Babu wani hari da aka kai sakatariyar NUJ a Yobe — ’Yan Sanda
Published: 19th, September 2025 GMT
Rundunar ’yan sandan Jihar Yobe, ta ƙaryata rahotannin da ke nuna cewar an kai hari sakatariyar ƙungiyar ’yan jarida ta Najeriya (NUJ) da ke Damaturu.
Wannan na cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar a ranar Juma’a.
An cafke mutum 6 kan tono gawa a kabari don yin asiri a Gombe Wata mata ta ƙona al’aurar ’yarta da wuta kan zargin maita a BauchiKakakin rundunar, SP Dungus Abdulkarim, ya ce abin da ya faru shi ne wani jami’in tsaro da ke gadin wajen ne ya samu rauni a ƙafarsa ta hagu.
A cewarsa, raunin ba shi da alaƙa da harbin bindiga, kamar yadda wasu shafukan Internet suka wallafa.
Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 1:45 na daren ranar 19 ga watan Satumba, 2025.
Rundunar ta ce babu wani ɗan jarida ko ma’aikacin NUJ da aka kai wa hari ko aka yi wa barazana.
SP Abdulkarim, ya ƙara da cewa ana ci gaba da bincike kan lamarin, kuma ya bai wa jama’a tabbacin cewa za a ɗauki matakan da suka dace.
Rundunar ta kuma yi kira ga ’yan jarida da su guji yaɗa labarai ba tare da tabbatarwa ba, domin hakan na iya haifar da tashin hankali.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Jarida Yan Sanda hari rahotanni
এছাড়াও পড়ুন:
Matar aure ta yanka wuyan mijinta, ta fasa masa ido da wuƙa a Neja
An kama wata matar aure a garin Kuta, hedikwatar Karamar Hukumar Shiroro ta Jihar Neja, bisa zargin yankar wuyan mijinta, Salisu Suleiman, da wukar girki.
Majiyoyi sun ce matar ta kuma soka wa mijin wuka a idonsa na hagu, lamarin da ya lalata idon gaba ɗaya.
Wata majiya da ta nemi a ɓoye sunanta ta bayyana wa wakilinmu cewa ma’auratan sun samu saɓani ne, inda matar ta jira har sai da mijin ya kwanta barci kafin ta kai masa hari da wuƙa.
Kakakin ’yan sanda na Jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, ya ce lamarinya auku ne da safiyar Asabar, 1 ga Nuwamba, 2025.
A cewarsa, “A ranar 1 ga Nuwamba, da misalin ƙarfe 2:30 na asuba, wani Salisu Suleiman na garin Kuta ya samu saɓani da matarsa, Halima Salisu, inda da mijin ya kwanta barci, matar ta ɗauki wuƙa ta yankar masa wuya, sannan ta soka masa a idon hagu.”
SP Abiodun ya ce an garzaya da wanda abin ya faru da shi Asibitin Gabaɗaya na Kuta, daga nan kuma aka mayar da shi Asibitin Ƙwararru na IBB da ke Minna domin ƙarin kulawar likitoci.
Ya ƙara da cewa, “An kama wadda ake zargi, kuma tana tsare a hannun ’yan sanda domin ci gaba da bincike da kuma gurfanar da ita a gaban kotu.”