Dan sanda ya yi batan dabo a bakin aikinsa a Katsina
Published: 12th, December 2025 GMT
Wani dan sandan mai suna Ahmed Tukur ‘Yantumaki ya yi batan dabo yayin da yake a bakin aikinsa a Babban Ofisishin ‘Yan sanda na Karamar Hukumar Danmusa da ke Jihar Katsina.
Bayanai sun nuna cewa, a ranar 25 ga watan Nuwamba, 2025 jami’in ya je bakin aiki inda ya ajiye jikkarsa da kular abincinsa a ofishinsu da ke cikin garin Danmusa sanna ya sanya hannu a kan rajistar kama aiki ta wannan rana, kuma ya nemi izni ya fita da nufin zai je ya sawo wani abu waje.
Da Aminiya ta tuntubi mahaifinsa mai suna Malam Tukur ‘Yantumaki don jin ta yadda ya samu labarin batan dansa sai ya ce, shi ma sai bayan kwana biyu da faruwar lamarin ne ‘yan sanda suka fada masa.
Malam Tukur ya ce, “’yan sandan ne da kansu suka zo har nan cikin gidana a karkashi jagorancin Babban Jami’in ‘Yan sanda na Karamar Hukumar Danmusa, DPO Isah Sule. Kuma shi ne ya fada min cewa, dana ya je aiki kwana biyu da suka wuce ya ajiye kayansa sannan ya sa hannu ya fita waje da nufin zai sawo wani abu amma ba a sake ganinsa ba.”
Ya ci gaba da cewa, “ya kuma bayyana min cewa, suna bakin kokarinsu don ganin sun gano shi don haka mu taya su da addu’a kuma mu sauke Alkur’ani. Ya kuma bayyana min cewa, sun yi ta kiran wayoyinsa amma ba sa samun, saboda duk wayoyin dana a kashe suke, sun ce, kuma duk lokacin da suka yi kokarin tirakin din layikansa sai na’urar binciken ta nuna masu ba ta iya ganin inda yake.”
Da yake wa Aminiya karin bayani yayan jami’in dan sandar da ya bata mai suna Ibrahim Tukur ya ce, “tun ranar da suka zo suka fada mana zancen batansa har yau babu wanda ya sake tuntubarmu game da zancen. A namu bangare, mun yi kokarin sanya labarin batansa a kafafen sada zumunta kuma mun samu wasu manyan don su taimaka mana su yi wa Kwamishinan ‘Yan sanda naJihar Katsina bayanin halin da ake ciki. Kuma muna nan muna kara jira mu ji bayanan da za su dawo mana das u tunda yake sun yi alkawari taimakawa.”
A cikin damuwa mahaifin dan sandan da ya bata wanda tunanin abin day a faru da dansa ya sa rashin lafiya ta kama shi yana kwance ya sheda wa Aminiya cewa, “ ina kira da babbar murya ga Gwamna Jihar Katsina Dakta Dikko Radda da Kwamishinan ‘Yan sanda na Jihar Katsina da su tabbatar sun gano min dana kuma sun dawo min da shi cikin ‘yan’uwansa lafiya, su tuna wannan hakki ne a kansu.
“Bai yiyuwa a ce, mutum kuma jami’in dan sanda da suka ce mana ma a lokacin da ya bace yana dauke da bindigarsa kuma a tsakiyar gari, wato tsakanin ofishin ‘yan sanda zuwa masallacin Juma’a ya bace kamar wata dabba. Ba duriyarsa ba kuma wani bayani gamsasshe ballanata kuma wani nuna damuwa daga bangarensu.”
Ya kara da cewa, “ba a gano inda yake ba, babu wanda ke yi min bayani game da inda yake, a gaskiya ma babu wanda ya nuna wata damuwa sosai daga bangaren gwamnati. Shin hakan yana nufin babu wanda ya damu da shi a matsayin dan sanda kuma babu wanda ya damu da mu a matsayinmu na talakawa? Shin haka kuwa labarin zai kasance idan da a bin ya faru da daya daga cikin ‘ya’yansu ne?”
Aminiya ta yi kokarin jin ta bakin jami’an ‘yan sanda na Jihar Katsina, inda ta farad a kiran DPO Isah Sule na Karamar Hukumar Danmusa amma hakan ya ci tura, domin layin wayarsa baya shiga sannan kuma bai bayar da amsar sakon da aka tura masa a waya ba.
Haka kuma Mai Magana da Yawun ‘yan sandar Jihar Katsina DSP Abubakar Sadik Aliyu wanda wakilin Aminiya ya tura wa sakon kart a kwana ba tare day a maido da amsa bat un jiya, daga bisani amsa kiran waya inda ya bayyana wa wakilinmu cewa, ya yi tafiya amma zai bincika yadda lamarin yake sannan ya yi bayani.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: babu wanda ya Jihar Katsina Yan sanda na yan sanda na
এছাড়াও পড়ুন:
Dalibin jami’a ya rasu a hatsarin motar murnar kammala jarabawa
Wani dalibin shekarar ƙarshe a Jami’ar Ambrose Alli da ke jihar Edo, ya mutu a wani hatsarin mota bayan shi da wasu dalibai sun yi jerin gwanon motoci domin murnar kammala jarabawar ƙarshe.
Aminiya ta samu labari a ranar Talata daga wani mai amfani da Facebook mai suna Inside Edo, cewa hatsarin ya faru ne a ranar Litinin jim kaɗan bayan daliban sun gama jarabawar ƙarshe. Sai dai ba a bayyana sunan dalibin ba.
DAGA LARABA: Ko Ziyarar Tawagar Amurka Za Ta Kawo Karshen Matsalar Tsaro A Najeriya? Iya sojojin da ke tsaron Seyi Tinubu sun isa su samar da tsaro a Benin – SoyinkaMajiyar ta ce motar ta yi ƙoƙarin wuce wata mota kafin ta kwace ta kuma daki wata babbar mota.
A cewar majiyar: “Wani mummunan hatsari ya faru a Ujoelen, kusa da makarantar firamare, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar wani dalibi da ya kammala karatu a jami’ar Ambrose Alli, Ekpoma.
“A cewar masu gani da ido, hatsarin ya faru ne yayin da aka yi yunƙurin wucewa da ɗaya daga cikin motocin da abin ya shafa.
“Wannan haɗarin ya jawo rasa iko, wanda ya haifar da mutuwar. Mazauna yankin da ke kusa sun ruga wurin, amma ba a iya ceto wanda ya jikkata ba.”
Haka kuma, Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa daliban sun kasance suna tukin mota cikin ganganci kafin su yi taho-mu-gama da wata babbar mota da ta tsaya a hanya.
An ce wanda ya rasu yana cikin jerin gwanon motocin da daliban da suka kammala karatu suka yi.
NAN ta ruwaito: “An ce yana cikin jerin gwanon sabbin daliban da suka shiga kan hanya a ranar Litinin jim kaɗan bayan bikin kammala makaranta.
“Lamarin ya faru ne lokacin da wanda ya rasu ya yi yunƙurin wuce wata babbar mota mai tafiya, amma ya buge da wata mota da ta tsaya a gefen hanya.”
Ƙoƙarin samun martani daga kwamandan sashe na jihar Edo a Hukumar Kiyaye Hadura ta Ƙasa (FRSC), Cyril Mathew, ya ci tura, domin lambar ba ta shiga har zuwa lokacin hada wannan rahoton.
Sai dai NAN ya rawaito daga baya Mathew ya tabbatar da lamarin, yana mai cewa mutum ɗaya ya mutu yayin da wasu biyar suka jikkata a hatsarin.
Ya ce: “Daliban, bayan sun gama rubuta takardar jarabawa ta ƙarshe, sun shiga hanya cikin jerin gwanon motoci.
“A cikin wannan yanayi, ɗaya daga cikinsu ya yi yunƙurin wuce wata mota, ya kuma buge da wata babbar mota da ta tsaya a gefen hanya,” kamar yadda NAN ya rawaito daga Mathew.