sakawa amma kuma da na fahimci ba a so ni ma kuma bana son na bayyanar da kaina sai na riƙa ɓoye sunana. ‘Studio’ da na y waƙa sai na saka sunan, misali idan na yi a Munnir Ali to, za ki ga an saka Munir Ali, haka idan a ‘studio’ Auta mg ne za a saka ‘Mg Boy Record’. Sai ka shiga za ka ji muryar ba ta shi ba ce, tawa ce. Ko na Umar M. Sharif ne zan sa a saka sunan ‘Studio’ ɗinsu, da dai sauransu.
Ba ka gudun a sace maka waƙa?
Sacewa an daɗe ana sacewa, amma ni bai taɓa damuna ba. Dan akwai wata waƙa da na taɓa yi ban taɓa jin an juya ta waƙar ba, sai da na je birnin kebbi, watarana zan je Nijar kawai na ji an saka ta ana ‘Campaign’ da ita. Wallahi waƙar da karin da baitin duk tawa ce, kuma na san mawaƙin ‘studio’ da na je na yi waƙa a ciki shi ya juya waƙar ya yi wa wani. Amma ni bai taɓa damuna ba gaskiya, saboda a ɗauki ma abun ka a juya alamu ne na an yaba da baiwarka, dan da ba da baiwar taka ba wani ko kaya ba zai sata ba.
Waɗanne Jarumai ne suke burgeka kafin ka fara fim, da kuma bayan shigar ka?
Ali Rabi’u Ali Daddy, sai Nura Hussain, su biyun nan su suka fi burge ni. A mata kuma jarumar da ta fi burge ni su uku ne, ta farko akwai Hadiza Gabon, sai jaruma ta biyu Zainab Basarakiya, sai ɗaya jarumar tana masifar burge ni, sai dai yadda na ɗauke ta ita ba haka ta ɗauke ni ba, shi ya sa ma ba zan ambaci sunanta ba.
Wane ne ubangidanka a masana’antar Kannywood?
Idan na ce babu ban yi biyayya ba, idan kuma na ce akwai na yi ƙarya. Zan dai iya cewa iya da ‘role model’ Ali Rabi’u Ali Daddy, kuma idan zan kira Ubangida ma shi ne ubangidana. Da ni da Aminu Saira me Labarina, da irinsu Salisu S. Fulani, da Sahabi Kwana Casa’in, da su Mudassir Isyaku Dutsenma, duk shi ne maigidanmu da sauransu. Dan a maza cikin Kannywood, ba a yi wanda nake so kamar shi ba.
Ko kana da waɗanda za ka gaisar?
A ƴ an fim zan yi musu jimlatan gabakiɗaya ina gaida kowa da kowa fatan alkhairi, Allah ta’ala ya cikawa kowa burinsa na alkhairi.
Muna godiya
Ni ma na gode.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Jarumar Fina finan Kannywood Kannywood wannan fim ɗin
এছাড়াও পড়ুন:
Sarkin Ruman Katsina ya rasu
A yau Litinin Allah Ya yi wa Sarkin Ruman Katsina kuma Hakimin Batsari, Alhaji Tukur Ma’azu, rasuwa.
Marigayin, wanda ya shafe shekaru 74 a duniya, ya daɗe yana fama da jinya gabanin rasuwarsa.
Hisbah ta kama masu safarar mata zuwa Saudiyya a Kano Jariri ya mutu a bayan uwarsa yayin tsere wa ’yan bindiga a NejaAlhaji Tukur wanda ya shafe shekaru 43 yana riƙe da sarautar Hakimin Batsari, ya rasu ya bar mata biyu, ’ya’ya da kuma jikoki.
Za a gudanar da jana’izarsa da misalin ƙarfe 4:30 na yammacin yau a gidansa da ke cikin garin Batsari, kamar yadda sanarwa daga iyalansa ta tabbatar.