Sojoji sun kashe ’yan bindiga 3 a Binuwai
Published: 12th, December 2025 GMT
Dakarun Sojin Operation Whirl Stroke (OPWS), sun kashe wasu mutum uku da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, yayin wani samame da suka kai a Ƙaramar Hukumar Ukum, a Jihar Binuwai.
Mai magana da yawun OPWS, Laftanar Ahmad Zubairu, ya ce sojojin sun samu bayanan sirri kuma suka yi aiki tare da ’yan sandan Zaki-Biam.
Maharan sun kafa shinge a kan hanyar Aturuku–Wembe–Ayati, inda suke tare matafiya suna ƙwace musu kayayyaki.
Da sojoji suka isa wajen, maharan sai suka fara harbe-harbe, wanda hakan ya sa sojojin suka buɗe musu wuta.
Hakan ya yi sanadin mutuwar uku daga cikinsu, sauran kuma suka tsere cikin daji.
Dakarun sun ƙwato babura guda biyu, yayin da suka ci gaba da farautar waɗanda suka tsere.
Bincike ya nuna cewa mutanen da suka mutu suna cikin wata ƙungiya da ta daɗe tana yi wa al’umma barazana ta hanyar garkuwa da mutane da kai hare-hare, musamman kusa da kasuwar doyar Zaki-Biam.
Mutanen gari sun tabbatar da sunan waɗanda dakarun suka kashe.
Kwamandan OPWS, Manjo-Janar Moses Gara, ya yaba wa sojojin bisa ƙwazo da jarumtarsu, tare da alƙawarin ci gaba da kare al’umma da tabbatar da zaman lafiya.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Bindiga Binuwa hare hare
এছাড়াও পড়ুন:
Dakarun IRGC 3 Sun Yi Shahadi A wani Harin Ta’addanci A Kudancin Kasar Iran
Dakarun kare juyin juya halin musulunci a nan Iran sun yi musayar wuta da yan ta’adda a kudu masu gabacin kasar, sannan wasu daga cikinsu su sun yi shahada sannan sun halaka yan ta’adda da dama. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na JMI ya dakarun na IRGC guda uku nesuka yi shahada a wannan fafatawar, a jiya Laraba a garinLar da ke kusa da birnin Zahidan babban birnin Lardin. Garin Lar dai yana kan iyakar kasar Iran da Pakisatan, kuma ba wannan ne karon farko wadanda dakarun suke fafatawa da yan ta’adda wadanda suke samun goyon bayan kasashen waje ba. Kuma suke da sansanoninsu a cikin lardin sitan Baluchistan na kasar Pakistan ba.Har yanzun dakarun rundunar Qudus wanda suke aiki a karkashinsu basu bayyana sunayen sojojin da suka yi shahadar ba. Amma sun kaddamarda wata tawaga wacce zata gudanar da binciken gaggawa don gano abinda ya faru.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Hamsa: HKI Tana Ci Gaba Da Keta Bangaren Farko Na Yarjeniyar Tsagaita Bude Wuta A Yankin December 11, 2025 Iran Ta Yi Tir Da Yanke Tallafin Da MDD Take Bawa Yan Gudun Hijiran Afganistan December 11, 2025 Ansarallah: Dole Ne Kasar Yemen Ta Tsarin Musulunci Na Kaiwa Ga Daukaka December 11, 2025 Shugaban Iran Ya Isa Astana Babban Birnin Kazakhstan December 11, 2025 ECOWAS ta bukaci waware batutuwa na siyasa ta hanyoyin lumana a yammacin Afirka December 11, 2025 Reuters: Amurka na matsa lamba kan kotun ICC don janye bincike kan yakin Gaza da Afghanistan December 11, 2025 Ghana ta yi Allah wadai da cin mutuncin ‘yan kasarta da ke balaguro a Isra’ila December 11, 2025 Sakamkon Jin Ra’ayi: Yawancin Amurkawa na adawa da kai hari kan Venezuela December 11, 2025 Hamas Ta yi Tir Da Sabbin Matsugunan Yahudawa Da Isra’ila Ke yi A Yankunan Da Ta Mamaye December 10, 2025 Kasashen Nijeriya Da Saudiyya Sun Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar Tsaro Ta Shekaru 5 December 10, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci