Benin ta fitar da sammacin kama dan fafutuka Kemi Seba
Published: 13th, December 2025 GMT
Gwamnatin Jamhuriyar Benin, ta fitar da sammacin kame dan fafatukar nan Kemi Seba da ya shahawa wajen kalubalantar siyasar faransa a kasashen Afrika.
Matakin dai an zuwa ne kasa da mako guda bayan yunkurin juyin mulki da aka yi wa Shugaba Patrice Talon, wanda ya girgizar kasar.
Kotun Jamhuriyar Benin ta bayar da sammacin kama, Kemi Seba da Sabi Sira Korogone, shugaban kungiyar ‘Yantar da Jama’a (MPL), bisa zargin goyan bayan ayyukan ta’addanci” da kuma “tunzura mutane su yi bore.
Mutanen biyu za su iya fuskantar hukuncin daurin shekaru biyu zuwa biyar a gidan yari da kuma tarar miliyan goma na CFA, a cewar wata majiyar shari’a.
Shi dai Kemi Seba, ya fitar wani bidiyo a ranar 7 ga Disamba inda ya yi murna da yunkurin juyin mulkin da aka yi wa shugaba Patrice Talon.
A cikin bidiyon, dan fafutukar ya yi nuni da wani yunkuri na farko da za a iya maimaitawa idan shugaban kasar bai sake duba ayyukansa ba, wanda hakan ya haifar da fushi daga hukumomi.
A lokaci guda kuma, an kama Candide Azannaï, tsohon Ministan Tsaro kuma babban jigo a jam’iyyar adawa, a safiyar Juma’a a Cotonou.
An kama shi ne a hedikwatar jam’iyyarsa, inda ‘yan sandan shari’a ke yi masa tambayoyi.
A yanzu haka, ba a fayyace ainihin dalilan kama shi ba. Duk da haka, Azannaï ya nisanta kansa daga juyin mulkin da bai yi nasara ba na ranar 7 ga Disamba.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Majalisar Dinkin Duniya Za ta Yi Zama Da Bangarorin Da ke Yaki A Sudan December 12, 2025 Birtaniya Ta yi Barazanar Yanke Gudunmawar Da Take Bawa Kotun Duniya December 12, 2025 Iran Ta soki Kasashe Masu Karfi Na Bawa Isra’ila Dama Ta Musamman Wajen Kai Hare-hare December 12, 2025 Shuwagabannin Kasashen Iran Da Iraqi Sun Tattauna A Wajen Taron Zaman Lafiya A Kasar Turkmanistan December 12, 2025 Kungiyar NLC A Najeriya Ta Shirya Zanga-Zanga Kan Matsalar Rashin Tsaro A Fadin Kasa December 12, 2025 Duniyarmu A Yau: Iran Da Kokarin Juyin Mulkin Amurka A Yakin Kwanaki 12, Wa Ya Sami Nasara? December 12, 2025 Pezeshkian: Duniya Tana Bukatar Amintaccen Madogara, Zaman Lafiya Da Kuma Hadin Kai December 12, 2025 Iran Zata Dauki Bakoncin Taro Dangane Da Kasar Afganistan Da Tsaron Yankin December 12, 2025 Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Amince Ya Ziyarci Beirut December 12, 2025 Islami: Yaki Ba Zai Hana Iran Ci Gaba A Shirinta Na Makamashin Nukliya Ba December 12, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaban Iran Ya Isa Astana Babban Birnin Kazakhstan
Shugaban Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Dr. Masoud Pezeshkian, ya isa babban birnin Kazakhstan, Astana, bisa gayyatar takwaransa na Kazakhstan.
Mataimakin Firayim Minista na Kazakhstan ya tarbi Shugaba Pezeshkian a filin jirgin saman Astana. Wannan ziyarar ta zo ne bisa gayyatar shugaban Kazakhstan, wadda ke da nufin yin tattaunawa ta musamman tsakanin kasashen biyu.
A daya bangaren kuma Jakadan Iran a Moscow, Kazem Jalali, ya sanar da shirin ganawa tsakanin Shugaban Iran Masoud Pezeshkian da Shugaban Rasha Vladimir Putin a Turkmenistan.
Wannan ya zo ne a lokacin ziyarar da Putin ya shirya kaiwa zuwa Ashgabat a ranakun 11 da 12 ga Disamba don halartar wani taron tunawa da Ranar Zaman Lafiya da Aminci ta Duniya.
Kasashen Iran da Rasha dai sun kara bunkasa harkokinsu an tsaro da ayyukan soji a cikin watannin baya-baya nan, duk da cewa akwai tsohuwar alaka ta soji a tsakanin kasashen biyu, amma dai a halin yanzu alakar tana samun ci gaba a cikin sauri da ba a taba ganin irinsa ba, wanda kuma ake ganin hakan ba zai rasa nasaba da irin halin Rashin tabbas da ake ciki yankin ba, inda kasashen biyu kawayen juna suke yin aiki kafada da kafada domin tukarar duk wani kalubale.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka ECOWAS ta bukaci waware batutuwa na siyasa ta hanyoyin lumana a yammacin Afirka December 11, 2025 Reuters: Amurka na matsa lamba kan kotun ICC don janye bincike kan yakin Gaza da Afghanistan December 11, 2025 Ghana ta yi Allah wadai da cin mutuncin ‘yan kasarta da ke balaguro a Isra’ila December 11, 2025 Sakamkon Jin Ra’ayi: Yawancin Amurkawa na adawa da kai hari kan Venezuela December 11, 2025 Hamas Ta yi Tir Da Sabbin Matsugunan Yahudawa Da Isra’ila Ke yi A Yankunan Da Ta Mamaye December 10, 2025 Kasashen Nijeriya Da Saudiyya Sun Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar Tsaro Ta Shekaru 5 December 10, 2025 Shugaban Kasar Iran Yace Mata Su ne Ginshin Gina Makomakar Kowacce Kasa December 10, 2025 Iran Ta yi Tir Da Kisan Karen Dangin Isra’ila A Gaza A Ranar Yaki Da Kisan Kiyashi Ta MDD December 10, 2025 Borkina Faso Ta Saki Sojojin Sama Na Najeriya 11 Da ta Kama Bayan Jirginsu Yayi Saukar Gaggawa. December 10, 2025 Hamas Ta yi Tir Da Sabbin Matsugunan Yahudawa Da Isra’ila Ke yi A Yankunan Da Ta Mamaye December 10, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci