Shugaban Kasar Iran Ya Yi Tsokaci Kan Shawarar Tsarin Inganta Jagorancin Duniya
Published: 21st, September 2025 GMT
A kwanan nan ne aka rufe taron kolin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai ko SCO a takaice, a birnin Tianjin dake arewacin kasar Sin, inda shugaban kasar, Xi Jinping ya gabatar da shawarar tsarin inganta jagorancin duniya. Wakiliyar babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG, ta zanta da shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian, wanda ya halarci taron, inda ya ce, ana amfani da ma’aunai biyu a halin yanzu a duk duniya.
Masoud Pezeshkian, ya ce bai kamata a aiwatar da ma’aunai biyu a fannin dokokin kasa da kasa ba, wato duk wata kasa, mai fama da talauci ko mai hannu da shuni, mai tasowa ko mai karfin tattalin arziki, babba ko karama, ya kamata a mutunta ta cikin adalci. Amma har yanzu ba a kai ga cimma wannan buri ba.
A ganinsa, ya dace sassan kasa da kasa su girmama wannan ka’ida, ta yadda za a iya aiwatar da shawarar tsarin inganta jagorancin duniya. Ya ce a hakikanin gaskiya, idan ana son yin watsi da ra’ayin nuna bangaranci, ya kamata a bi tsarin da aka kafa, gami da yarjeniyoyin da aka daddale a wajen taron kolin kungiyar SCO na wannan karo, tare da aiwatar da su a zahirance. (Murtala Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Pezeshkian: Bunkasa Masana’antar Makamashin Nukiliyar Iran Don Inganta Rayuwar Al’ummar Iran Ne
Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Faɗaɗa masana’antar makamashin nukiliyar Iran don inganta rayuwar mutanen kasar ne, ba don makamai ba
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya gana da manyan jami’ai a masana’antar makamashin nukiliya ta ƙasar a lokacin ziyarar da ya kai Hukumar Makamashin Nukiliya ta Iran (AEOI).
Shugaban Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Masoud Pezeshkian, ya ziyarci AEOI a ranar Asabar da yamma, inda ya gana da wasu manyan jami’ai a masana’antar makamashin nukiliyar.
A yayin taron, Shugaba Pezeshkian ya jaddada cewa: Abin takaici, farfagandar son zuciya ta sanya ra’ayin “Makamashin nukiliya” ya zama daidai da samar da makaman nukiliya. Ya ce, “Samar da bama-bamai na nukiliya ƙaramin ɓangare ne kawai na sakamakon da ba su dace ba da rashin tausayi na wannan fanni. Sauran wannan masana’antar tana da nufin biyan buƙatun ɗan adam na asali. Manufar Iran da nufin kasar na faɗaɗa wannan masana’antar ita ce biyan buƙatun mutane da inganta rayuwar ƙasar ne, ba don samar da makamai ba.”
Shugaban ya kuma jaddada cewa: “Suna ɗaukar amfani da bama-bamai na nukiliya haramun ne, bisa ga fatawar da Babban Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci ya bayar.” Ya ƙara da cewa: “Ilimin yana cikin tunanin masana kimiyyar Iran, kuma rushe gine-gine da masana’antu ba zai hana kasar ci gaba ba. Za ta sake gina cibiyoyin makamashin nukiliyarta da ƙarfi sosai.”
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Araqchi: Da Hadin Bakin Amurka, Gwamnatin Isra’ila ta kaddamar Da Hari Kan Kasar Iran November 2, 2025 Larijani: Iran Ba Ta Tsoron Gudanar Da Tattaunawa, Amma Ta Zama Mai Amfani November 2, 2025 Gwamnatin Isra’ila Tana Ci Gaba Da Hana Masu Jinya Zuwa Kasashen Waje Neman Magani Daga Gaza November 2, 2025 Kasar Qatar Ta Ba Da Tallafin Gaggawa Ga Al’ummar Sudan Bayan Gumurzun El-Fasher November 2, 2025 IAEA : Babu wata shaida da ke nuna cewa Iran na kera makaman nukiliya November 2, 2025 Amurka : zamu dauki matakin soja idan Najeriya ta gaza kawo karshen kashe Kiristoci November 2, 2025 Hamas ta musanta zargin Amurka na cewa tana sace kayan agaji a Gaza November 2, 2025 Wasu Yan Ta’adda Sun Kashe Dakarun Sa Kai 2 A Kudu Maso Gabashin Iran November 2, 2025 Sojojin Amurka Na Kara Fuskantar Venezuwela Adaidai Lokacin da Trump Ke Musanta Batun Kai Hari November 2, 2025 Isra’ila Ta Kashe Mutane 4 Tare Da Jikkata Wasu Guda 3 A Kudancin Labanon November 2, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci