HausaTv:
2025-12-12@12:13:20 GMT

Islami: Yaki Ba Zai Hana Iran Ci Gaba A Shirinta Na Makamashin Nukliya Ba

Published: 12th, December 2025 GMT

Shugaban hukumar makamashin Nukliya na kasar Iran Mohammad Islami ya bayyana cewa, kasar zata ci gaba a fannonin ilmi guda 6 na fasahar nukliya wato Fission, Fussion, Lasers, fasahar Quantum, da kuma Plasma duk tare da barazanar yaki, ko na siyasa ko kuma yakin kwakwalwan da makiya suke wa kasar.

Yace, matsayin  JMI a bayyana yake, kan cewa ba zata daina aikin ci gaba a fannonin ilmin makamashin nukliya don samun ci gaba a bangarorin kiwon lafiya da magunguna ba da wasu bangarorin ci gaba ba.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Islami yana fadar haka, a wani bukin kaddamar wasu sabbin kayakin aikin wadanda aka samar a cikin gida wadanda suka hada da ‘Plasma-Based drug synthesis da kuma wani sabon na’ura na jinyar gulando da fasahar Plasma jets.

A ranar 22 ga watan yunin da ya gabata ne gwamnatin kasar Amurka ta kaddamar da hare-hare kan cibiyoyin makamashin nukliya na kasar Iran dake Fordo, Natanz da kuma Esfahan da kawo karshen shirin a kasar, sannan ta yi haka ne a dai dai lokacinda Iran take tattaunawa da ita.

Muhammad Islami ya karada cewa kasar Iran zata ci gaba wajen bunkasa ilmin masu amfani ga kasar ba tare da wata matsala ba, ya ce, luguden wuta a kan cibiyoyin nukliyar kasar ba zasu tsada wannan ci gaban ba, haka ma yaki da takurawa ta tattalin arziki, siyasa da sauransu.

Yace mutanen kasar Iran ba zasu ci gaba da zama masu sayan ilmi daga waje ba. Musamman ilmomi masu muhimmanci ga ci gaban mutanemmu a wannan zamanin.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Za A Yi Manyan Zabuka A Kasar Habasha A Watan Yuni Na 2026 December 12, 2025  Turkiya A Shirye Take Ta Aike Da Sojoji Zuwa Yankin Gaza December 12, 2025 Kremlin: Putin Ya Bayyana Wa Shugaba Maduro  Na Venezuela Goyon Bayansa December 12, 2025 Ben Gafir Ya Sha Alwashin Rushe Kabarin Sheikh Izzuddin Alkassam December 12, 2025 Maduro: Amurka Ta Bude Sabon Salon Fashi Akan Doron Ruwa December 12, 2025 Ayatollah Khamenei : Iran na samun ci gaba duk da kalubale da dama December 11, 2025 Kyaftin Traoré : Yau Burkina ta zama misali a duniya December 11, 2025 Iran da Kazakhstan Sun rattaba hannu kan yarjeniyoyi da dama December 11, 2025 Hamas : Isra’ila ta gaza cika alkawarin da ta dauka kan yarjejeniyar tsagaita wuta December 11, 2025 Kasashen ECOWAS sun rage kudin sufirin jiragan sama a tsakaninsu   December 11, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnonin Arewa Sun Yi Rawar Gani A Kafa Gidauniyar Fuskantar Matsalar Tsaro

A nan za mu iya cewa, wannan zunzurutun kudaden da za su tara har Naira biliyan 19 a wata daya, ya zama wajibi alummar yankin su sauya, na dakile matsalar domin kuwa, ‘yan Nijeriya, sun gaji batun ana tara dimbin kudade, domin magance wata matsala a kasar, amma daga, a karkatar da su, zuwa wata sabga, ta da ban.

Kazalika, batun ba wai kawai na tara wadannan zunzurutun kudaden ba ne, amma babbar ahaure’yan ambayar a nan ita ce, shin wa zai tafiyar da wadanda kudaden ? kuma shin, takamai-mai, wacce daga cikin matsalar ta tsaron, za a tunkarar? ta yaya za a kashe kudaden tare da fayyace yadda aka kashe su?

Matukar gwamonin, ba su bayar da wata gamsasshiyar amsar wadannan tamaboyin ba, wannan Gidauniyar, za ta kasance a cikin shakku, wadda za ta kasance wata hanya ta arzurta ‘yan Kwangila da kuma wasu da za a dauko, a matsayin mutanen tuntba, inda su kuma alumomin da ya kamata, magance masu kalubalen, za su ci gaba kai Gawarwakin ‘yanuwansu, makabartu, suna bizne su, saboda ci gaba da hare-haren na ‘yan bindiga.

Bugu da kari, Gwamonin sun bukaci da a dakatar da hakar ma’adanai, har na tsawon watanni shida, duba da cewa, hakar na’adanan, ta haramtacciyar hanyar, ta kasance tamkar wata hanya, samun kudaden ga ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda.

Alumomin da ke a jihohin Zamfara, Kaduna da Neja, sun ci gaba da fuskantar ‘yan bindiga da kuma’yan ta’adda bakin haure, ke kutsawa cikin alumomin da ke a wadannan jihohin suna hana su, kwanciyar hankali, tare da gindaya masu haraji.

A yanzu, Gwamonin na son ganin an tsaftace fannin na hakar ma’adanai ta hayar bayar da lasisi.

A nan, za a iya cewa, dakatawar ta watanni shida, ba ta wadatar ba, domin har yanzu, wasu na ci gaba da gudanar da ayyukan, ta haramtacciyar hanya.

A saboda haka, ya zama wajibi Gwamonin, su bukaci Ma’aikatar Hakar Ma’adanai ta Tarayya da ta sanar da su, ainahin kamfanonin da suka mallaki lasisin hakar ma’adanai tare da kuma wadanda suke amfana da fannin.

Hakazalika, akwai bukatar jihohin su samu cikakkun bayanan sirri, kan ayyukan da a ke gudanarwa, ba hakar ma’adanai a jihohin su da alumomin da abin ya shafa, inda kuma alummar, na ‘yancin su fada ko har yanzu, ana ci gaba da gudanar da ayyukan a yankunan su.

Kazalika, gungiyay ta kuma goyi bayan kafa ‘yansanda na jihohi, inda shi kasansa, wannan batun ke da bukatar, a yi dogon nazari a kai.

A bisa tunaninsu, kirkiro da ‘yansandan na jihohi, ita ce, hanya daya tilo, za a iya magance kalubalen rashin tsaro

Abu daya da takardar sakamakon taron ba su ta tsalle shi ne, shin a ta yaya ne, yankin ya tsinci kasansa, a cikin wannan matsalar ta rashin tsaro.

Gwamonin su kuma mika ta’aziyyarsu ga shugaba Bola Tinubu da kuma kokarin da yake ci gaba da yi, na tabbatar da tsaro, amma sun gaza yin dubi ga batun cin hanci da rashawa da yin tunani kan yadda ‘yan bindiga da kuma’yan ta’adda, ke ci gaba da aikata ta’asarsu, a cikin alumomi ba.

A nan za mu iya cwa, batun ya fi karfin tara kudade da damar da kayan aiki, amma dole ne, Gwamnonin su fuskanci gaskiya, musamman kan gazawar iya shugabanci wadda ta bayar da damar samun matsalar ta rashin tsaro.

Ya zama wajibi, Gwamnonin su yi dubi kan yadda ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda ke watayawarsu a cikin alumma tare da kakkafa sansanoninsu su kuma kai hare-harensu, ba tare da a far masu ba.

Batun na tara Naira biliyan 228 a shekara, batu ne da ya wuce maganar fitar da sanarwa ga kafafen yada labarai, amma sakamko na gari, shi ne ake bukata.

Shin dalibai a jihar Zamfara, za su iya zuwa makarantunsu na Boko, ba tare da jin wani tsoro ba? Manoma a jihar Kaduna, za su iya zuwa su iya komawa ci gaba da noma gonaksnu ba tare da wata fargaba ba? Matafiya za su iya bin babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna ba tare da ‘yan bindiga sun kai masu hari ba?

Gwamnonin sun dauki matakai da dabaru na zuba kudade domin tunkarar kalubalen na rashin tsaro.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Katsina Ta Amince Da Bayar Da Alawus Na Naira 30,000 Duk Wata Ga Malaman Karkara December 11, 2025 Manyan Labarai EFCC Ta Kama Tsohon Gwamnan Anambra Chris Ngige A Abuja December 11, 2025 Manyan Labarai Rikicin PDP Ne Ya Sanya Ni Komawa Jam’iyyar Accord – Adeleke December 11, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnonin Arewa Sun Yi Rawar Gani A Kafa Gidauniyar Fuskantar Matsalar Tsaro
  • BUA ya tallafa wa ɗaliban Sakkwato 200 da miliyan 40
  • Ayatollah Khamenei : Iran na samun ci gaba duk da kalubale da dama
  • Dakarun IRGC 3 Sun Yi Shahadi A wani Harin Ta’addanci A Kudancin Kasar Iran
  • Hamsa: HKI Tana Ci Gaba Da Keta Bangaren Farko Na Yarjeniyar Tsagaita Bude Wuta A Yankin
  • Iran Ta Yi Tir Da Yanke Tallafin Da MDD Take Bawa Yan Gudun Hijiran Afganistan
  • Shugaban Kasar Iran Yace Mata Su ne Ginshin Gina Makomakar Kowacce Kasa
  • Iran Ta yi Tir Da Kisan Karen Dangin Isra’ila A Gaza A Ranar Yaki Da Kisan Kiyashi Ta MDD
  • Sakkwatawa na murnar kisan da sojoji suka yi wa mataimakin Bello Turji