2025-12-12@09:47:33 GMT
إجمالي نتائج البحث: 17

«Annabi SAW ya ce»:

    Annabi Ibrahim ne ya fara kafa massallaci ya fara tsaida sallah, wadannan salloli na Ikamu da muke yi Annabi Ibrahim ya fara, Annabi Ibrahim ya fara canza a yi layya dabba maimakon dan Adam, saboda darajar da dan Adam yake da ita wajen Allah. Ya kawo tsarin a bar layya da mutane a yi da dabbobi da abubuwa da yawa, sai dai wadannan malamai na wannan lokaci ba su yarda wani ya yi tunanin wani ilmi a waje ba, saboda suna tsoron kar ya yi wani tunani da ya fi nasu, don haka jama’a kar mu ji tsoron wani ilimi, babu wani ilimi da Annabi bai zo da shi ba, amma har yau wanda ba su san ilimin ba suna...
    Manzon Allah (S.A.W.) yana da tunani mai zurfi, tunanin nan har ya shigar da shi duniyar tunani, duniyar tunani ta zamar masa gaskiya har yana tu’ammali da duniyar tunani, in ji mai wannan littafin masanin falsafa. Manzon Allah (S.A.W.) cikin gaskiya ya shiga ya yi tafakkuri, ya ya ibada, ya yi zikiri har ya koma asalinsa har ya haɗu da haƙiƙarsa ta Muhammadiyya (S.A.W.). Wata rana Annabi yana sallah a nan inda yake da Sahabbai, ya ce ga Al’janna ina kallo ga kuma wuta nan ina kallo, kai dai ba ka ji zafinta ba. Manzon Allah (.S.A.W.) yana da tunani mai zurfi, yana da yalwar tunani da ƙarfi, kai har abin da ƙwaƙwalwarsa take shirya masa sai ya zama gaskiya,...
    Saboda haka mu saki ilimi, mu ba ilimi hanya kar mu ji tsoro, mu je mu nemo shi duk inda yake kayanmu ne. Manzon Allah ya ce “ilimi hikima ce kayan mumini ne, saboda haka kar ka ji tsoro, ba wanda ya fi karfin Allah, ba wanda ya fi karfin Manzon Allah (S.A.W.). saboda haka ba wanda zai je ya shiga halwa ko ya shiga wani tunani ko ya shiga kaza har ya zo “summa dana fatadalla”, ba wanda zai zo nan sai dai Manzon Allah (S.A.W.). Dan haka Sufaye ba sa jin tsoron ko waye zai yi maganar ilimi, ba sa jin tsoron ko wane littafi bare damuwa, haka kuma ba a iya kada su, saboda duk abin da...
    Hakazalika, ta bai wa mata 30 masu kananan sana’o’i tallafin buhun gawayi, da kilo 10 na Shinkafa da litar man girki.   Bugu da kari, ga kungiyoyi shida na mata manoma, kowacce za ta karɓi fanfunan feshi, famfun ruwa, da kuma maganin feshin ciyawa.   Hajiya Shema’u, ta yaba da karuwar adadin mata a harkar noma, inda ta ce, manoma mata da suka yi rajista da NAWIA a yanzu sun haura 2000, yayin da wadanda ba su yi rajista ba sun kai 5,000.   Shemau ta kuma mika godiyarta ga Uwargidan gwamnan jihar Zamfara, Hajjiya Hurriya Dauda bisa namijin kokarin da take yi na bunkasa noman mata a Jihar Zamfara.   Sauran hukumomin da kungiyoyin da suke tare da NAWIA...
    Kudubi yana tare da kwayar zarrar kowace halittar Allah, shi yake isar mata da sakon magana, wanda bai zauna da wadannan mazaje ba sai ya ji magana ce mai girma, sai ya ga kamar an maida shi Allah, ya ce mai aka bar wa Allah ragowa, abun ba haka yake ba, abun mammaki da mai fadar wannan yana da wayewar da yake ganin fina-finai na Turawa, da ya ga wannan magana kai-tsaye a sarari. Misali a kan Kudubi, Turawa suna da wani fim da suke shiryawa na Dirakula (Dracula) wani mai shan jini, abun kamar tatsuniya ce suke shiryawa, amma wani ya ce an yi fada ne da Daular Usmaniyya, wato daular Turkiya, akwai abubuwa da ya ba su tsoro...
    Ƙungiyoyin Musulmi maza da mata da ƙananan yara daga sassa daban-daban na Jihar Oyo sun gudanar da bukukuwan zagayowar ranar haihuwar fiyayyen halitta, Manzon Allah Annabi Muhammad (SAW), na bana (shekara ta 1447 bayan hijira). Aminiya ta ruwaito cewa an fara gudanar da bukukuwan ne a ranar Asabar daga harabar babban Masallacin Unguwar Sabo, mazaunin Hausawa a Ibadan, babban birnin Jihar Oyo. Khalifofin mazhabobin Darikun Tijjaniyya da Ƙadiriyya a Ibadan su ne suka jagoranci manyan malaman addinin Musulunci tare da dimbin mabiya wajen yin tattaki na tsawon kilomita 10 da ya zagaya wasu sassan birnin domin nuna farin ciki da murnar wannan rana. An ga ƙungiyoyin Musulmi daban-daban masu halartar zagayen Maulidi sanye da sutura iri ɗaya (amko) suna rera...
      “Kowace ranar 12 ga watan Rabi’ul Auwal rana ce ta murnar zagayowar ranar haihuwar Manzonmu mai albarka (SAW).   “Wannan lokaci ne mai kyau da ya kamata dukkan Musulmi su yi koyi da rayuwar Manzon Allah (SAW).   “Musulunci ba addini kawai ba ne, hanya ce ta rayuwa, rayuwar Annabi (SAW), ta shiryar da mu zuwa ga kyawawan ɗabi’u, halaye da ayyuka.   “Ya kamata mu yi amfani da irin waɗannan muhimman lokuta na addini domin mu dage da addu’o’in samun zaman lafiya a Jihar Zamfara, Arewa maso Yamma, da ƙasa baki ɗaya.   “Allah (T) ya kawo mana ƙarshen ta’addanci da duk wani nau’in aikata laifuka a cikin al’ummarmu.” Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun...
    Sannan Annabi (SAW) ya ce “Babu wata rana mafificiya a wajen Allah kamar Ranar Arfa”, haka nan kuma ragowar kwanakin da ke cikin 10 na farkon watan nan, Ranar Arfa ta ninninka su falala. Don a wannan ranar ce Annabi (SAW) ya ce Ubangiji yana sauka zuwa saman duniya (Kamar yadda ya dace da Shi (SWT). Ire-iren waɗannan Hadisan ne ake ce musu “Mutashabihai”. Ana kawo bayanansu ne ta yadda za a yi mana kwatance amma ba kamar yadda ma’anar lamarin yake a hulɗar da ke tsakaninmu ba. Wajibi ne yin imani da Hadisan don rashin yin imani da su ridda ne, amma ba kuma a riƙa fassarawa da yadda ƙananan ƙwaƙwalenmu ke ɗaukawa ba. Duk wanda ya ce zai...
    Ma’anar addu’ar ita ce, “Allah ina neman tsari da kai, ya Ubangiji mai girma, da hasken fuskarka (yadda ya dace da shi) mai girma, da sarautarka dauwamammiya, daga shaidani abin jefewa, da sunanka Allah, Allah ka yi salati ga Annabi Muhammad (SAW) da ‘ya’yan gidansa, ka yi aminci a gare shi. Allah ka gafarta mun zunubina, Allah ka bude mun kofofin rahamarka.” Ba a Harami ba kawai, a kowane Masallaci an so a karanta daga kan salatin Annabin nan zuwa karshen addu’ar idan za a shiga. Idan mutum bai iya wannan addu’ar ba, ya yi a’uziyya da bisimillah da salatin Annabi (SAW) da kuma addu’ar da ya iya. Ana so da zarar mutum ya shiga idanunsa sun kalli Dakin Ka’aba,...
    Amma an fi so a yi da Rakumi ga wanda yake da iko. A Aikin Hajji, an fi son yawan nama sabanin Layya da aka fi son nama mai dadi da kitse. Shari’a ta yarda mutum bakwai su hada kudi su sayi Rakumin hadaya guda daya. Idan Alhajin da hadaya ta hau kansa bai samu dabbar da zai yi ba, sai ya yi azumi na kwana uku a Makka kafin a fita zuwa Arfa idan zai yiwu. Idan bai samu dama ba sai ya yi bayan Arfa kafin ya bar Makka. Bayan ya dawo garinsu, sai ya yi sauran azumin kwana bakwai. Jimillar azumin kwana 10 ne yake madadin hadayar da bai yi ba. Amma kuma kar ya zama Alhaji...
    –Ya Kamata Malamai Su Karfafa Zamantakewa Ta Wayewar Musulunci A Duk Inda Musulmi Suke   Assalamu alaikum wa rahmtullahi ta’ala wa barkatuh, ya Shehunmu da sauran daukacin Bayin Allah, muna mika sakon gaisuwa da kuma ziyara ta ‘yan’uwantaka ta Musulunci a dukkanin matakai da Annabi (SAW) ya zo mana da shi na Musulunci da Imani da kuma Ihsani. Bayan haka, muna godiya da irin bayanin da aka yi mana a karatunka na Tafsiri na rana ta 11 a game da muhimmancin karfafa zamantakewa ta wayewar Musulunci a tsakanin Musulmi a duk inda suke. Tabbas, lokaci ya yi da masu wa’azin Musulunci ya kamata su daina kafa hujjar yaki da ayoyin Surar Bara’a a wuraren da ba su dace ba, domin akwai...
    Shi wannan azumi, na wani lokaci ya fi na wani lokaci kamar an so a dinga yin azumi sau Uku a cikin kowanne wata, lokacin kwanan wata yana 13 da 14 da 15, wannan kwanaki hasken wata ya fi haske a cikinsu, to kamar yadda suke haske haka zuciyarka za ta kara haske sabida saduwa da hasken, sannan kuma hawa-hawa na musulunci guda Uku ne (Islam da Iman da Ihsan) to wanda ya riski wannan kwanaki Uku kamar Ya hau dukka wannan Matakan addinin ne. Akwai azumin Litinin da Alhamis, azumin ranar Litinin Annabi (SAW) ne yake yi, an tambaye shi cewa Ya Rasulullahi sabida me kake azumin ranar Litinin? sai ya ce ranar ce aka haife ni, ina godiya...
      Jinkirta Sahur Da Gaggauta Buda-baki An karba daga Anas, ya ce, Annabi SAW ya ce “ku dinga yin Sahur, domin shi yin Sahur akwai albarka a cikinsa”, ba burgewa ba ce mutum ya dinga cewa ‘ai ni ban yin sahur’ albarka mai yawa ta wuce shi. An karba daga Sahlu dan Sa’adu Allah ya kara yarda da shi ya ce, Manzon Allah (SAW) ya ce “Mutane ba za su gushe ba cikin alkairi muddin sun gaggauta yin buda-baki” Ma’anar wannan hadisi, sabida Allah ya fada cikin Alkur’ani “summa atimmus siyama ilallai – sannan ku cika azumi zuwa dare” sai Annabi ya koya mana sunnarshi zuwa dai-dai lokacin da ya dace na buda-bakin (ba cikin dare Allah yake nufi ba),...
    Annabi (SAW) yana da Alfadarai Bakwai, akwai wazanda ya rike har ya rasu suna wurinsa akwai kuma wazanda ya bai wa wasu daga cikin sahabbansa. Wacce ya je yakin Hunaini da ita, wani sarkin Larabawa (zan makafatul kinani) ne ya bashi, akwai wacce sarkin Ailatu ya bashi akwai ta sarkin Limatul Jandali, akwai ta Sarki Najjashi, akwai ta sarkin Kisra, akwai ta sarkin Mukaukisu akwai Jindilu. Jindilu itace mashhuriya wacce Annabi ya rasu ya bar ta Sayyidina Aliyu ya ci gaba da hawanta, duk yakukuwan Sayyidina Ali, mafi yawancinsu a kanta ya yi, ranar yakin Wak’atu Jamal, Sayyada A’isha (RA) ta ganshi a kanta, sai ta ce “ya yi kama da zan’uwansa” sai mai rike da akalar rakuminta ya jefar...
    Annabi (SAW) a cikin dukkan kyawawan halaye ba a kamanta shi da kowa. Jabir dan Abdullahi (RA) yana cewa, ba a tava tambayar Annabi (SAW) da wani abu ba ya ce babu. Abdullahi dan Abbas (RA) yana cewa “Annabi (SAW) ya kasance mafi baiwar Mutane da alkairi, lokacin da Annabi ya fi baiwa, shi ne lokacin watan Azumin Ramadana, ya kasance idan ya hadu da Mala’ika Jibrilu, Mala’ika Jibrilu yana zuwa suna Musaffan Karatun Alkur’ani da Annabi (SAW) duk watan Ramadana sau daya, sai shekarar wafati ce suka yi sau biyu. Shi ya sa, duk musulmai suna da baiwa da kyauta amma in watan Ramadana ya zo sai ka ga sun kara ninkawa. An karvo hadisi daga Anas khadimin Manzon...
    In an taba rarrauna a gabanka, kana da ikon kare masa, to ka kare masa, kin kare masa sakaci ne ba hakuri ba ne. An ruwaito cewa, Annabi (SAW) bai taba dukan wata daga cikin Matansa ba ko kuma cikin masu masa hidima a gida ko a waje. An kama wani Mutum da yake shirin kashe Annabi (SAW), aka gurfanar da shi gaban Annabi (SAW), sai jikinsa ya fara makyerkyata, Annabi (SAW) ya ce masa, kar ka firgita, ko da ka yi niyyar kashe ni, Allah ba zai dora ka a kaina ba. Zaidu dan Sa’anatal Yahudi ya zo wurin Annabi (SAW) kafin ya Musulunta yana neman Annabi (SAW) ya biya shi bashin da ya karba a wurinshi. Sai ya...
    Shi hakuri, ana nufin halin nutsuwa, in wani abu ya tayar maka da hankali amma a ga mutum cikin nutsuwa da kuma tabbata a kan nutsuwa lokacin da wasu abubuwa da ba makawa in aka yi wa mutum sai sun hargitsa shi amma ya dake a gan shi cikin nutsuwa bai yi fushi ba. Ita kuma juriya cikin dauke bala’o’i, ita ce tsare rai cikin rashin damuwa lokacin da ake cikin tsananin damuwa, mutum ya nuna kamar abu bai faru ba. Ita kuma yafiya ko rangwame, ita ce barin ramuwa ga wanda ya yi maka ba daidai ba. Dukkan wadannan halaye, suna daga cikin wadanda Ubangiji ya ladabtar da ma’aikinsa (SAW) da su. Ubangiji yana fada masa a cikin hakkinsa...
۱