’Yan sanda sun kama mutane 5 kan zargin satar abincin yara a Borno
Published: 21st, September 2025 GMT
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Borno, ta kama mutum biyar da ake zargi da satar fakiti 7,871 na abincin yara, wanda aka fi sani da Tamuwa, wanda aka tanada don yara masu fama da cutar yunwa.
Kakakin rundunar, ASP Nahum Kenneth Daso ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar 19 ga Satumba, 2025 .
Ya bayyana cewa an gano kayan ne a samame guda biyu da aka kai a Maiduguri.
Shettima ya bar Abuja don halartar taron majalisar ɗinkin duniya a New York An sanya tukwicin N10m domin kama makasan limamin coci a EnuguSamamen farko ya auku ne a ranar 12 ga Afrilu, lokacin da aka tsayar da wata mota a Njimtilo, kusa da Maiduguri, inda aka gano fakiti 3,314 na Tamuwa, wanda hakan ya sa aka kama mutum biyu.
Haka kuma, a ranar 9 ga watan Yuni, jami’an tsaro sun tsayar da wata mota a Legacy Estate, Maiduguri, inda aka gano ƙarin fakiti 4,557.
Wannan ya kai ga kama wasu mutum uku da ake zargi.
ASP Daso ya ce: “’Yan sanda ba za su lamunci karkatar da kayayyakin agaji ba, domin an tanade su ne don ceton rayuka, musamman na marasa galihu.”
An miƙa kayan da aka ƙwato ga gwamnatin Jihar Borno, ta hannun Kwamishinan Lafiya, Farfesa Baba Mallum Gana, domin raba su yadda ya dace.
A halin yanzu, an gurfanar da mutane biyar da aka kama a gaban kotu domin fuskantar hukunci.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Sanda tamowa yara
এছাড়াও পড়ুন:
An sanya tukwicin N10m domin kama makasan limamin coci a Enugu
Gwamnatin Jihar Enugu ta tanadi tukwuicin naira miliyan goma ga duk mutumin da ya taimaka aka kama waɗanda ake zargi da kashe fitaccen limamin cocin Katolika, Matthew Eya.
Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa tabbatar da alƙawari da Kwamishinan Labarai, Malachy Agbo, ya fitar ranar a Asabar.
NAF ta hallaka Boko Haram 32 a Borno Jami’ar European-American ta musanta bai wa Rarara digirin girmamawaWasu ‘yan bindiga ne suka harbe Mr Eya, limamin cocin katolika ta Saint Charles Catholic Church da ke garin Eha-Ndiagu ranar Juma’a a kan hanyar Eha-Alumonah–Eha-Ndiagu da ke ƙaramar hukumar Nsukka.
Rahotanni sun ce ’yan bindiga sun yi wa limamin kwanton-ɓauna wanda suke harbe a yayin da yake kan hanyar komawa gida daga yankin Enugu Urban.
Limamin cocin mamba ne a Cocin Nsukka Catholic Diocese, wadda ta tabbatar da kisan nasa.
A sanarwar da Mista Agbo ya fitar, ya ambato gwamnatin Enugu tana “yin Allah wadai da kakkausar muryar” bisa “mummunan kisan” da aka yi wa limanin cocin.
“Gwamnatin Enugu tana miƙa saƙon ta’aziyyarta ga iyalan limanin cocin, da Catholic Diocese ta Nsukka, da kuma mabiya ɗarikar Katolika baki ɗaya bisa wannan iftila’i,” a cewar kwamishinan.
Ya bayyana makasan a matsayin “matsorata” waɗanda suka aiwatar da kisan “rashin imani”, inda ya sha alwashin cewa gwamnati za ta kama ‘yan bindigar da suka yi wannan aika-aika.