Yadda za ku nemi aikin jami’an lafiya a Hajjin 2026 da NAHCON
Published: 13th, December 2025 GMT
Hukumar Aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON) ta fara ɗaukar likitoci da sauran ma’aikatan lafiya domin aikin Hajji da ke tafe a ƙasar Saudiyya.
Hukumar NAHCON ta bayyana cewa shafin neman aikin ya fara aiki daga ƙarfe 11 na dare ranar Juma’a 12 ga Nuwamba, 2025. Za a rufe shafin da ƙarfe 11.59 ranar Litinin, 15 ga watan Disamba, 2025
Latsa nan domin shiga shafin ɗaukar ma’aikatan lafiyan kai-tsaye.
NAHCON ta bayyana cewa jami’an lafiyan da za a ɗauka Su ƙunshi likitoci, masu haɗa magunguna, malaman jinya, da jami’an kula da lafiyar lafiya da ta muhalli (CHO/EHO). Su ne za su yi aikin kula da lafiyar alhazai a yayin aikin Hajjin na shekarar 2026.
NAHCON ta bayyana cewa jami’an da suka yi aiki da ita a matsayin kula da lafiyar alhazai a shekaru uku da suka gabata (2023 zuwa 2025) ba ne kaɗai za a ɗauka domin wannan aiki na 2026.
Yadda za ku nemi aikinMasu nema za su shiga shafinta kai-tsaye domin ganin ka’idodin da kuma cike bayanansu. Latsa nan domin lafiyan kai-tsaye.
Ko kuma su gaida babban shafinta daga nan su latsa wasu layuka huɗu da ke hannun dama daga sama.
Daga daga nan su latsa RESOURCES, sai su latsa su shiga NMT Application Portal.
A ciki za su ga ka’idodin neman aikin, su cike bayansu, da kuma sauke duk dakardun da su cike.
Hukumar NAHCON ta bayyana cewa daga bisani za a tuntuɓi duk waɗanda suka yi nasara.
Allah Ya ba da sa’a.
Ka’idodin neman aikinNAHCON ta jaddada cewa:
– Ma’aikatan lafiya da suka cancanta ne kawai za su iya nema aikin ba Tawagar Lafiya ta Ƙasa (NMT) domin aikin Hajjin 2026
– Aikin NMT na 2026 zai gudana ne bisa tsarin sa-kai, bisa ƙa’idojin duniya da NAHCON ta amince da su.
– Bayanai da aka bayar za su taimaka wajen tantance cancanta da shirin shiga matakin gaba na tantancewa ko jarabawa.
– Duk bayanan da aka gabatar za a duba su. Duk wani kuskure. Ɓoye gaskiya, ko ƙirƙirar bayanan ƙarya zai iya jawo ƙin amincewa da aikace-aikacen ko cirewa daga jerin waɗanda cancanta.
– Wannan aikace-aikacen kyauta ne gaba ɗaya. NAHCON ba ta karɓar kuɗi kai tsaye ko a kaikaice, ko ta hannun wakilai ko hukumomi. Ku yi hattara!
– Cika fom ɗin ba ya nufin an amince da cancanta ko zaɓen ku.
Ƙa’idar shekaru:
– Likitoci: 27 zuwa 60 shekara
– Masu haɗa Magunguna: shekara 26 zuwa 60
– Nas da sauran rukuni: 22–60 shekara .
SharuɗɗaDole masu neman shiga NMT su kasance:
1. Suna aiki a lokacin neman shiga.
2. Ba su halarci ayyukan NMT a shekara uku da suka gabata ba (2023, 2024, da 2025).
3. Su kasance a shirye su yi aiki na tsawon kwanaki 28 da kuma zama a Saudiyya har zuwa kwanaki 45 kafin dawowa Najeriya.
4. Ba za a sallame su a wurin aikinsu ba kafin su kammala aikin NMT.
5. Su nuna kyawawan halaye tare da bin ƙa’idojin aikin lafiya da na NAHCON.
6. Su gabatar da tabbacin mai tsaya musu (guarantor).
Sharuɗɗan Guarantor:
– Dole ya kasance mutum mai daraja: Ma’aikacin gwamnati (ba ƙasa da GL 15), basaraken gargajiya, Alƙali (Magistrate), ko Shugaban Ƙaramar Hukuma.
– Dole ya san mai neman aikin NMT tsawon aƙalla shekaru biyar kuma ya tabbatar da gaskiya, ƙwarewa, da iya aikinsa.
– Dole ya gabatar da kwafin katin shaida ko wata takardar shaida da ake amfani da ita a ofisoshin gwamnati na Najeriya.
Takardun da dole a haɗa da su:
– Fom ɗin Guarantor da aka cika
– Takardar shaidar ƙwarewar aiki (Basic Professional Certificate)
– Takardar NYSC (idan ta shafi mai nema)
– Lasisin aikin lafiya na wannan shekara
– Hoton fasfo (mai farin baya)
– Sanarwar mai nema (applicant’s declaration)
– Takardar izini daga wurin aiki (employer’s clearance letter) .
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: jami an lafiya NAHCON ta bayyana cewa
এছাড়াও পড়ুন:
Iyaye Sun Yi Fitowar Farin Dango Don Yi Wa “Yayansu Allurar Rigakafi a Sule-Tankarkar
Daga Usman Muhammad Zaria
Aikin rigakafin watan Disamba a karamar hukumar Sule-Tankarkar ta jihar Jigawa ya samu gagarumar nasara, yayin da iyaye suka fito kwansu da kwarkwata domin tabbatar da cewa an yi wa ’ya’yansu cikakken rigakafi.
Wasu daga cikin iyayen da suka kawo ’ya’yansu domin karbar rigakafin yau da kullum da na shan inna sun bayyana jin dadinsu kan yadda aka gudanar da aikin cikin kwanciyar hankali.
Daya daga cikinsu, Malama Ummahani Danbala, ta ce an wayar da kan jama’a sosai ta hannun mata ’yan sa-kai a unguwarsu, inda aka karfafa gwiwar iyaye mata su kawo ’ya’yansu domin karbar rigakafin yau da kullum da na shan inna.
Malam Yunusa, wani mai sa ido a karamar hukumar, ya bayyana gamsuwarsa da yadda aka gudanar da aikin rigakafin a yankin.
A cewarsa, aikin wayar da kan jama’a ya yi matukar tasiri, domin mutane na kawo ’ya’yansu da kansu ba tare da kin amincewa da rigakafin ba.
Yunusa ya bayyana cewa duk da kasancewar karamar hukumar tana kan iyaka, aikin ya gudana cikin nasara, sakamakon hadin gwiwar da aka samu daga dukkan masu ruwa da tsaki.
Ya kara da cewa ana sa ran rigakafin yara kusan 45,221, inda aka yi niyyar kai rigakafin makarantu da wuraren ibada domin gano yaran da ba a musu ba.
Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa karamar hukumar na da cibiyoyin lafiya guda 28, kuma aikin rigakafin ya gudana cikin kwanciyar hankali a al’ummomin Ablasu, Kings, Amanda, Togai, Nagwamatse da Hannun Giwa.
Ana sa ran kammala zagayen rigakafin shan inna na watan Disamba a ranar Juma’a a fadin kananan hukumomi 27 na jihar Jigawa.